← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 152 OF 206

Sashe 152

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wani muhimmin aikin sirrine ya tsaresa bai dawo abujan ba sai da yazo kuma yatarar da mr aqeel har yafara  aikin ayayinda yake kan jiransa da sako, wanda ko hutawa basuyi ba ya dauki file din nur agidansa snn suka zagaya Abuja wajen clients dinsu suka karasa binciko wasu abubuwan da dacan bai saka ba dan yasan koma yayane tunda an dago maganan to dole ne javeed ya kasance cikin matsala in har gaskiyar Nur firdaus bai fito ata fuska me kyau agidansu ba.

sultan kuma yajima dasanin gaskiyar nur dan shi akoina labari yake inda shine aka bashi aikin bincika tou ko angoge sai yasamo, he had full details na rayuwar nur acikin file dincan da javeed ya tsallake yaki dubawa but he just cannot breach his own profesionalism ethics nd protocols ko wani marital privacy wajen gaya mishi tunda dai yasan javeed din baso yake ana yawan shige masa hidimar rayuwar aurensa da nur ba.

javeed yay shiru har saida sultan ya gama surutunsa na bada haqurin bata masa lokaci dayayi shide baice komi ba

hadadden agogonsa kawai ya duba yaga time can cikin sauke ajiyan zuciya da calm voice dinsa me sanyi yace sultan its okay, ynxu zaka tsaya surutu ne ko zaka zo dan ance mother zata kasance a gidan nan by 10:am and i need to be ready. agaggauce sultan din yace "alryt ina zuwa kawai i will be with you in minutes inna zo we wll talk more.

javeed baice komi ba ya katse wayar sai kuma bai koma cikin safe din ba, daukar parcel din da yasaka stained bedsheet din yay snn ya bude dark acreage dinsa ya dan kunne candle light ya zauna kusa da hoton mamansa yay shiru for while baice komi ba.

dan tun da aka fara case dinnan ya dinga jin tsananin kewarta wanda yasan da ace tana raye da bazata taba kin bin bayansa akan nur firdaus ba and she wll help him find the truth badai ta juyamai baya ba shiyasa haryau yake jin radadin mutuwarta da absence inta in his life duk da yawan shekarunsan nan.

yana daga zaune banda kallon fuskrta babu abunda yakeyi ayayinda yake raya wasu abubuwa acikin ransa bai kuma tashi ba saida yaji kamar motsin janet a dakin snn ya fito

9:30 an on d dot ta kawo abincin dayace matan tay umarni ya bata akan ta aje tray din breakfast din akan table daga nan ta fice cikin sauri...

bayan ficewarta ya jawo note pad ya rubuta ma nur sako akai snn ya rage wutar dakin sai ya fita waje

saukowarsa bada jimawa ba yaga sakon Mr aqeel na cewa sun iso, 9:35am ya zaga kofar undergrond garage dinsa yana fitowa sai suma gasu nan sundiro tanan sun shigo cikin convoy na wasu kyafaffun jeepa jeepan DBX bakake kusan guda shida ajere sultan ne da body gurds dinsa sai kuma mr aqeel  a tsakiyarsu.

wanda tunkan su gama karasowa wata sihirtaccyar ajiyan zucya ta kufce ma sultan ganin kamar javeed looks fine dan yadda yaga yay kyau sosai baiga alaman wata damuwa atattare dashi  ba.

yana karasowa ya fito a motar jikinsa sanye da kananan kaya nan sukayi musabaha mr aqeel kuma ya gaishe da javeed din da ladabi snn ya ja gefe ya basu waje.

babu wani bata lkci sultan ya mikamai file din...javeed ya karba amma bai bude ba kawai yace sultan ya gaya masa iyakar abunda yake da bukatar jin duka dan har ransa baison shida kansa yay invading privacy na matarsa sabida hakan baida wani ma'ana ko a addinance.

sultan bai boye masa komi ba saidai dake yariga yagane me javeed din yake nufi tuni aransa ya kulla cewa bakomine da yaji gameda relshp din nur da mrs haseena zai gaya masa a fili ba dan akwai abubuwan da shikansa sun bashi takaici da mamaki aciki.

iyaka main point din kawai ya ciccicire tun daga case din mrs haseena na siyasa da alakar hakan da hajya farida bala,
sadaat,da duk likitocin da suke da hannu akai da zak zak abunda yafaru ranar da aka farmasu nur, da alluran ciki da aka ma nur na HGC har izuwa case din Dr surayya wanda already ma sun same contact inta har sunyi magana da likitanta dake chan cairo sun daidaita komi.

sultan yace ma javeed Wani allura farida bala tasaka aka dinga ma dr surayyan akai akai tun ranar data fara jinyartan anan nigeria waidan karta warke dawuri bare ta tafadi gaskiya abunda yafaru da nur shiyasa haryau itama ake jinyarta amma babu alamar warkewa.

tunjiya dai yasaka spies dinsa da suke egypt suka dauketa yanxu haka ankaita asibitin john hopkins birnin Baltimore dake america an damkata hannun trusted doctor specialist dinsu kuma ake aiki akanta har likitan yace yau da safe speech dinta yafara dawowa tafara magana da kadan kadan izuwa sati 1-zuwa 4 zata warke gabaki daya musmn inhar illar allurar da akayi ta matan bai taba brain inta sosai ba.

suna daga tsaye anan
sultan ya fayyace ma javeed komi da komi da kuma informtion akan duk wanda suke da hannu aciki.

kafin nan mr aqeel ma ya karaso kusa da su nan yahau gaya masa cewa already yasaka mutanensu agari zasu capke senator farida bala,da duk wanda hannunsun yake kan case din tareda dukkan likitocin da sukayi aikin, snn ya bawa javeed full details na yadda sadaat ya rasu a hannunsu Adnan shehuri a matsayin revenge na nur firdaus da sukayi masa da  uwan acid.

javeed baiwani sha mamaki akan sauran abubuwan da suka fito fili game da nur ba dan sai yanxu komi ya kama hankli.

saidai sosai yasha mamaki akan abbwan da layla tay ma nur na bata suna a schl dinsu kafin nan yuwar auren su da adnan da kuma yadda adnan din ya zamo batacce. shide yasan tun ranar da yafara amsar wayr nur ya haddace lambar yaron, snn yay bincike mekyau akansa bai dai samu komi na dabiar banza ko batanci akansa ba wanda shiyasa ma baiwani daga hankali sosai akan soyayyrsu  da nur firdaus ba saidai yaudin yasha mamaki sosai daya ji cewa wai still adnan dinne shida abokanan sa suka kashe sadaat under the influence of hard drugs batare da sanin kowa ba.

wani karamin tunani yay snn yace ma mr aqeel yaje yaji da sauran kawai yabarshi shida kansa zaiyi handling din su adnan din personally amma sauran mutanen kam kaf wanda hannunsu yake cikin case din akamasu snn akai masa su chan cikin underground torture room dinsu dake Abuja.

godiya yay ma sultan duk dama sultan ya kance masa babu godiya a tsakaninsu cos they are like twin brothers tun da suka taso kuma yawancin manyan influence da samun kariyarsa daga can sama yana zuwa masa ne daga ahalin mufasa he practcly sees them as his only family dan shi na shi iyayen sun jima da rasuwa.

bayan javeed ya gama bada oder akan akyale su adnan abar masa,  da ladabi Mr aqeel ya amsa shi, nan atake suka yo sallama snn suka kara ficewa agidan shida sultan

sultan ya kara wucewa garin abuja mr aqeel da sauran men dinsa kuma suka fada harkan aikin da aka sakasu.

nan javeed ya koma cikin gidan rike da file din a hannunsa baiko bude ba, fitowarsa daga wajen kenan suka kusan cin karo da lady siddika lkcin tawani irin shan kwalliya ta saka kaya ubansu ga gwagwalai dan har wani ankon colour sukayi dark royal purple ita da kirjin biki wato hajy zubaida da tunanin yaune auren kanwarta simran da javeed mufasa.

wanda tun asuba suke ta bidiri ana famar yagalgala simran ana kodata ita kuma sai tafka zumudi takeyi jin yaune aurenta da javeed kanta na rawa duk ta kasa nitsuwa, she was feeling her self tanajin yadda ake mata nasihar aure har wani zugata akeyi ana ce mata ana daura auren daren farkonta da javeed marmaza tay tay cikinsa saboda shekarunta ya danja dai ta tasamu ta haifi koda y'ay'a biyu zuwa uku da shi....

wani dan uban hada rai da javeed yay ya saka lady sid bata iyayin dogon magana da shi ba tuna irin tsawa da rashin kunyar da yay ma anty suad itakam tasan hala marinta zaiyi tsaf in tace zata hatsala shi, suna hade ido sai kawai sai tace mai ai nan da minti goma mother za ta iso ana jiransa a babban falon gidan dan tarbanta.

da idonsa kawai ya bata amsa snn ya dauke kai ya shiga dakinsa ya samu har nur ta farka jikinta babu wani karfi sosai tana zaune a takure agefen gado tay shiru

kara hasken dakin dayay yasaka ta dago kai atake tadan kalleshi suna hadeb ido ganin hawaye na sauka a fuskrta yuu yasaka ya aje file din akan table yay sauri ya karaso inda take kamar zararre yana jawota jikinsa tabi ta sulale akan kirjinshi ahnkli suka wani irin rungume junansu sosai ayayinda jikinta yadau wani dan uban zafi.

lallabarta ya dingayi har saida tasha pain relivers dake kan tray din,snn ya hada mata tea dakansa ya bata takarba cikin lallami yace mata taci abinci kadan ta kwanta zaije can kasa ya samu babansa yanxun nan zai dawo.

dake ma batajin dadin jikinta sai bata masa wani gardama ba

jikinta a muce take kallonsa har ya dauko parcel din daya saka bedsheet din jinin aciki yahada har da file din, dacan har zai fita saikuma ya tuna is better to keep her motivated dan baison tasaka tsoro aranta ko tay ta tunanin da zai daga mata hankli

lambar likitan dake kulawa da dr surayyan ya cire a file din snn ya kira asibitin direct yace a hada shi da client dinsa tunda ance tafara magana kadan kadan

ana kkrin hadasun kuwa nan ya maida call din video snn ya kawoshi ma nur ya mika mata wayar yace mata tayta magana da antynta kafin nan yaje kasa ya dawo da sauri ta aje tea din hannun ta da kirjinta na rawa rawa duk ta dauka razia ce dan babu karya tafi dora tunanin razia aranta fiye da na kowa despite keeping it to her self amma haryau babu wanda take son gani kamar yar uwanta razia.
Chapter 152 · 0% Book details