← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 206

Sashe 112

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yau kwana biyu da tafiyar javeed still akazo breakfst Suga nur bata fito ba kowa da abun aransa amma duk cikinsu babu wanda ya iya tambaya sabida suna matukar balain jin haushinta da kishinta.

Daga sashen nur din kuwa wani dan uban zazzabine ya rufeta cikin dare ya hanata bacci dan haka sallahn dare kawai tayitayi wanda har saida safe bayan tay wanka da ruwan sanyi tasha magani snn tay sallahn fajr ta daga hannu tanata addua wa mijinta javeed akan sallayar bacci ya dauketa batare da ta shirya mahakan ba.

ita kuwa na'ima koda tazo ta sameta tana bacci ganin baccin yay nisa zufa ya fetso mata akai yasaka ta kyaleta bata tasheta ba

daga dinning anzuba abincin kenan simran hartay ready zata fara yagar katon naman kaza data dauko acikin dish nan alhaj attah dake lura da yanayinsun ya dakatar dasu kofara cin abincin bai bari anyi, kai tsaye ya tsaresu da zancen rashin zuwan nur kan table din jiya iyau.

wanda kamar dama jira suke nan danan lady sid tafara masifa yadda zaka san kyaun nur din ya jima yana bata haushi a zafafe take cewa wai halan tana can daki tana kwalliyane kmr wacce zataje gasar kyau..

anty suad tace sam mulki ne kawai da rainin wayo, nur jira take aje har dakin a daukota tunda me kawota nan din bayanan..

Alhaj Yay shiru yana jin kowa na fadin albarkacin bakinsa yana dada lura da yadda kowacce acikinsu take rike da wani muguwar abu aranta game da nur firdaus.

cikin sauke ajiyan zyciya fuskarsa ba asake ba ya dubi hajya zubaida tare da umartan ta akan ta haura sama taje ta dubo lafyar nur dan yasan koda bazata ci abincin ba zatazo ta gaishesu...

tunma kafin hjy xubyn ta amsa cikin zafin kai anty suad tafara wargaza waje tana masifa tana cewa badai aje a dauko nur a daki ba, itadin waye? wasu maganganuntan cike suke da cin fuska, da yadda take bayyana bambamcin social status dinsu da ahalin nur din gabaku daya tana zage zage.

ganin hakan ne yasaka hjy zubaidan yin taurin kai itama taki ta tashi..

alhaj attah still baice musu uffan ba yay waya aka kira main house cook yasakata ta shirya breakfst agabansu ya mike yace ta biyosa estate din nur din da shi, shi ai surkuwansa ne kuma amana javeed ya bar masa bazai zauna yay shiru akanta ba.

ganin baici komi ba ya mike zai wuce duk matayen suka mike tsaye cikin kasa danne haushi da bacin ransu suka hau binsa chan da rawar jiki simran itama ta hau binsu saman duk dama tasan anyi banning inta sai sand'a takeyi tana sum sum abayan hajy zubbyn tsabar son zuwa taga me zaije ya faru..

alhaj attah da cook dake biyosa da breafst din suna shiga aka bude musu kofar sashen

lokacin na'ima ta gama komi wajen ya dau wani irin qamshi

nan tay sauri ta amshe tray din a hannun cook snn ta rusuna kasa tafara gaida alhaj attah cikin girmamawa.

babu yabo babu fallsa ya tambayeta inda nur din take

bata amsa ba sai ga nan su anty suad sun faso sashin dama basu taba zagawo nan ba sai wani yatsinawa suke suna kukkunin yadda komi na sashen ta yay daban agidan

tana shigowa da zafin kai takatse na'ima da cewa ina yarinyar nan take and why is she not on the table dis morning?

na'ima tay murya kasa kasa tace hajya tana can ciki tana..

wani irin bangaje ta anty suad din tay ta duro cikin dakin Alhaj attah yana kkrin jawota baya sam taki tsayawa ita da ayarinta duk suka shiga ciki

alhaj yana hade ido da na'ima data san dattako da kunya ne ya hanasa shiga tay masa alaman ya shiga din kawai babu komi...

baiso shiga ba amma gigin iskanci da zafin kan dake uawo akan su suad dinne kawai ya sakashi shiga, yana kusa kai daga kofa yagansu atsaye kamr an dasasu dan sunga yin tsammani ne zasu su sameta tana kwalliya ko tana kan baccinta akan gado.

na'ima na shigowa da tray din abincin ta aje akan table snn ta kallesu duka tace musu su shigo ta nan..

binta sukayi yuu takai su har cikin prayer coner din dakin inda nur ke dukunkune akan sallaya jikinta killace da dogon farin indonesian style hijab qur'aninta abude tana kan baccinta peacfully agefensa

Borin kunya ne ya hanasu magana ayayinda naima ta durkusa gently kmr wanda ranta baisoba ta hau taba nur din kadan tareda kiran sunanta gently tanamai gaya mata cewa tay baqi...

sosai baccin yay mata dan jiyan bayan zzbi ga kwanan sallahn datay, kalman baqin ne kawai yasaka ta dan daure ta kwace baccin a idanunta da kyar ta bude ido ta mike zaune da tulin mamakin ganin zugar mutanen gidan atsaye akanta sun zura mata idanunsu kowacce tana mata wani irin kallon da zaka san ba haka sukazo suzo suganta ba.

Dan gyara zaman hijabin tay batare da tace musu komi ba tana shirin mikewa tsaye naima tay saurin cewa Hajiya..sir alhaj mufasa yana ciki..

ahankli nur tace father inlaw?

na'ima tana gyada mata kai sai tamike ta kallesu antyn sama sama ta gaishe su bata tsaya jin meya kawosu ba ta fito tsakar dakin taga alhaj attah a tsaye nan ta rusuna har kasa ta gaidashi duk suka fito suna tsayen sunajisu yana kan tambayarta ko lafya jiya da yau bata fito ba

Nur ta rasa me zatace
ta dan sunkuyar da kanta kasa for a while tana tunani dan jikinta sam babu wani karfi da tunanin mijinta kawai ke yawo a brain inta.

cikin wata muryan nitsuwa na'ima tay gyaran murya da ladabi ta ari bakinta tafara gayamai ai takan raba dare ne tana sallan domin yin addua ma general shiyasa da safe inta tashi bacci baya barinta tafito yau kuma sai tadan farka da zazzabi.

anty suad tafara kame kame tana masifa ma naiman cikin borin kunya tana cewa shine ke bazaki sauko kasa kigayamana tana zazzabi sai abun yay tsanani ne snn zaki fada..lady sid ma ta jonata suka tayi, wani maganan ma baiya kama kan hanya.

nur ta fara bawa alhaj attahn hakurin rashin fitowartan shikuma yana comforting inta da words dinsa masu sanyi, sosai yaji ta kara burgesa, cikin soka ma su anty suad din magana ya dinga yabon nur akan irin salon data dauka na taya javeed neman kariya da nasara daga wajen Allah, yadda yake maganan har idanunsa na tara ruwa don nuna musu yake tabbas dansa javeed yay dace da mace ta gari..itade batace komi ba bayan gode masa tay...

anty suad da borin kunya ya cikata tasaka naima kawo ma nur maganin zazzabi alhaj yace mata tasha snn taci abincin inta gama freshening up zata samesu akasa.

bazaka iya fadin irin yawan haushi da baqin cikin da simran da hajya zubby sukaji ba
tunda aka fara maganan addua da sallahn dare sai tsittt kakeji ita da hajy zubby basu sake nunfashi awajen ba musmn ma da sukaga anty suad har ta sauko ta sauya baki kamar ba ita tazo sashen da buhun rashin mutunci ba duk kushen lady sid itama hakanan ta biye ma antyn dan tasan duk tsiya bazata taba kushe abunda zai kare rayuwar javeed ba.

Bayan ficewarsu daga dakin borin kunya ya saka babu wanda ya koma kan dinning table karshe saida a aiko privates maid suna debawa suna kai musu ciki.

nur ta sha maganin snn tay wanka taji dan dama dama taci abincin kadan sai chan bayan sallahn azhar ta shirya kanta cikin marron colour abaya snn ta sauko kasa ta wuce sashen alhaj attah takai masa drugs na dinsa na jiya ta zauna a falon nasa suka danyi hira.

tunda suke bai taba bata labarin mahaifiyr javeed dayawa ba sai yau daya kara dagowa da kamanceceniyar halinsu wajen ibada dan bakaramin burgesa nur tay yau ba

Yana zaune daga kan dogon kujera ita tana zaune akan dadduma akasa yana bata labarin very calmy yana murmushi but she can still feel the immense pain of loss and deep love da wani irin kewarta dayake raunatashi ta ciki.

anan ne nur ta san yawanci daga cikin qualifications dinsa harda kasancewrsa ex admiral of upper half na navy ne a kasa waje da yadda dacan dayake captain din shima yakanje ire iren wayann mission din da can can ayi ta tension amma kuma yace tabbas adduar matarsa akansa shiya ke karamai karfin gwiwa ba yawan powern makamansa da dabararsa ba

hira sukasha har 3:30 snnn ta koma sashen ta tanajin dama dama jin yadda mahaifin javeed din ya kara mata gwiwa akan hakan sosai..

simran kuwa kulle kanta take yi tay ta ciye ciye tana waya da kawayenta inta gaji tay bacci da yamma likita yazo ya duba mata hannu shikenan

amma a waje kuma nunawa suke ai yawancin kaji da simran ta tsirayi ijiya zuwa yau depression ne da damuwa.

haka nan rayuwar gidan ya kasance sauki daya da anty suad ta fara dauke ido akan lamarin nur firdaus saboda yadda taga tazage da ibadah
just after 3 days da tafiyar javeed tafara saukar qur'ani inda ta bawa kanta kwana biyu da safe da yamma take karatun ta hadda a garden ko a daki da yaqinin Allah zai kare mata mijinta.

dan dolennsu suka saduda suka rasa ta cewa akanta duk dama intazo dinning din sai alhaj yay dagaske take cin abinci yafi loma biyar sabanin simran data fara cin sama da plate biyu na kayan dadi.

daga taga su anty suad sun fara hirar nitsuwar nur akan ibada marmaza sai tayanke jiki tafadi tahauce musu ai jiyama tay mummunan mafarki akan javeed haka zata razba kuka tana daga musu hankli dan kawai ace adduar nur da jajircewanta akan ibada bai haifar da komi ba kusan kullum sai anyi wani drama agidan..

ana kwana biyar din ne hajia amira tazo gidan bazata su anty kaf sunyi murnan ganinta dan haka suka dan wuni a falo anata tattauna tafiyar javeed
mission..
Chapter 112 · 0% Book details