← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 206

Sashe 3

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yau nur take cika kwana uku a kaduna kuma yaundine ranar dinner su laylan washe gari bayan budan kai zaa kai amarya gidan mijinta da dare.

Duk walakancin da ake musu a sakaye Layla bata gani tsabar ta saka ranta akan kwadayin abun, wasu mutanen ma a idon mrs haseena suke kushe kankantar shekarun layla amma inaaa ko ajikinsu, wasu har cewa suke kwadayin abun duniya yasaka haseena siyar da mutuncin kwailar yarta wa hajy mairam kanem shehuri.

Maganganun banza da gori dai babu wanda hasina bata sha ba akan auren nan, wani abun ma saida aka tursasa adnan yazo shi wajen dinner, taga yadda familynsa suke yin komi dominsa ita kuma layla saita zama kamar yar kallo dan ko manni zasuyi basu wani fiye bita kanta ba

Tunda aka fara hidimar ko sau daya ango baiyi wani abu romantic ko da kuwa murmushi ba shiyasa ma ba ayi wani fun moment a awajen dinner ba har aka karkare. Babu lefi layla tabaza kyau kam dan kyau amma its all black out in her heart, adnan kept embrasing her awajen dinner dan duk abunda akace ango da amarya suyi tare haka yake kin motsawa, gashi babu kawa, dangi ko jini ko daya nata bare wani abin ya ragu musu.

washe gari ana shirin budan kai hirar dinner duk yacika dangi anata cewa wai auren dole akama adnan tun layla tana iya daurewa harta dawo tana boye kanta a bayin gida tay ta kuka sosai...

ahakan kuma wai tana tunawa da nur firdaus dan gani take kamar duk inda matsala ya sameta nur zatazo kuma ai bata taba barinta acikin matsala ba sai a wann karon

a daddafe dai akayi hidiman karshen har aka karkare budan kai
wanda shima Adnan beizo wajen ba sai can da yamma yarufa duk aka gaji da jira kuma yana zuwa ma bejima ba akayi manni da sauransu suka kama gabansu shida abokansa.

hankalin mrs Haseena bakaramin tashi yay ba dataji yadda sunan layla ya karade dangi da gulma kawai a fito fili ace musu auren cushe ne kawai ba a fada ba amma Adnan makes everything difficult and obvious

wanda basu san baison auren bama saida yayi yadda suka fahimce lamarin tun daga yanayin yadda yake banzatar da komi na auren kamar ba aurensa ba

Koda akazo kai layla dakin mijinta haka Mrs hasina ta dinga lallabata tace mata ta toshe kunnuwanta komi zaizo ya wuce
Kwanan nan inta haihu da shi bakin yan gulma duk zai rufu

da haka ta lallabata laylan suka rabu suna hawaye aka kai layla wani irin hadadden sabon gida da aka gina ma adnan a maitama wanda still iyayensa ne suka saka komi aciki dan hjy mairam ta gayawa mrs hasina cewa bata da arxikin da zata yi ma yarta irin garar da sukeso so agidan dansu dam haka zasuyi abunsu aidama auren na alfarma ne bana soyayya ba.

ahaka dai aka rabu Babu dadi cikin zucyar Mrs haseena dan ranar da aka kai layla dakin miji ko runtswa bata iyay ba tsaban tunanin irin ukubar dangin miji da yarta zata shiga gata bata da wani wayo kai shekaruntan har nawa ne abunda duk yazo kuma yanata damunta

daga gidan amarya layla kuwa tunda aka kaita dakinta kowa ya watse akabarta ita daya tun tana zaune a tsakiyar gado tana jiran ango yazo ya bude mata kai suci kazar amarci har ta gaji da xama dataga karfe biyun dare ya wuce baizo ba ta hakura tayaye makanta mayafin tay wanka tanemi tea tasha ta kwanta ita

kasa baccin tayi sai inta tuna nur firdaus sai kuma taji kamar bata kyauta mata ba.

hakanan rayuwarta ya fara agidan da tunanin any time soon zataga shigowar Adnan amma sai shiru, koda tazaga gidan sai taga ashe ma sashensa agidan anyisa ne daban dakayan alatun da sukaci uban wanda yake sashenta sai kuma damuwa yabi ya cikata cos all she can rmbr awajen auren nasu is how adnan keep reminding her cewa he is going to be her walking night mare...NA KUDINE
PLEASE DONT SHARE IT

08060712446

[23/04, 23:03] Anne-Aurora🦋: NF2surayyahms:

Bayan kwana biyu da hidimar biki layla itakadai tacigaba da zamanta agidan tana mai dada lumar da zucyarta acikin tsananin tsoro da damuwa gashi bbu me nemanta koda a waya face mummynta kullum kuma acikin kaimata kuka take akan tunda aka kawota gidan adnan harynxu bai shigo gidan ba mrs haseena kullum tana kan aikin rarrashinta akan ai dama zaman aure haquri akeyi.

A sati na farko da kammala biki burin Mrs haseena ya cika sakamakon damka mata takardun gida da hajya mairam tay

she is now the sole owner of her own mansion na gwarimpa iyakan ne kawai ya faranta mata ranta amma banda batun auren yarta layla gashi bata isa ta kai korafi gaban hjy akan adnan ba dan mutane ne da basuson agaya musu aibun yayansu kokadan ynnxun nan saisu hau fushi da gorance gorance

domin kujewa gori da baqar magana yasaka kawai mrs haseena tay shiru saidai kawai ta rarrashe yartan..

yadda adnan ya jefa layla a matsanancin damuwar rashin ganinsa a gidan tun ranar da aka kawota yasaka Mrs haseena tunanin inama ace da nur firdaus tana nan da zata umarceta ta kirasa ta dan lallaba musu shi yadawo gida wajen matarsa dan tasani sarai adnan zaiji maganan nur firdaus fiye da na kowa.

tanason tay hakan amma kuma ego ya hanata saukar dakai ta nemi lambarta gani take kamar intay hakan girmanta ya fadi kasa warwas kawai gara ta nemi mafita ta wani waje.

a fannin Adnan din kuwa wani hotel suka kama shida abokansa suke zama aciki tun da ya san cewa nur ta bar rayuwarsu batama zaune cikin Abujan yanxu ya dada tabarbarewa. daren aurensa they do alot of drugs sabida he kept imagining ina ma ace nur zaije ya tarar a gidansa amatsayin matarsa na sunna.

wann tunanin kusan haukata brain dinsa ta dingayi wanda ya jawo masa dada zurfafa cikin shan kayan maye sosai...

gashi dad dinsa ko ya kirashi baya son daukawa bare mum dinsa da haryau yake dora mata laifin komi, tun suna daga jjiyar wuyarsu akan ya dawo gida har suka gaji suka kyalesa..

tunda aka kai masa layla akalla saida yay kusan sati be leko inda take ba, akwana na takwas din ne cikin tsakiyar dare ya dawo gidan yakwanta a can shashensa snn yafara tunanin akan rayuwarsa da alkwarun daya dauka ma nur firdaus cewa zai koma kan karatu da kuma aikinsa duk sanda ya tuna cewa ba nur bace agidansa matsayin matarsa sai yayita kuka shikadai

washe gari da safe koda suka hadu da laylah ta fito daga nata sashen kenan tahangosa zai fita.

jiki na bari tay sauri tataho wajensa tafara masa magana lkcin ransa a mugun harde dan beiko kalleta ba bare ya amsata ya saka kai ya fita

jikin window tay ta kama labula tana kallonsa hawaye na zuba aidonta tana kallo har ya shige cikin motarsa ya kara bar mata gidan ofishin mum dinsa ya wuce kai tsaye Domin fara shirin komawa bakin aiki da karatunsa wai koda wani abun zai masa sauki.

**********

Bayan kwana biyu.

Kamar kiftawar ido da bismillah Rayuwa ya fara sauyawa Nur firdaus acan gidan kawunta dan kuwa kulawa na musman ake bata ta kowani bangare, doc taher shima yana balain taimakwa wajen engaging dinta da deep converstion session irinasu na professionals ahankli ahankli yanayi yana jin ra'ayoyinta tana kuma fitar da abubuwa da yawa wanda suke toshe mata tunani da jin dadi.

ga wasu allurai da ake mata ajijiya suna da mugun zafi kam amma cikin kankanin lokaci tasomajin kamar kwaco kwaklta akeyi daga halin data shiga na tsananin damuwa abaya, sosai tasoma fahimtar kanta takuma soma jin sauki sauki sosai a zuciyarta sabida samin nitsaten bacci da kwanciyar hankli tare da kulawar Razia,

gabaki daya satin sai tajita daban with no one to scold or hurt her, snn babu kadaici ko lokacin yin tunani dan matan uncle dinta ma kadai basa barinta da kalar suruntunsu thy are alwys in her company,safe rana dare suna sakata dariya da magana dan dole kuma dama docton cewa yay abashi sati guda da ita zai iya bakin kkrinsa wajen rage mata tunani da yawan damuwa sauran kuma su dasu dora daga nan...

Dan haka hajy sa'a da hajya bilki suka hau shirya abubuwan da zasuna dorata akai anasu fannin na gargajiya irinde home training da suka ba razia kamr koyan girki
,qamshi, da sauran dabiu masu kyau na yan mata dan sunsan ba lallaine ace mrs Haseena ta zauna ta bata tarbiya ko koya musu yadda kalubalen dake cikin rayuwar ya mace yake ba.

Burin su baifi suga nur firdaus din ta dawo tamkar yar cikinsu agidan ba. They all belive she have a better future ahead of her, ko sau daya basu sake tuna mata da abunda ya faru da ita abaya ba, dan sosai kawunta yake so ya cika mata burinta nayin zurfin karatu dan haryau kokadan bai karaya da rayuwar Nur firdaus ba.

su hajya sun fara shirin hiring wanda zasu koyar mata kala kalan girki kenan sai kuma tafiyan business ya kamasu dan atare suke harkan shipping din kayan kitchen da kayan sawa agidan sun maidashi kamar family business.

Bayan tafiyarsu Daga ita sai razia da wasu mata masu aikin kulawa dasu agidan aka bari gidan sai ya zama shiru babu abun yi duk sai tarasa abunda yake mata dadi jim tunanin abubuwa sun fara dawo mata afresh
Chapter 3 · 0% Book details