← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 206

Sashe 41

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mrs haseena ce tay ruwa tay tsaki ana komi da ita manema larabarai kala kala suka zagayeta da naurorinsu kowa na son jin bayani daga bakinta.

wani irin kyau tay ta sako bugaggiyar ladies getner me kyalli ta yi dauri daya mugun zama daram akanta doguwar sumantan nan dukda ta turfkeshi har kusan bayanta jelarsa yake zuba.

ana mata interviews sai washe baki take tana bayyana yadda suka samu nasara me girma wajen kamo me lefin tareda gurfanar da ita agaban alkali

dan jaridar BBC Hausa yace “Madam Haseena, muna taya ki murna bisa nasarar shari’ar nan tabbas Wannan hukunci da kotu ta yanke kan matar da ta kashe mijinta saboda ya aura mata kishiya ya kayatar da al’umma sosai ya kuma bude sabon shafi ga kare haƙƙin mata a Najeriya.”

wani irin murmushi takeyi tace “Na gode ƙwarai. Wannan ba nasarata ce kaɗai ba. Gaskiya ba zan iya daina jinjinawa ba ga shugabarmu Hajia Mariam Kanem ba. Tana daga cikin mutanen da suka suke bamu karfin gwiwa akan wann kungiyar, ayauma ita tabani cikaken damar fuskantar wann tsarin shari’ar da karfin gwiwa.

Yan jarida suka daga wayoyinsu don daukar wannan jawabi, wasu kuma suna gyara makirfo don jin karin bayani nan wani journalis daga Trust TV yace “To mrs Haseena, za mu dan juya daga siyasa zuwa gida. Mun samu rahoto daga bakin wasu jami’an mu cewa diyarki Nur Firdaus ta bude wani babban Islamiya da Philanthropic Center a garin kaduna. Wasu sun ce mana akwai makaranta da asibiti da kungiyar temako a karkashinta. Shin zaki iya bayyana mana wannan batu? Ko shiri ne da ke da nasaba da kudirin ahalinki na ci gaban al’umma?”

mrs Haseena ta dauke numfashi jin wani dan uban mamaki ya rufeta atake..

kasa magana tay tanaji kamar kirkiro maganan kawai dan jaridar yay ya watsa mata face saida ya nuna mata hoton wajen awayarsa.

dakyar wasu dabari suka bayyana a fuskarta tay Kamar bata da cikakken bayani kan abinda dan jaridar ke magana akai ta dan gyara tsayuwa snn ta sunkuyar da kai kadan

cikin sigar kame-kame tace “Uhm... ehm… to gaskiya… na ji dadi da jin wannan labari. Nur Firdaus dama yarinya ce mai hangen nesa da kishin al’umma. Ko da yake… bana da cikakken bayani a yanzu, ehm… zan iya cewa akwai wasu shirye-shirye da dama da ke gudana karkashin kulawar iyalina. Kuma idan wannan labari gaskiya ne, sai dai na ce... ina alfahari da ita sosai”

Yan jarida suka yi tafi tare da jinjina aka bar mrs Haseena da aikin share gumi kadan da tana kokarin dede numfashinta dan ya komawa daidai

wani dan jarida ne yace toh hajiya hasina zamu so karin bayani daga gare ki a gaba ko ta ofishinki, idan kin gama tabbatar da abubuwan da suka shafi wannan cibiyar. Al’umma na bukatar sanin irin gudummawar da ke fitowa daga iyalai irin naki.”

da kyar cikin murmushin dole tace “In sha Allah. Zan ba da hadin kai.”...

daga nan ta wuce cikin ofishinta jin zuciyarta na wani irin tafarfasa kanta na yawo da wasu irin tambayoyi da kuma tsananin kishin abin da Nur ke yi ba tare da saninta ba...

ko zama batay ba tahau kiraye kirayen mutanenta a kaduna har saida ta samu labarin sabon wajen dama can tana fama da haushin gulmace gulmacen da aka dinga kawo mata ma cewa nur ta hallaci internationl confrence a abujan nan har video an nuna mata ta gani.

sosai taji hanklinta ya mugun tashi wani baqin ciki ya turnuke dan aranta ba haka taso tanajin labarin nur firddaus ba taso ace nur tanacikin wuya da damuwa wanda zai tilasta ta dawo abuja ta zauna a karkashinta na dole.

jin kanta ya kasa daukar abubuwan datake gani nan tafara tunanin koma zataje kadunan taci ma abubakar mutunci sai kuma ta tuna shidin ma ba tayan bayane ba,kuma dama tasan yana cike da ita sosai, she thinks he is doing all this for nur just to mock her dan kawai yanuna mata cewa ita bata iya kulawa da yarta ba.

tsabar bacin rai da baqin ciki bata iya zaman office din yau ba, kama hanya kawai tay ta wuce gida cikin hushi gashi dama tay alkwari aranta cewa bazata sake kiran layla awaya ba, dan yau kwana uku kenan da tazo gidan ta tarar da cewa laylan har ta gudu takoma dakin mijinta batare da saninta ba...
[02/05, 19:40] BLUE💙: EPISODE 26🦋
Lagos state, Nigeria. morning.
*ADM Attah Mufasa Fortress, No. 1 Black Tide Boulevard, Exclusive Waterfront Edge, Lagos, Nigeria.*
*******
tsaftatacciyar iskar safiya hade da sautin makaken ruwan teku dake xagaye dasu datake fetsar da wata balain sanyi dasaka nitsuwa ke kadawa wanda ahankli sanyin iskar safiyar maicike da nitsuwa ke ratsawa tacikin wasu dogayen mahaukatan labulen windown dakin javeed A mufasa wanda suke nan farare kal dasu kuma sharara..

kusan al'adace masa kowani safiya sai ya bude wann fararen labulayen windonsa
dan kawai yaji iskar sanyin safiya, karar ruwan teku da kuma kukan tsuntsaye.

Dakin nasa yafi karfin Ma ace dashi daki don yana da wani irin girmane its like an apartment on its own dauke da faluka manya aciki.

A tsakiyar dakin aka kafa masa Wani irin sharbaben oak wood with bronze colour king sized royal bed dataji lallausar katifa da aka lailaye da pure silk dark red cololur tsadadden zanin gado me bargo.

tun bayan daya dawo daga sallan asubh a masallacin gidansu bai motsa ba, zaune yay akan lafiyayyen kujerun dake dakin idanuwansa a lumshe dan kwata kwata baici komiba bayan cimen da yay a jirgi da yamma haryanzu bai saka komai a cikinshi ba, Ahalin yanzu ma bai jin sha'awar cin wani abinci.

Jiyay zuciyarshi tana yawan harbawa da wata boyayyar feeling na kamillen zakuwa da soyayyar nur firdaus me yawa dan kamar bazai kaiga karkare batun auren san nan yau ba haka yakeji..

bayan ya kammala latse latsensa a wata customised military system saida yadau lokaci yahuta sosai batare da andameshi ba Can Kafin nan ya tashi yafita wajen motsa jiki inda janet tasamu cikekken damar shigowa dakin domin ta hadamai ruwan wanka.

acikin zuciyarshi har Allah Allah yake ya gama kominsa ya fito dan yasan yaune kawai zai iya sanin next step dinsa sabida already wata mission me tsananin hatsari da kuma muhimmanci datake jiransa agaba kwata kwata baiso yaje mission din nan batare daya mallake nur firdaus a matsayin matarsa ba... .

yasan kuma inhar ya samu amincewar familynsa akanta ayau toh komi zaizo masa da sauki tunda dama ahalin nasu basa wani shirmen bidia a aure daga sunje sunyi yar introduction angana da iyaye an karbesu toh next time zasu zo daurin aure ne direct ayishi tareda daukar amaryansu a lkci guda sudama basu wani hidimar daurin auren ahalinsu abayyane.

As usual yana bada bayar kuwa cikin dan kankanin lokci janet ta shigo cikin dakin ta kimtsa, daga nan bayinshi ta nufa tay gaban Wata katoton mirror mai dauke da handler na kowani irin kalar kayan gyaran jiki mayuka da turaren wanka a wata show glass na jikin bango

Gefe dashi akwai scrolls na fari da milk da kuma dark blue colour soft cotton bathtrobes body towels dinsa kuma zallan fararene babu wani surkin launi ajiki wanda ajikin scrolls din drawers ne masu yawa na aje wasu kayayaykin gyarar fuska da tarkacen goge kai da hannu.

full size jaccuzi shine a tsakiya,da kuma site din transparent auto- rectangular glass wall shower stand dake wani kyalli kamar ba ataba taba shi ba, Ko mai dai a bayin white nd golden colour ne hakama bayin ya kasance yana da fadi da girma sosai dan har flat screen tv da diner akwai agefe.

Nan danan tay setting masa ruwan wankan da luxurious bathrum themometer shi in warm nd relaxing tempureture snn tabi ta sassaka drops na almond essential oil da zai taya warware masa kasala da gajiya sai drops na rosemary oil danyay relaxing din muscles dinsa tareda sakamai nitsuwa.

Koda ya shigo farin towel mai kauri kawai yadora abisa kugunsa snn ya shiga wankan yadade yana nutse acikin ruwan wankan idonsa a lumshe yanamai jin balain dadin ruwan ajikin shi.

Bayan ya kammala komi ya fito Baidauke wani lokci ba yay yen shafe shafensa ya dada gyara kwanciyar lallausar suman kanshi da caved sajensa da gabaki daya suka dau sheki

snn yashafa kamshin original gallivant brooklyn musk a dukka fatar jikinshi kafin nan yabi da tsadadden turarensa na mufasa noir mai tsantsar kama jiki da wani irin sanyin kamshi mai dadi mai kuma ratsa zuciya da kwakwalwa.

coffe colour pantone shot da wani lallausa kuma hadadden coton v neck napoliana shirt mai nitsatsen blazer da limited edition smart watch na patek philip yasaka wanda gabakidaya komi ya dauke surar ginannen jikinsan casss casss provocking some deep sense of stability nd calmness.

daga nan wani simple coffe brown loafers ya saka a kafafunsa yay kyau bana kadan ba.

Cikakkiyar nitsuwa da dedetuwar hankli duk natare dashi ayayin da yasa harman fitowa..

ahankli ya bude kofar dakinshi Har Lokcin mr aqeel ne kawai a tsaye yanamai jiran fitowar san..

wnn azabbaben sanyin qamshin turarensa mai rikitarwa dake bibiyarshi a duk inda yaratsa ya fara sanar da kowa fitowarshi.

Ratsa dogon hallway din sashen nasa yay Cikin sanyin taku mai tafeda sassanyar kasaita batare daya kalle kowaba ya nufo kofar da zatakaishi ainihin falonsa takasa kai tsaye yaratsa ciki mr aqeel din na mara masa baya. hadaddun manyan faloka masu amsa sunansu faloka sunkai uku suka ratsa kafin suka bar sashen nasa.

Direct suka nufi hanyar bangaren mahaifinshi wanda ke gefen dama da nashi bangaren.

wani irin shiru gidan yadauka kamar babu wasu halittu acikinsa dake duk inda javeed zairatsa babu wani servant ko maid daya isa yahada hanya dashi.

gidan nasu is not a Luxury home da aka saba gani,infact its a typical mafian fortress basu wani saka masa kyale kyalen kayan duniya Da wasu tarkace ba
Chapter 41 · 0% Book details