← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 175 OF 206

Sashe 175

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

main event na bikin shine kowa daga cikin ahalin mufasa xaixo ya siya jinin da nur ta xubar na budurci da wani abu me daraja
amma banda kudi, it maybe stones, jeweries,compnies, shares. da sauransu banda dai kudi dan sukan dora darajar mace ne sama da kowani irin kudi.

Laylah tanajin yadda hjy mammy take ta bayanin hakan masu hajy sa'adatu kowa cikinsu yana masha Allah tubarkallah.

layla sai taji takara rudewa wai mafarki take ko gaskiya? wata nur din ce virgin? bayan tasan har cikin shege tay, jikinta sai rawa rawa yake ta rasa ma uban waye zatay ma wann gulman a tunaninta ko hala ma basu san labarin rayuwar nur bane

tana cikin tunanin wanda zata iya samu anan ta toni asirin nur
koda ma bikin nan zai tarwatse caraf sai taji hajy mammy tana cewa wai Ai bame zama akan wancan kujerar da nur din ta zauna sai budurwa

sukansu hajy sa'a sau sukaji kansu ya kulle sosai gashi suna jin nauyi suyi tambaya..

laylah kuwa kamar wacce aka tsikareta tamike taje ta wajensu jadidahn

sai yanxu nur ta ganta ido da ido bakaramin mamaki tasha dataga laylan ba saikuma ta tuna cewa jiya mrs haseena tace xata mata suprise ko hala laylan ne suprise din oho.

dacan har security zasuy awon gaba da ita nur tace musu ai kanwartace sai kawai aka barta tazo ta xauna tare dasu asama kusa da jadida Allah Allah take wani yaxo ta tada tarxoma ta tonawa nur asiri dan sosai wann uban kudi da hidimar yake neman ya haukatata

idonta sosai ya rufe da baqar hassada da tsinannen kishi data kasa dannewa..

Suna dan hade ido da nur nur din tay mata murmushi me sanyi saidai tun bata mayar mata ba kawai sai ga mother ta iso wajen sheik haidar mufasa yana rike da ita

ana binsu da wani katon silver tray wanda aka shimfida kyallen bedsheet na jinin budurcin nur
firdaus da mother ta saka aka nannade mata shi da kyau aka boye wajen jinin

akai mother ta xuba
Wasu duwatsun heart of eternity diamond, extemely rare ko kera wani abun wuya dashi ba ayi ba gungun dutsen ta dora akai a matsayin tukucinta

dama can bisa al'ada sai wakiliyar ahalin ta dora kyautan farko atafin hannun nur tayi jawabin darajarsa sn ajeshi akan dadduman da ke gabanta daga nan kuma kowa acikin ahali zai kawo nasa ajere.

mother na isowa wajen hajy mammy ma taxo da nata 3 hefty boxes of rare jeweries da wasu gift wanda sanadiyar jawabin farko na mika kyautar daraja dake bisa bedsheet din da mother tayi ne layla ta kara jin matsanancin rudewa jin yadda ake cewa wai tukuicin jinin daren farkonta kenan
kuma yadda tabasu jininta haka zasu bata dukiyarsu da darajarwarsu.

bayan ta bata stone ta hade mata wasu kyautaka na sarkoki da abun hannu da shares na business na man fetur anan nigeria, kafin hajy mammy itama tabata komi da aka kawo sai anbudeshi akan wann carpet din kowa yana kallo..

cike da nuna so da kauna hjy mammy ta hademata da gidajen gona snn tasaka mata albarka aciki.

daga nan alhaj attah ya kawo nasa gift din set of triangular mousseife red diomnds da blue fancy vivid diamonds stones da share na computer technology firms guda biyu a singapore snm yasaka mata albarka.

anty suad tazo ta saka original wittels bach diamond jeweries da wasu mayun gwalagwali na fashion da akayi su da pure gold tabata pent house a hawaii snn ta saka mata albarka ta wuce

snn aka dawo kan sheik haidar shima jeweries na duka na 5 precious stone din nan ya bata, medauke da ruby, topaz, emirald
, gold, and diamond all in thier boxes da wani crypto wallet, khaleefa ya bata wani katon box na customed collection of rare gold watches d katon fili a ikeja lagos. kamil ya bata varieties of bracelet, anklets, da abun wuya yan tsirara na casual dressings da sukaji white diamonds ajiki snn ya bata 2 customixed G wagons.

hjya amira ma ta kawo mata set of jeweries da stock share na new food industries a mexico
wanda kafin kabude ido dadduman da aka shimfida agaban nur yacike da kyautuka da box box na stones da varieties of jeweries da gifts

javeed yana saka nashi kalar kyautar aka rafka guda iya guda albarka da adduoi samun zaman lafya babu wanda ba ayi ba.

lokacin layla hawaye kawai take xubarwa kamar ruwa tana numfashi kamar me ciwon iska dan tun hannunta na rawa rawa tana daukar kan dadduman da video kai har takasa iya daurewa abun yabi ya dame mimie dan kukan baqin ciki da layla takeyi yay yawa

ta dan tambaya jadida ko lafyar laylan jadida ta kalle laylan ta fashe da muguwar dariya me ban haushi tace ma mimie ai haka nan layla take idan taga yar uwanta na cikin damshin daukaka ita kuma kukan murna kawai take iyayi.

mimie kuwa har wani tausayi taji laylan ta bata she genuinely tot kukan murna kawai layla takeyi ma nur, lokcin hankalin nur baikansu sabida rububin masu bata kyauta.

har saida aka gama sann hjy mammy ta jagorance su alhaj abbakar da matayensa suka dauki nur din daga wajen zamanta suna zagawa da ita sashen wajen zaman ahali domin nuna godiyarsu bisa al'adar hidima.

saidai dan xuwa da sukayi da nasu kalar tukuicin yasaka bakaramin dagawa nur din kima da daraja ya karayi a idanun duk wanda suke wajen ba

Jadida tay tay da layla akan ta tashi taje tabi tawagar familyn su layla taki sam sai rabxa kuka takeyi tanajin kamar da ruwan barkwanon duka duniyarn nan ne gabako daya ake tafasa mata gangan jikinta dashi.

cewa ma jadida takeyi wai inta tashi tsaye jiri zai kayar da ita beside aima kawunsu abbakr nur firdaus din kawai suka sani itace yarsu ita uban miye zataje ta musu acan.

mamakin layla ya gama cika zucyar miemie jin sunata musu da jadida har ta tsoma musu baki sublty take bawa laylahn shawara akan tamike kawai taje ta samesu ayi komi da ita dan for sure za'a iya bada ahalin nur firdaus tukuicin suma

da wani irin girman kai da fushi layla taki ma ta kulasu tay zamanta abunta tana kuka tana daukar komi a wayarta

tana kallo iyayen nasu suna zagawa da nur ana godiya kalaman godiya da girmamawa da ake gaya ma alhaj abbakar masu dadi.

it was such a proud moment da sukaji kowa ahalin mufasa yana yaba ilimin addini da tabiyan da nur firdaus take dashi

cikin girmawa da komi suma suka bada tukuicinsu nagani na fada dan bakaramin kudi suma suka kashe ba.

aikuwa suna komawa wajen zamansu aka biyosu da tsarabar su including lands in kaduna, busines tours, da bunch bunch na kudi. hakanan girman kai da hassada yasaka layla bata samu ko kyautar cat ba infact babu wanda yay noticin inta sosai a matsayin kanwar nur firdaus..

Bayan angama duk wani abu da akeyi na bikin al'adar tarban amarya, javeed ya riiriko hanun amaryanshi A yanayin yadda sukayi kyau tare yasa suka samu tukuicin couples daga abokan babansa da few of their important guest harma fiye da yadda ake xato.

manyan dake wajen duka sukayi jawabai masu taba zuciya akan zaman aure

hajya mammy ta musu nasiha game da rike addini sosai snn alhaj abbkar yay speech dinsa me taba zuciya saida nur tay hawaye jin yadda yake bayyana mata how much her real father wil have love to be here...

sosai hankalin layla ya tashi sai firgita takey ita kadai dan yaune tafara experiencing stage na farko daga cikin 5 good stages of pure grieve akan rayuwrta

she started frm right Anger da fushi bata san cewa nadaman rayuwa me tsanani bane yake gigita mata kwakwalarta tun yanxu.

koda taxo taga irin so, gata, arxiki da daukakar da nur fidaus take ciki ayanxu, sai takejin kamar bataga mema ta cimma mekyau anata rayuwar ba...

adnan baya kaunarta, ita batay arziki ba, kuma arziki da matsayin uwar mijintan da take jiji dakai dashi sai taga kamar ko darajar kudin takalman nur firdaus bai kai ba.

koda akazo ciye ciye kowa na ci cikin nishadi amma sam laylah bata cikin hayyacinta.

she cant believe wai nur tasamu babban family da kuma mijin da yaci uban nata mijin akomi da komi, sai satar kallon javeed take gashi nan wanke hannu kataba ga wann dan uban soyayyar dataga javeed din yana nunawa nur a fili dat feel soo real, special and romantic with all the jokes da sukeyi da abokinsa sultan da matarsa mimie, slow dance ne, hannun shi akan kugunta kusan ako yaushe kallon ta yakeyi. layla taga kamar ashe ashe da can ma ba asalin soyayya me zafi nur tay da adnan ba.

gabaki daya ta kasa zuwa inda nur din take sai sum sum take ita kadai tama rasa ina zata sakanta dan sosai komi ya kure mata tinani.....
Babu wani abu mafi muni da abun tsoro kamar kaci haqqin mutum bakajin ko dar dar aranka littafina ba kyauta bane kudi ake sawa ake karantawa ga wanda imaninsu yakeda saura chat me and pay via 08060712446
#SURAYYAHMS
kamar mai ciwon mashasharar tsuntsaye haka layla ta kasance acikin hall din looking dull and moody ,angry and depressed.

3:40 pm akaje break dan ayi sallah asr dake su basu wasa da ibada a ahalinsu snn duk wankan kece raini da akayi babu wanda wani barin jikinta ko kanta yake nan abude.

masu canza kaya tun anan suka samu dama while all the mufasa brother suka saka all black suits matayen kuma suka lafayoyinsu masu tsada.

a rububin hakan ne layla tadan jijji labarin waye nur firdaus ta aura and how extra rich and exclusive the mufasas are.

dataji mafian family ne taraza gabaki daya jikinta sai yamutu ganin jadida tasauya kaya sai itama tasaka datan leshin aron da sukazo dashi tsabar baqin ciki sai bata kara kula su kawun nata ba komi zatay ita kadai takeyi sabida self resentment da evident of life failures dayay nauyi aranta.
Chapter 175 · 0% Book details