← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 206

Sashe 102

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nur tama janet ido akan tasaketa snn ta fita a ruwan, tace toh gani ga ki sai mukara aga waye ne asalin matsoraciya.

ganin janet ta fita naima kuma ta saketa simran tay wani kukan kura ta kama nur da dambe saidai dake ta galabaita kusan taruwa suka mata da na'iman sukayi bullying inta kalar wanda ba ataba mata a rayuwarta ba.

ganin fada ya kaure janet ta sabule tafita taje tasaka wasu kaya mas zak zak irin wanda taciresu yanxu saida taje har main house tay raising alarm acikin gidan snn tazo sashen javeed tasame shi jikinta har na rawa tacemai ai simran ne tazo tajefa nur acikin ruwa.

dama yagama saka kaya ajikinsa kenan dayaji hakan baiko tsaya jin karshen ba ya dau bindigarsa dake kan table ya fito agaggauce janet ta hau biyosa abaya cikin sauri.

rubibin sautin zuwan ayarin gidan yasaka nur ta wani sake jikinta ma simran simran ta fara kkrin shakureta nur ta wani irin sumewar karya, aka abar naima da ririkke simran din baya baya tana wani hargowa zata koma kan nur ta daketa dan kamar wata zaki haka take huci ita sam bata gane komi bama saida taga dandazon jamaar gidan har anzo ta nan...

salatin su anty suad da lady sid kakeji ya karade wajennn

kafin brain in simran ya bata meke shirin faruwa awajen sai taji wani irin harbi tautau yabi gefen hannunta ya fasashi, da azaban tsoro da zafi ta kwalla ihu me kara jin kamar kurwanta ake zarewa

Da wani irin mugun gudu hajya zubby ta kama kokowa da hannun javeed dake shirin kara mata harbin tana wani irin ihu tana rokonsa kar ya harbe simran..

dakyar saida alhaj attah yazo dakansa ya kwace bindigan a hannunsa dakyar

yana sake mishi gun din yayo bakin ruwan da gudu Naima datay kamar raba fadar takeyi ita ta dauko nur din datay kamar bata motsi ta mika masa ita snn ita tafito daga cikin ruwan tana maida numfashi .

wani irin kuka simran take tanajin kamar ta hadiye ranta ta mutu tsabar azaban zafi tarike wajen harbin damm jinin ta nata xubowa hajya zubby tay gudu tafada cikin ruwan tahau daure ma simran din hannuntan da bindigar yafasa da dankwalinta
sabida kar ta shiga gun trauma shock.

kukan azaba kawai simran take kamar zata cire ranta dan bata taba ganin makirci irin wnn ba.

salatine ya karade wajen anata tambayar meya faru meyafaru javeed kuma yanata kkrin danna ma nur cikinta da kirjinta duk yabi yarikice dan asaninshi gani yake kamar nur bata iya wani swimming ba so definatly yasan janta cikin ruwan nan akayi

dadai naima zata fara bada bayani ma su alhaj attah kenan nur din tay wani irin mika tafarka idonta krmr agalabaice suna hade ido da javeed ta fashe masa da wani irin maraitaccen kuka tareda fadowa jikinsa tarungumesa sosai saida yaji hankalinsa yakara tashi..

Hankalinsa amugun tashe yake rarrashinta yanamai dada manneta ajikinshi yana shafa mata bayanta ahankli kuma cikin rarrashi..

naima ce ta hau bada wani irin shiryayyen labari tun simran na sako baki tana karyatata harta fara musu ihu awajen kamar tazare tana cewa wallh sune suka taru suka daketa..

aikuwa nan janet ta kara bada shaida tace itama tazo duba abu ne atanan sai kawai taga lkcin da simran take abubuwa ma nur kamar zata kashe ta.

azuciye javeed ya mike yasamu babansa idonsa yay wani irin jaa out of respect yace masa simran tabar gidan yanxu kar kuma ta sake dawowa ko kuma shi yafitar da ita kuma inhar suka bari ya fitar da ita sai ya karasata.

yana gama fadin haka
yadawo ya ciccibe nur dinsa ahannunsa suka bar wajen cikin sauri sauri dan sosai jikinta ya jike da ruwa haryana diga

bayanin duniyan nan simran tayi musu akan abunda yafaru amma ganin ko kayan janet a bushe yake, da yadda akazo akaga na'iman tanata janta baya baya tana rirriketa acikin ruwan ga nur a sume yasaka kowa yafara mata kallon wata tababbiya.

su anty suad ne ke famar yin questions anata Allah wadai wajen ya kaure da surutu da masifa...

duk da jiri da zafin harbi da kuma trauma simran taki tay shiru dan bata taba sanin zafin da akeji in aka ma mutum makirci ba duk dama abune wanda takeyinshi akan wasu duk sanda taga dama

manyan gidan duk atare suka gaji da surutun suka barta awajen da ita da hajya zubaidan dake famr rirriketa.

suna barin wajen tafara kuka ba acikin hayyacinta ba tafara cewa yaa zubby wallah wallah wallh sharri suke min they bully me, sharri sukamin wllh karya sukemin...yaa zubyy pls belieive me tay hakan ne dan akoreni

wani irin tukukin haushine ya turnuke hajya zubaida bata san sanda ta dauketa da mari ba

idonta yay jaaaa cikin hatsallen tsawa tace mata simran karma kisake min magana fuck ur truth after all evidences of rashin gaskiya da kuma abuse is pointing againts you ryt now kawai ki rufe min baki....

wani irin kukan fitan hankali simran take ga azaban zafi da hannunta yake jini nata zuba suna ficewa daga ruwan ta yanke jiki ta fadi ta suma jin kwakwalrta ya kasa daukar komi ga kuma gun shot trauma

bata tashi bude ido ba sai can bayan ishai taganta akan gadonta har ancire bullet din anyi dressing din hannun...

wani irin jiri na debarta amma haka ta yage drip din ahannunta tqfito har ta babban falon jikinta yay zafi sosai inda ta boyu fa labe a bango tanajin yadda hatsaniya ya kaure aciki..

gani tay hajiya zubaida ta tsuguna akan gwiwarta agaban ahalin gidan duka tana roka ma simran gafara kowa nagaya mata maganar banza kamr ba asanta ba.

komawa sama simran tay tana kuka sosai dan how on earth har yarinya yar shekara sha 18 zata bringing insu down to their knees at such a speed runtse idanunta babu abunda ke dawo mata face cewa da nur tay akan yau zata saka ta bar gidan..

i will update later nagode
[24/05, 22:43] BLUE💙: EPISODE 64
Arewabooks@surayyahms.
simran tafara tattara bags dinta dakomi nata dan gabaki daya bataga amfanin zama ba tasan akan abun nan dayafaru hala javeed zai karajin tsanarta snn ta lura kamar nur tasan duka sirrinta akan javeed yanxu gashi kuma anan falo an sako yayarta agaba ana cin mutuncinta akanta

ji tay gara kawai tabar gidan kar abun ya fara taba mata kwakwalrta sosai..

tana tattata kayan amma gabaki daya jitakeyi zuciyatta da kwakwalta sunyi mugun rauni dan ko a mafarki in akace mata yarinya karama kamr nur zata mata wann abun wallah bazata yarda ba.

gashi jiya ta mata sharri kadan ita yau tamata mai kankat bata san nan gaba kuma uban me zata mata ba dan gani take kamr wann yarinyar shaidance.

Simran tanakan tattara kayanta zata bar gidan saiga wata maid daga main house ta shigo mata da sakon cewa ana nemanta a babban falon gidan marmaza..

share hawayenta tay ta fito tanajin jiri jiri har suka iso falon da wani irin kinibibi inka ganta abar tausayi lady sid ne taje ta riko hannunta takaraso da ita ciki ta ajeta a tsakiyar manyan gidan aka fara mata sabbin tambayoyi tana amsawa tanata kuka tana karyata komi, su anty suad saiyi suke kamar basu aminta da ita ba amma kuma tabasu tausayi sosai.

babu kalar rantsuwar da simran batay akan nata labarin ba amma inaaa haka alhaj attah yace bai iyaji ba..

tun daga kan anty suad din har izuwa kan simran saida ya wankesu tasss yace musu basa kaunar gaskiya kuma basa adalci yanxu inda nur ce tay hakan da bazasu bari takara 2scnds agidan ba dan haka kawai simran itama ta kwashe nata inata tabar mai gida sabida kar javeed yazo ya mata wani abu na lahani wanda bazaizo yay musu dadi ba...

Dakyar matayen suka hade baki suka rokesa aka barta akan zata kwana yau amma izuwa washe gari zata tafi sabida wnn pain da gun shot trauma data samu dolene kawai ta dan huta...

shide baice musu komi ba ya kama hanyarsa ya haura sama

Daga ita har hajy zuby zuciyarsu a mugun raunace suka tashi suka koma sama nan kowa yay hanyar dakinsa batare da sun furta ma juna komi ba

koda simran bata sani ba tasan yau kam ta kuntata ma hajy zubby bana wasa ba tunda har saida tay hawaye agabansu anty..

tana shiga dakinta ta sulale akasa with da wani irin baqin ciki mai tattare da rauni dan ji takeyi kamar yaune ranar da alaqar ta da javeed ya rushe after all this time dat she gave him na rywrt bayan duk irin haukar datay na canza tsarin halittarsa akansa to fit his class and mafia aura amma wai akan wata yar ficiciyar yarinya yar talaka yar almajirai wacce batay karatun boko ba har javeed ya harbeta snn da bakinsa zaice a koreta agidan ...

gabaki daya ta rasa meke mata dadi ta kuma rasa menene guda daya takeji.

babban tambayar dake mata yawo a brain inta yana kima zautar da ita yanxu baifi cewa ko zata iya haqura da quidirnta na son zamowa mtar javeed ko bazata iya ba dan inhar javeed bai aureta ba kunyar kawayenta ma kadai ya isa ya kasheta dan tajima tana nuna musu cewa ita already matarsa ce dan kuwa alkwarin aure me mugun karfine a tsakaninta dashi..

acikin ciwo da radadi gameda takurarren rudani ta zauna akasa tanata kuka cikin rasa kwakwarar mafita..

Ata dayan fannin kuwa tunda javeed ya dauke nur ahanunsa suka bar wajen basu tsaya a koina ba sai dakinta..

yana direta akan kafafunta tafara masa kuka ahankli bata bude idanu ba wani irin kallo yake binta dashi kaman yaune rana tafarko daya fara ganinta awani hali kusan komi dake kan kirjinta na nunawa gawani irin kamshi datakeyi wanda kaman zai shide tsabar dadinsa..

Janyota yayi ya rugumeta tsammm ajikinshi ya dinga lallashinta yana bata hakuri akan bhvr din simran akanta wanda ita bama jinshi take ba cos all she want is to be with him ryt now sanin cewa babu komi tsakaninsa da simran yariga ya kara mata jin wani irin kishi da shauqin mijinta kuma tariga ta gudura aranta cewa yau kam bazata barshi yafita waje yaje koina ba..
Chapter 102 · 0% Book details