← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 183 OF 206

Sashe 183

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ana idar da sallahn asr tashuwa yay kawai yafara hada kayansa da kudadensa dakomi nasa duka yazuba acikin jakansa snn yadauki biro da paper dogo ya zauna ya fara rubuta ma laylah sako. yafi minti ashirin yana rubuta duk wani abunda yake cikin ransa, the hatred, the pity, da kuma saki, pouring all his heart into writing it bai rage komi daga abunda ya ke jiba wanda har saida yagama rubutun snn yaji zuciyarsa tay masa sanyi sosai

acikin sauke ajiyan zuciya ya nannade lettern neatly snn ya saka a brown envelop yaje room dinta ya aje matashi akan madubinta.

daga nan baiyi wata wata ba yakoma dakinsa ya shirya kansa cikin kananan kaya snn ya fito da komi nashi driver ya kaishi airpot kafin yamma jirginsa ya wuce da shi kano state da niyyar yaje ya biya diyyar sadaat wa iyayensa duk dama dai report din javeed ya tabbata cewa DNA dinsa baiyacikin na wanda sukayi asalin kisan duk dama shine babban culprit din sai yakejin gwara kawai yabiya abari acewa baya cikin hayyacinsa yay lefin, besides, ya riga yaci alwashin barin kasan nan kenan har abada bakara ganinsa za'ayi ba.

daga babban asibiti kuwa daf ana kirar sallahn magrib layla tafarka cikin buɗe idonta dake zubda ruwan hawaye da ƙyar duk tafirgice ta razana kamar wacce ta farka daga mugun mafarki. Hasken dakin ICUn ne ya dan daki kwayar idonta tana jin jikinta babu wani ƙarfi.

abubuwan da suka farun ne suka fara dawowa mata kai tanajin zuciyarta kamar an haƙa mata duwatsun wuta aciki, da kyar take numfashi dan tamkar ta rufe ido ace mata komi karya ne itace taci nasara arayuwa ba nur firdaus ba haka takeji

dan ko ayanxu dai tasan itace rayuwarta yake alalace kuma a tsaye cak awaje guda babu wani cigaba cikin jin matsanancin ciwon kai tafara juya kan a hankali tana tuna abubuwan da suka faru awjen biki

tun daga shigarsu har izuwa yadda taga nur firdaus ta dawo tamkar wata sarauniya da yadda komi ya wakana har jin amon muryan nur din takey a brain inta ayayinda take gayawa mata cewa ko batun rape da cikin ma da aka mata duk karya ne.

nan tayi saurin dafe kirjinta 2nd stage of grieve and depression yana neman ya rufeta tafashe da kuka mai zafii mecike da wani irin karyewar xuciya

irin ka dingajin kamar baka ma aminta da abunda ya faru dakai din nan ba, dan wann kalar mugun qaddarar rayuwar bata tsammanin nata ne, nur ce ya kamata ace tana shan wahala haka ita kuma tana cikin irin wancan daula ba d other way round ba

ayayinda take kukan brain inta is seriously bargaining on her nemesis da tunanin koda za'a samu wani kuskure daga wani waje dan bazaiyu ace yadda rayuwa zai kasance mata kenan ba, after all she went tru, da duk dumbin kokrinta na juya ma nur firdaus baya da kwace mata adnan datayi arayuwar ta sann sai ace harta samu miji wanda yafishi komi da komi? yoo ita kenan bata tsince komi na sa'ar soyayya ko aure ba, bare har ajega batun jin qamshin samun rayuwa acikin dukiya da kwancyar hankali??? this is soo unfair.

jujjuya kanta take kanyi sabida ta kasa yadda this is the point where u tell urself it cant be, while it has already been done.

hawaye masu ciwo suna gangarowa daga gefen idonta tana jin kamar zuciyarta zata tsage ta kuma tarwatse.

a hankali tana kuka
cikin tsananin bawin ciki da kuka ta juya tana kallon bango tanajin tsananin fushi da haushin komi na dada rufeta, aiko da za'a ce komi gaskiya ne baikamata ace mata wai nur bata da wani mugun tabo arayuwarta ba, koda zancen cikin nan ne yakamata ace gaskiya ne idan ba haka ba toh ita bata san wani nasara kwakwara taci anata rayuwar ba

tana cikin raya haka aranta Sai kawai ƙofar ICU ɗin ta buɗu Sai ga nan Mrs. Haseena ta shigo cikin sauri duk ta galabaice Likita ne ke bayanta yanadan murmushi da takardar bincikensa ahannu.

suna shigowa likitan ya hau gwada jikin layla sanda ya qamsu snn yace Alhamdlillah, akwai sauki saidai fa haryanxu akwai wasu yan matsaloli ajikinta anaso tarage damuwa snn ta dinga kulawa da lafyar zuciyarta sosai sabida yana daf da shiga cikin hatsari.

mrs haseena tace toh likita Za'a kula Nagode sosai.

Likitan yana fita mrs Haseena ta karasa gaban Laylan da already bango kawai take kallo jikin mrs haseenan a sanyaye ta zauna a gefen gadon ganin yadda Layla ta ƙara fashewa da kuka me zafi sosai musmn data dan dafata tace mata ya jiki,kuka mai zafi layla takeyi har muryanta na kagewa dakanshi abun duniya yay ma mrs haseena yawa nan ta daure fuska ta fara masifa tace haba layla yanxu fa kinaji likita yace ki rage saka damuwa aranki waiko sai xucyarki ya fashe ne kafin ki gane halin da kike ciki

cikin girgiza kai tareda matsanancin kuka layla tace mummy, mummy na shiga uku ina kike ganin zan saka kaina, mummy my life is ruined, bikin yar uwata naje amma ya zama silar baqin ciki da damuwa a rayuwata wallh dana san haka ne da nazabi mutuwata akan danaje bikin nan.

cikin katseta da daure fuska mrs haseena tace, ya isa haka Kiyi shiru Layla! Wannan
maganan bata gadon asibiti bane danwasu abubuwa dayawa masu girgizawa sun faru bayan kin kwanta, badon ke ba da tuni nabar nan sabida yan jarida suna neman su karasa ni
we need to go home now in munje gidan zamuyi magana

laylah dake kuka batace komi ba har mrs haseena ta kira nurses aka shirya musu tarkadn sallama da komi snn suka bar asibitin ta kofar baya batare da kowa ya sani ba.

suna isa gidan mrs haseena layla ta kwanta akan kujera tana zubda ruwan hawaye looking vry depressed kamar wacce take makoki banda tuna rayuwar nur firdaus babu abunda takeyi a mind inta

ruwan shayi me kauri mrs haseena ta kawo mata tay forcing inta ta sha kadan tare da magani, tana gama sha ko dawowa hayyacinta bata gama yi ba tafara bawa mrs haseena cikakken labarin sabuwar rayuwr nur firdaus,ta siffanta mata ahalin suwaye nur din ta aura, da kalar barin dukiya da akayi ma nur , tabi ta nuna mata videon bikin da komi da komi da akayi.

wanda hakan ya kara tabbata ma brain din mrs haseena cewa tabbas nur wasnt raped, she was just framed, dumbin mamaki, girgixa, borin kunya da nadama ya tsananin shigewa jikinta atake dan bata san sanda ta tsilalo kasa ta zauna dubus da duwawunta kamar me ciwon hauka ba.

saidai abunka da yadda layla ta zake wajen sako kalaman makirci da hatred me yawa acikin maganan, sai cewa take wai nur firdaus tazo ne kawai dan ta dauki fansa akansu ta wakalansu, snn tazage aurenta, sabida ynxu tay kyakkwan miji, kuma tay arxiki, ita ko janta cikin hidimar ma batay ba.

kuka laylah take zuciyarta kamar zai fashe tana gayawa mrs haseena duk abunda alhaj abbkr da matayensa sukayi ma nur firdaus na darajawa awajen auren, suma tace banda cin zarafi da rashin mutunci babu abunda ta kwasa awajensu.

duk ta gigita ma mrs haseena hankli tanata kuka tana playing pity and victim card a lokci guda duk ta hana mrs haseenan ma yin wani kwakwaran tunani

itadai kawai so take kowa yaji kamar itace kawai aka cuta a duniyan nan ba nur fidaus ba, itace aka jonata da mummunn qaddarar aure snn kuma
kawunta na kaduna ma nur firdaus kawai suka sani ita sun wareta.

mrs haseena tay iya bakin kkri wajen sasaita layla tare da bata labarin abunda ke faruwa na batun saadat da sen farida bala,.

da mamaki mrs haseena taji layla tana cewa ai tasani
kuma aidama saadat ne yazo musu adaren ranar, kawai taki gaya gaskiya ne sabida kar ta bata siyarsa haseenan

nan fa wasu asirin laylan suka soma tonowa fili musmn ma na
sharri datake yawan yima nur akan sadaat harda zuwa dakin su datakeyi in haseenan bata nan.

cikin tsananin tashin hankali suka fara musayar yawun baki da mrs haseena suna hayya hayya kamar zasu daga gidan musmn da layla ta bushe ido take kan gayama mrs haseena asalin halin sadaat datasani tadinga boyewa tana lakawa nur firdaus zargi da alhakin komi ..

babu kalar mari da bata sha ahannun mrs haseena ba amma ba shine yake hanata mata rashin kunya tana ce mata ita ba nur firdaus bane wallh inta cigaba da marinta sai ta ramaa ai dama can mijinta da aikinta kawai tasako agaba ba tarbiyansu ba shiyasa itama tay amfani da hakan tana boye gaskiyar nur dan ta cimma nata burikan akan adnaan shehuri

kai abu tun yana zafi har laylah ta harkuza taje kitchen ta dau gallon din oil ta fito tsakar gidan da mugun gudu ta kwara petrol ajikinta tana shirin kyasta ashana wai zata kona kanta ta mutu kawai tunda ita ba akaunarta sai ihu takeyi tana cewa ai ko wani irin nasara da kulawa nur firdaus ne kawai ta sameshi bayan itace karama kuma angani sarai cewa nata rayuwar ne yake rushewa kullum ba na nur ba amma babu wanda ya damu da ita.

saida malam liman ya taya mrs haseena kokawa da layla kafin nan suka iya rabata da ashanar, gida duk ya rikice makawabta su maman sa'id duk sun hallaro jikin gate dinsu sun manna kunnuwn su sunata jin gurmi

isowar motar hajy mairam da security ya saka taron magulmata na kofar gidan ya tarwatse

hajya mairam dinne da kanta tare da wani private security dinta su biyu sukazo sabida maganar mutane da kuma babbam burinta na son dawowa da mr haseena kan harkan siyasa sabida suyi amfanin da rayuwar yayanta su karo jama'a da cigaba ma siyasarsu

tana zuwa tasamu ana kace kace ana ririkke jikin laylah a tsakar gida. dake ta manyanta itace ta tatsawatr musu suka koma cikin gidan
Chapter 183 · 0% Book details