← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 155 OF 206

Sashe 155

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da cewarsa hakan simran ta samu dalilin share hawayenta sann ta nitsu, abu kadan sai tay habaici wa hajy zubaida agaban lady sid tanace mata ashe itama ba zuwa akai gidansu aka aurota ba dan baqin ciki shine ita zata hanata.

hajy zubaida tay shiru bata sake cewa komi ba sunfi minti arbain a dakin suna jiran kira amma ba akirasu ba...

daga tacan falon kuwa har saida wajen yay shiru snn mother ta bada alhaj attah fili ya fara gabatar da case din nur din tare da fayyace ma mother abunda ke cikin file da su suad da zubaida suka kawo snn yace shima ya duba file din sosai kuma yaga ba fake news bane.

bayan ya gama magana mother batace komi ba ta bawa anty suad equal chance nayin magana

tunda tafara magana hawayen takaici na zubo mata jin yadda shirun da kowa yay a falon aka zuba mata ido yahau sakata jin tsarguwa saitanajin irin kamr an maidata mahaukaciyane bata sani ba.

tunda fara magana bata wuce kalma daya zuwa biyu bata kawo cin mutunci akan nur ta ko zazzage javeed aciki ba, that intense secret jelousy nd envy she have for him, da kuma kin aurensa da nur din sabida bata so ne akawo mace irin mahaifyar javeed kuma yar talaka

daukawa tay cewa tana sakaya maganar acikin habaici bata san da cewa kowa yana fahimtar duk abunda take nufi daga karsashin fushi dake fita daga muryanta ba.

haka kunya yasaka danta kamil ya binne kansa kasa ya kasa dagowa sama ya kalli kowa haryanxu idanunsa duk yay jaaa ya rasa meke masa dadi.

sai fidda magana take zafi zafi tana nuna cewa ai wa daraja da kimar ahalinsu take fighting amma duk anbi an daure ma javeed gindi yana abunda yaga dama baya daraja al'ada baya daraja manya still tacema mother saidai a bawa danta ragamar rike mufasa dan bataga amfanin bada dukiya ma lusarin namiji kmr javeed ba da yarinya karamace tazo take juya masa kwakwalwa

snn a daura masa aure da simran tunda ta jima tana bauta masa agidan kuma agaggauta kirawo nur gabansu ynzu asakata agaba tafadi gaskiy snn ayi adalci ta hanyar sakashi ya saki nur din agabansu dan tabar musu gidan su, hka ta dage tana cewa ita sam bata aminta da cewa jinin nur bane ma ajikin zanin gadon kawai boye gaskiya javeed yakeyi dan abarsa da matarsa.

wani irin shiru falon yay kowa naji mata kunyar kalaman dake fita daga bakinta amma sai dagewa takeyi akansu, wanda har tagama bayaninta mother kawai kallonta take tana girgiza kai can snn tace mata toh ta zauna toh aji ta bakin javeed din..

waje ta nema ta zauna
still taga kowa ya dauke ido akanta saidai javeed yana mikewa kuma taga kowa ya nitsu ana jiran abunda zai fada.

cikin tattaro makansa nitsuwa yakalli mother snn ya fara fayyace mata duk abunda ya faru da nur cikin ruwan sanyi kuma a killace har saida kowa acikinsu ya fahimce yadda akayi ma akasa mu information dinta me dauke da half truth a dark internat wanda anty suad take kan kafa hujja dashi shide baice musu karya anty suad din tay ba amma kuma ya fadada musu komi daga bayaninta abayyane. wanda tun bai gama ba ta kasa hakuri ta mike tsaye ta buga kasa tace sammmm karya ne wallh wallhi karya ne

danta kamil abun ya ishesa ransa yayi mugun baci shikasan baisan lkcin da ya daka mata tsawa yace mata kawai tay ma mutane shiru awajen ba..tabi ta harzuka zata hau zaginshi alhaj attah ya zare mata jan idonsa tukun ta tsorata ta zauna tafara koke koken banza.

duk sai da javeed ya fadi abunda akama nur na sharri a abuja wanda ya jawo bata gama scndry schl ba saida tazo kaduna jikin su yay sanyi sosai bacin kowa daya ke alhanin jin abunda akay ma yar yarinya suad ce take ganin kamar komi karya ne ai nur din ma bazata iya daukar kalar wann qaddarar ma yay mata nauyi.

hajy amira mufasa har hawaye taji yataru a idonta masu zafi musmn ma da javeed yakara da bayanin abunda su anty suad sukayi mata agidan nan. duk abunda ake ciki ya gayamasu snn ya gaya ma babansa cewa ba haka kawai ya aure nur ba, shidin ma yay bincike aknta kuma yana da file dinsa aknta kawai abune daya shafi personal trauma da baisaka kansa aciki ba wanda shima iya kuskuren daya san yay kenan.

javeed yana gama magana masu salati sukai jikin alhaj attah bai gama yin sanyi ba saida mother ta kara bawa sheik haidar ali daman yin magana a maimakonta.

dan tasan cewa in har wasu basu gama aminta da furucin javeed akan matarsa ba aidolene zasu aminta da ita nata shaidar..

nan haidar ali yace musu suma acan morocon sunyi nasu binciken wanda kusan duk abunda javeed yafada anan shine gaskiyan, da mamaki shina bai fayyace alaqar rashin jituwar nur da mrs haseena ko ya ambace sunan sadaat a matsayin mijin mrs haseenan ba.

cike da kare mutuncin nur firdaus yace musu case din was not even personal, harkace ta siyasa, daya jawo har akay victimizing nur firdaus da yar uwanta layla agidan iyayensu aka farmasu da fake Injections na HCG dat will mimick pregncy symptoms dan kawai a'bata ma mahaiyarsu suna da siyasarta.

har yadan kara musu ilimi akan dabi'un nur tare da nuna musu cewa asalin ba itace ma main target din farida bala ba, she was deeply cought into dis ne sabda kare ya uwarta dataje yi snn ya fayyace musu halayenta na kwarai har wanda basu san tana da shi ba, dan ya lura kowa agidan yana daukar kamar karatun qur'anin ne kawai madogaran ta face saida yagaya musu cewa record din nur a abuja ya nuna musu cewa ita din babban abar kwatance wajen manya da yara it was at end she got stained and traumatized with fake narratives.

daga ganin fuskansu zaka san cewa kowa yasha mamakin maganan amma dake shine babba namiji saida yay yar nasiha akan yanke ma mutum hukuncin gaggawa kafin nan ya zauna

mother tafara magana amma da alhaj attah tafara jan masa kunne akan yakara yin hankli da ire iren wnn half cooked labarukan daga nan sai bata wani ja maganan ba

saida ta dawo kan anty suad dake kuka kamar ranta zai fita duk ta kasa daga kai sabida borin kunya daya gama riketa ya hanata motsi gashi duk an bada shaidoji kwarara bata halin cewa komi snn ta tsaya tamata wani irin kallo snn ta amshi files din nur din duka biyu dana hannun javeed dana hannun sheik tasaka khaleefa mufasa yakawo katon burner tray aka kunna masa wuta snn ta jefa files din duka ciki suka kama konewa..

bedsheet din kawai ta dauka ta rike kafin nan ta mike tsaye tafara addresing dinsu da cewa yadda ta kona files din anan haka take so maganan nur firdaus yakare anan snn bata son tasake jin cewa wani yayi acting akan half truth harma yaci ma wani mutunci akai dan hakan ba adalci bane snn addinin musulci baice haka ba

darajar kamil yasaka bata ma suad tass tass agaban yaran ba musmn yadda take so taga tamata zagin da zai dameta har abada.

saidai duk da haka sanda ta dubeta ta gaya mata manyan maganganu masu ciwo akan hada kanta datay da su zubaida agidan har ana cin mutuncin javeed kai tsaye. maganganu ta gaya mata masu zafi da nauyi acikin ruwan sanyi agaban yaran snn ta nuna bacin ranta akan yadda tay watsi da girma da kuma darajar babban mace me hankali da suka bata aka damka mata amanar nur tare da bata daman zuwa gidan dantana kulawa da auren javeed din saigashi tazo ta maida abun kamar ego fight tana baza mulki da rashin adalci da rashin nitsuwa tanakuma zubar da mutuncinta agaban kowa.

kasa cewa komi anty suad tay tanata kuka har tanajan sheshhka ganin babu wanda ya kulata borin kunya kamar zai kasheta, wa ita mother ta bawa tokar files din nur din snn tace mata taje ta zubar awaje acikin ruwa me gudana.

ficewarta da tokar yasaka alhaj attah ya dawo gefen mother yanata bata haquri ayayinda duk sauran mazan suka dan shiga maganan musmn ma kamil mufasa sunata bada baki hajy amira ke zaune kusa da javeed kowa cikinsu dai yana magana.

anty suad tadawo daga zubar tokan kenan tazo ta samu javeed yanakan cewa inde zai zauna da matarsa anan gidan toh sai in har kowa ya tattare nashi ya koma inda ya fito sabida matarsa is enuf ta rike gidansu shi baiga dalilin da zaisaka mutane sutaru mata akai ba.. yanayi yana dan tausasa maganar amma kanaji kasan gaya mata kawai yake a kore su anty suad agidann ubansa dan bazai iya zama dasu ba matar sa nur da babansa sun ishe shi,

yana fadin hakan kuwa kusan kowa cikin mazan gidan suka hau goya masa baya...

hajiya amira kuwa ta dinga kawo korafi akan yawan zaman simran agidan da yadda ake bata wasu kananan dama da power da bai dace ba

shide alhaj attah baice komi ba anty suad kuwa kasa karasowa cikinsu tay tatsaya a kofa hawaye na zuba a idonta jin wai javeed yacema mother takore su akan nur firdaus itada gidan yayanta fa

a mugun zuciye ta aje tray din tokar ta juya zata bar falon mother ta kirawota ta dawo

hakanan ta sake nanata mata abunda javeed din ya furta agaban kowa snn tace mata ai tunda yanzu case yakare kuma kowa ya san asalin yarinya an gamsu dolene kawai ayi ma javeed da nur firdaus sabuwar bikin auren al'adarsu na karban amarya fully into the family sabida tana so ne marmaza aje can marocco dukkan atare da zubaida da kuma siddika da nur din tunda yanxu sune surkunayen gidan za'aje ayi initiation ceremony for the last time dan kowa ya san matsayinsa.

anty suad har taji wani sanyi aranta jin za'aje morocco tanata addua aranta Allah yasa ma jinin ahalin mufasa yaki karban jinin nur kamar yadda yay ma sauran matan
Chapter 155 · 0% Book details