← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 206

Sashe 16

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

takalle adnan da wani irin sabuwar kalar shaukin tausayinsa a kwayar idanunta ahnkli tace "I got to go
thank you so much..
...hawaye taga zai taru a idonsa tay saurin girgiza mai kai kawai sai yay ta maza yace "toh shikenan see yhou around. ya dada kallon fuskarta" yace babe ki gaida kawu abubakar pls kice masa na gode sosai.

...kawai dariya ta masa me sanyi.. snn ta ma matayen sallama bata ma jira sun amsa ta ba ta maida spec dinta saman idanunta ta juya cikin kamewa

nan sai ga layla data dawo daga washroom da ruwa baja baja akan fuskarta duk ya caccaba mata make up din cikin sauri ta karaso bayan taje taci uban kuka a bayi tafito har tana wani jan jan ajiyan zuciya aboye.

babu wanda yasan yaushe ta zame ta wuce washroom kawai gani akay tadawo

kai tsaye wajen nur din ta nufa suka dan yi nesa kadan da family kawai layla tafara magana kmar zatay kuka har zata fara ma mur complains cikin katseta nur din tace

its okay, 'ive send u sumtin a account dinki ynxu laylah..pls manage it.

nan tafara barin baki da kame kame big sis wallh kawai de banajin dadin jikina ne shiyasa kika ganni ahaka..dama wata magana.. ahnki nur ta kalleta cikin katseta snn tadafa kafadunta tace karki damu litle sis, Allah zai baki lfya
..ai aure da kudi na magananin duk wata damuwa, barema you neva needed me for anything barema ai yanxu akwai mummy.

nan ta bude jakarta ta ciro bunch na kudi ta mika mata a sirrince tace ga wannn kireke incase inwanda na tura miki yanxu bazasu isheki ba..and i hope ure happy.

layla dakejin kamar numfashinta zai sarkafe yakuma dauke cak nan take taji wasu kalar hawaye masu ciwo na shirin sauko mata cikin rasa abunda zatace ma nur, bakinta na rawa rawa tabudi baki zatay godiya, nan ma cikin datsar numfashinta

nur tace ahhh ahhh karki damu ba kudin karuwanci bane, is frm my pocket money da kawu yake bani ko wani wata...so, make sure u tell ur mum abt it kafin gobe tace na baki kudin karuwanci kin karba. hey, i got to go. ga can familynki acan suna jiranki kije ki samesu...bye little sis.

daga haka suka rabu laylah was sooo extra shocked ta tsaya da hawaye zirrrr duk takasa motsi dan kamar wacce akay mutum mutuminta hakanan tadinga kallon bayan nur firdaus harsaida tabace maganinta

nur kuwa ko ajikinta wai kadanji abun ya dameka sam ita bata wani ji komi ba dan inma akwai wanda ya nata tausayi befi adnan inta ba duk ta rasa yadda zatay ta sakashi ya iya mancewa da ita tunani tay aranta tace hala ko sai yaji ance masa tayi auren soyayya kafin nan hala zai saduda

tanakaiwa seat dinta kuwa jirginsu bai kara minti biyarba ya tashi aka lula da ita kaduna

da kyar da sudin goshi kafin nan layla ta iya dawowa hayyacinta tay marmaza ta share hawayenta ta dunkule kudin a gyalen abayan ta sann ta karaso wajen familynsun duk jikinta a sanyaye.

gani tay babu ma wanda yay mata kallo na biyu,kawai surutu ake ana raha ana hirar haduwar nur firdaus

tanaji dan uwansun yanace ma adnan cikin rahar audama wann ne nur firdaus din ahhh justice for Adnan daga yanxu ina bayanka. saikuma ya juya yakalle laylan atsakaninsu kawai suka kwashe mata da wata muguwar dariya.

Hajy mairam kuwa gabaki daya mamaki da wani irin damuwa saiya rufe mata zuciya dan ta mugun jimawa rabonta dataga danta adnan ya dawo cikin hayyacinsa at once haryana hira acikin yan uwa ana wasa da dariya haka dashi

gashi ma gabaki daya yarinyar batay mata kama da wacce ta shiga wancan trauma din ba..

wani tunani tay taga dama tabarsane ya auri wann hadaddiyar yarinyar dayake son din atleast she get to keep her son happy, da kuma rlshp dinsu ta uwa da da bai lalace ba dan gabaki daya adnan yanxu ya canza hali ya dawo marar kunya gashi bata isa ta hanashi kudi ba sai yabude safe inta yadauka ko tanaso ko bata so he is just terrorizing her life. saidai aikin gama yariga ya gama babu wani mafita.

tunda aka kama hanyar gida daga ita sai layla ne basa magana acikin motar

sauran kuma duk hirar kyau, haduwa da kayan jikin nur kawai akeyi da alama de gabaki daya ta burgesu dan dayan antyn adnan har googling jaka da blazer din jikin nur
tay waikoda zata samu irinsa ta siya amma sai taga ashe customed made ne

frankie yariga yasan za'ayi hakan,dolene wasu zasuce zasu kwaiwaye suturrar nur shiyasa yayi dwelling akan zallan hadaddun customised tailored outfits just for her inda ko kaje kasuwa saidai ka samu shigensa amma badai irinsa zak zak ba....

[22/04, 23:00] Anne-Aurora🦋: EPISODE 9🦋
SURAYYAHMS
wajajen Karfe bakwai saura jirginsu Nur firdaus ya iso garin kaduna, bayanta dawo gida kowa yay mata maraba sede Kafin ta yi komai wanka ta faɗa donji take jikinta har wani danko-danko yake mata. Ga ta da son wankan dama kamar agwagwa duk rana saitay wanka kamar sau uku balle kuma dataje tayi kwana ukun Abuja bata wani samu lkcin kulawa da jikintan sosai ba yau Hatta gashin kanta ji ta yi kmar yana mata wani kaikayi kaikayi..

Mikewa zaune tayi Ta warware doguwar bakin gashintan data dunkuleshi in a pony tail tashiga toilet din da ke cikin lapiyayyen dakinta,tsaye tayi na dan lokaci kamr wata mai nazarin bandakin nata wanda ke dauke da lafiyayyen babban bathtube na hollow cup jacuzzi, kalarsa white komai da ke cikin bandakin kalarsa kenan. Ahankli Ta mika hannu ta zare hair clip din da ta daure tulin gashinta da ya riga ya wargaje yazubo a kafadunta
,baki sidik mai wani irin tsayi da tsantsi protein hair mask, traditional shampoos, da non sulphurous conditioners kala-kala masu tsada dake a jere ta dauka inda kusan babu kalar da babu awajen wannan na da nasaba ne da yadda take bala'in son tsaftace komi nata.a lokacin ta manta da komai tashiga tara ruwan dumi cikin bahon wanka snn ta shiga ta soma abin da ta fi so a rayuwarta wato wanka.

Ta jima tana kalkale sassalkar fatar jikinta batare da ta tuno da komi daya faru a airpot ba, can kafin ta soma wanke sumar kantan bayan tayi conditioning dinsa da mint hair masque tana cudawa da kumfar bayan Ta kammala komi ta dauro alwala ta fito snn ta bushar dashi a handryer.

Doguwar rigar baccinta me laushi ta saka ta dauko hijabin sallarta ta tada sallah tajima azaune tana karatun qur'ani da muryanta me dadi sannan ta samu cikaken nutsuwa ta zauna ta soma cin abincinta acikin nitsuwa, brown spaghteti jollof da meat balls, A gefe kuma wani gasasshiyar meal din hanta ce a cikin bowl na tangaran ta sanya fork tana cin hantar a hankali bayan ta gama da jolof din. Da ta gama, ta kora da ruwa mai sanyi, sannan ta kishingida a sofar dakin tana dan hutawa nan tajivwani abu na tsantsan shauqin imani da tausayi na neman shigarta tare da tursasa mata tunani bisa yanayin yadda taga yar uwarta layla ta lalace duk ta rame
dazu dan harga Allah yadda taga laylah a lalacen yay mata ciwo

snn bazata iya tsayawa tuhumarta bane badon komi ba saidan tunanin halin makircinta da tay sai dan layla sosai tasha bata makurar mamaki musmmn ma lkcin rubibin aurenta da adnan yadda ta dinga mata rashin mutunci da rashin kunya, sede ko makaho yaga layla ayau yasan ba dadin rayuwar aurenta takeji ba tunani tay karkuma tafara kkrin taimakon ta tazo tasake juya mata wani makirci da sharrin a idon mrss haseena, besides
tasan yanxu layla tay wayo tunda ta iya zaman aure dan haka duk wani abu yaje ya taso mrs hasina zata iya dragging insa akan kawunta sannan tazubar masa da mutunci gara kawai ta fita a sha'aninsu

aranta tace inde har laylah na bukatar taimakon dagaske she wll look for a way to find her.

take ta kawar da wann tunani tafara tunanin birthday inta da zaizo nan da kwana uku gashi haryau Razia bata gama exams din ta ba bare ta dawo kamar yadda tay musu alkwari,itade bawai abun ya darata bane amma yadda taga matayen kawunta suka saka rai akan 18th birthday dinta yasa take son itama taga wann ranar
saidai harga Allah bataso ace razia tay missinh inshi att all

tunani ta dinga akan hakan har bacci mai nauyi ya sunkuce ta washe gari ta farka ta cigaba da normal life activities dinta na chilling ayayinda su hajya saadatu da hjy bilqis suke famar shirye shiryen mata simple home birthday party iyasu ya su.

ata fannin su layla kuwa tun ranar da suka hade nur a aiport bacci ya kaurace wa idanuwanta dan duk sanda tay juyi sai sabuwar kamannin nur din kawai take kallo, yadda nur ta wanku ta canza ta zama kamar wata yar shugaban kasa ya tsaya mata a wuya ya kuma razana kokon zuciyarta bana kadan ba dan abune wanda kwata kwata ko a mafarki batayi tsammanin gani ba,

irin takurarren feeling din nan kishi,nadama, haushin kanka, da kuma rasa nayi shiya shakurema layla hanyar fitar numfashi dagata mirgana nan sai ta mirgina can sai kaga zurrr hawayenta na sauka kamar ruwa

dan yadda suka san nur da sanyin hali da kuma tsananin haquri
sam batay zaton zata mance dasu da wuri har tay glow up haka ba. mrs hasina kam ma kullum tsammani take nacewa nur din ai zatagaji daxama a kaduna snn zata dawo taroketa gafara nd she is alwys convincing herself da wann tunanin, dan gani take ai nur din bazata iya tattara rayuwarta da komi nata ta zauna a wajen wasu na daban ba in ba wajenta ba.

abubuwan duniya suka taru sukama layla yawa akan kirjinta, tun tana iya nazari har tazo tarasa gane shin zallan zafin nadamar rayuwarta takey ko tsantsan kishi da baqin cikin ganin nur takeji.

yadda suka dawo gidan batako runtsa ba tun asbh takasa haquri takira mrs haseena, mrs hasina tana daukawa kawai tafashe mata da kuka
tanamai bata labarin yadda jiya taga nur firdaus a airport da duk wani abinda ya faru.
Chapter 16 · 0% Book details