← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 206

Sashe 90

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tana zuwa ta samu wajen a kulle gashi babu janet babu mr aqeel nan ma taci kusan minti 20 tana buga kofarsa amma sai shiru.

da azaban rudanin haka aranta tashare sauran hawayenta cikin sanyin jiki ta sauko dinning da tunanin ko zata samesa anan niyyarta koma agaban wayene kawai de zata tsuguna ta bashi haquri ta gaya masa ita ba haka halinta yake ba dan wallhi ita kanta batasan meke ma damunta ba tukuna.

tana shigowa main side din tun kafin ta karaso anty suad ta dinga masifa tana bambami na rashin zuwan javeed dinning na kwana biyu.

nur ta iso kenan aka gama maganar bataji lkcin da alhaj attah yace musu javeed ya dau helicopter ya wuce abuja just few minutes ago da gaggawa ba..

dan shi koda yabar sashen nur da bacin ran abunda ta furta masan, bawai zama yay ba, dan yasan inya zauna mata agidan yau hala zasu iyayin fada me zafi atsakanin su kuma shi baison ya tsoratata ko kadan.

nur ta gaishesu suka amsata as usual suka mata kallo da tunanin tasan inda javeed din yake sai kowa ya dan basar da hirar basu kara dagowa ba..

yauko daga ido ta kalle simran batay ba dan kirjinta banda bugawa babu abunda yakeyi gabaki daya da bata gansa anan adinning din ba sai taji kamar takara shigewa wani matsanancin damuwa ne ma.

banda juya spoon acikin abinci babu abunda tay ko sau daya bata kai abincin bakinta ba alhaj attah ne ke lura da ita baice komi ba har aka gama ta tashi da sauri ta koma sashenta da wann damuwar aranta da damuwar tazauna abakin gado tay shiru hawayenta na sauka kamr ruwa yau ko garden din bata fita ba.

Daga fannin javeed kuwa har ya isa Abuja bai dena tunani da jin nauyin abun daya farun aransa ba sabida abune wanda kwata kwata baiyi tsammanin nur zata taba iya furta masa ba

he blamed himself for being too cool with her, awani bangaren kuma sai yaji kamar fahimtar ta ne kawai baigama yi ba kode akwai laifinsa ata wani awaje, kai koma yayane duk dai simrance ta jawo masa wann masifar but deep within his heart yasan bazai taba iya kyale nur tana amfani da fushinta tana sako mum dinsa acikin kalamanta ba..

is highly intolerable harga Allah yasan bazai iya daukar raini ba duk dama yana matsanacin sonta aransa ya qudira cewa dolene zai mata horo sann zai ja mata layi akan mahaifyrsan saidai in zata tsanesa.

bai yanke hukuncin komi ba dan ma kar ya takura kansa da tunaninta yana sauka a Abuja ya dira acikin boyayyen training base dinsu.

kowa nata shan mamakin zuwansa dan duk basuyi tsamanin ganinsa yaudin ba yana zuwa ya shiga wani daki ya canza kayansa izuwa na training din sojoji .

suka shiga training tare da team of 7 men expert dayayi training dinsu akan mission dinsa a kwana biyun nan.

abubuwa sosai suka masa yawa a brain dinsa dan daga sama yasan babu hannun manyansa aciki sabida case din is a one way ticket ko ayi rai ko amutu gashi manyan kusoshin gwamanati dake juya kasar suna harkokin kasuwanci abubuwa dayawa da nagaza brotherhood shikuma gabar dake tsakaninsu is deeply personal bazai iya kyalewa ba

sabida tsoron me zaije ya dawo yasa gabaki daya ba'a asakamai hannu ya debi batallions dinsa ba iyaka dai seven men dayay training kawai zai wuce dasu.

baikuma gayama mahaifinsa ba dan yasan bazai taba amince masa ba, duba da haryau yana jinyar zuciyarsa akan sace shi da aka tabayi da kuma rasa mahaifyarsa yasan bazai taba yarje masa ya je ba inhar bai boye masa ba.

tun daga kan karfe 10 na safiya har izuwa karfe hudu na yamma suna filin training cin abinci da sallah kadai ke daga su.,

wajajen hudu da rabi dede sultan yazo da mota ya daukesa sukajesu wani hotel

suna shiga javeed baiyi wata wata ba ya fada wanka ya jima acikin shower yana tunanin abunda ma zaiyi ma nur amma bai samu ba har ya fito da towel daure akan kugunsa..

samu yay sultan yana kwance akan gadon yay kane kane yana waya wanda daga ji kasan da matarsa ce..

yana zama a bakin gadon zai shafa lotion ajikinshi yaji sultan yana kkrin sallama da matarsan sunata rikici irinna masoya har dai ya kashe dede lkcin javeed ya mike tsaye yana gyara zaman wandonsa daya saka yay gyaran murya uhum uhm yace toh barin kara da gaba indan nine za a kashe mata waya.

sultan ya dan runtse idanunsa a hnkli yana murmushi yace guy
pls tundaga shiga wankanka nfa muke magana,hmm ka ga wannan babe din wai ita mimie fitinarta yy yawa ne wallhy so take in gaya mata inda nake kuma ina gaya mata muna hotel zata fara min rikici tace nadawo gida ynxu, then she wll again lecture me on how much she trust me amma fa bata nuna min haka a aikace ya karashe maganan da karamar dariya

javeed dake famar gyara tsayuwarsa ajikin madubi yace hmmm toh ai baka da wani matsala inde haka ne u wont get what i am feeliing sai randa babyna tamaka rikici ga kishi dats becoming disrepectful.

Cike da yanayin rashin fahimta sultan Yace disrespecful like What do u mean..did u let her slap on the face you again.

javeed ya juyo ya kallesa yace Look I dont mean to bother you with all these stuffs but im serious. wani abu na damun brain din baby kwana biyun na amma fa banga lefinta ba duk simran ce, Right from d start simran ce ta lalata min chance dina na gaya ma baby komi yau din nan duk baby tay fushi sai wasu irin maganganu take gaya min wai banda tarbiya..

wani irin dagowa sultan yay ya kallesa da mamaki ahnkli yace what?..amma what actually happen datace maka haka

javeed ya kallesa sai kuma ya dauke kai baice komi ba ykasar wuyarsa yace just forget it

cikin zakuwa sultan ya juyo with serious face yace javeed aure fa baida manual pls man u need to get somethings ryt

wani irin hararasa yay tace daga wajenku magabata ko?

dariya sultan yay yace
"what eva, amma ni nasan zaman aure da yarinya chataf irinsu mimie da babyn naka ai ba abu bane me sauki, see am speaking frm experience, kai bari nagaya maka farko farkon auren mu ashakrar mimie tacika 17, i had to slap her one time sabida shegen rashin kunya. ranar naje wani harkata, i kept her in d dark yes, amma nayi hakane sabida in kare rayuwarta amma saida ta kureni har tasa na mareta ranar but at the end duk dai wnn yawuce kuma ta fahimceni yanxu
Da mamaki javeed ya kallesa cikin kyabe baki yace ohh dama soyayyar karya dai kukayi, kai ni bazan taba iya dora hannu akan baby ba..i mean no offense, but baby is just a girl..yaushe ma ta gama mallakar hanklin kanta.

sultan yana dariya kasa kasa yace shiyasa kakeso ka daura ma simran lefin komi kenan...?

cikin katsetsa javeed ya nemi waje yazauna yace listen, nam yahau tsagura masa dan abunda ya farun.. sultan sai kallonsa yake yana mamakin yadda javeed yake kaucewa dorawa nur lefin komi sai yace aisimran ce tajawo, duk dama kana kallon idonsan kasan abun ya bata mai rai but still shide yanama nur dinshi uzuri sosai

har saida ya gama labarin kafin sultan ya fara fayyace masa wasu abubuwan cikin fahimtar dashi cewa dolensa ne yabawa nur firdaus wani kalar tarbiya da zata dinga kallon kimansa dashi snn yadaure yana nuna mata kuskurenta sabida indan yasake ta taso ahaka da izgili nan gaba bazai iya gyarata ta sauki ba.

yi yay kamar baijin shi amma kuma maganan makes sense to him sosai. gaskiyar sultan ne da akwai some basic form of respect da zai iyakoya ma nur da kuma yanayin tarbiyan sa da zai iyadorata akai inhar yanason zaman lafya me dorewa ya wanxu atsakaninsu.

haka suka gama maganan har aka karkare amma yaki sam yay admiting cewa nur tayi masa lefi sosai, amma duk yaji komi kuma ya kuma fahimce shawarar da sultan ya bashi akan ya dauke mata wuta yay grounding inta dakansa ya koya mata cewa akwai basic respect a tsakaninsu sosai.

a lagos kuwa yanayin damuwa da nur tashiga yasaka ko simran bata samu fuskar kawo kanta sashen ta kamar yadda ta shirya ba kawai saita shirya tabi hajya zuby sukaje duba sabon asibiti da alhaji attah ya dorata akai tun bayan karyawan su nasafe.

yau kwata kwata kamr marar lafya nur ta zauna dan ko su naima basu gane kanta ba, taki sam taci abinci mai nauyi sai tunanin maganan data furta masan takeyi tana dada jin kunya da nadama da kuma mugun fargaban abunda zai biyo baya

rashin jin duriyar javeed agidan yasaka ta dada zaucewa ta rasa sukuninta da kyar naima ta lallabata suka fito garden da yamma wajajen karfe hudu....

nan ma duk abun tabawa da aka kawo mata bataci ba wani bin kawai mamakin kanta takeyi da har ta iya furta masa wnn maganan...

Wani katoton pool ne ke shimfide awajen data gaji da zama ta koma bakin pool din ta zauna ta rafka uban tagumi...
[21/05, 21:36] BLUE💙: EPISODE 57
AREWABOOKS@ SURAYYAHM

karar ruwan na zuba amma ko kadan bataji dan tsabar tay nisa cikin tunanin javeed batama lura ba saida taji muryan na'ima adaf daf tana dan cewa hajiya hajiya
...ranki shi dade hajiya you have a visitor..

adan firgit tajuyo sai kuma suka hade ido da alhaj attah da hadadden bakin walking stick dinsa yana karasowa cikin wajen wani doguwar farar jallabiyace ajikinsa da hularsa irin tabani kasha hadisi din nan shikadai ya taho.

matsanancin mamakin ganinsa ya sata mikewa da sauri ta karaso ta wajensa tana kakalo murmushi naima tarusuna har kasa ta fara gaishesa snn tay marmaza zata bar wajen yace mata tadawo shi ba jimawa zaiyi anan ba

nur tana tsugunawa agabansa ya dagata yace mata su zauna akan kujerar tukuna
Chapter 90 · 0% Book details