← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 206

Sashe 133

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ji yayi hawayen ta na tsokalo masa nashi kamota yayi tareda daura kanshi akan kirjinta ya rungumeta a hankali da disashen muryanta tace "thank you for saving my life and i am really sorry da irin zargin dana maka abaya...i am just scared, bana son ka rabu dani niban taba son wani namiji kamar yadda nake sonka ba, i was mad, and angry..i dont want to lose you..cikin hawaye take maganan tana kuka tayi kissing dinshi muryan ta adishe takuma kankameshi sosao ta sake cewa "thank you for sharing ur world with me wallhy basai ka tsananta min bayani ba na fahince ka,na dade da sanin kai mutumin kirki ne...ni banda karfin ikon hanaka zuciyata dan Allahne ya riga ya mallaka maka shi tunranan dana fara saka idanuna akanka Dukkan abunda kayi min arayuwata,mai kyau da marar kyau dukkansu na karbe su amatsayin qadadarar snn rayuwata nayi maka alkwari i wll be the woman u want me to be for you..i wll neva leave you zan tsaya maka duk rintsi duk wuya,, i love you..im ready to take any risk to be with you i cant breath witout you.

Bai amsa ba yabi dukan hawayen nata da kiss kafin chan ya saketa tareda dagota sama suka mike tsaye yanata kallon fuskarta kamar wanda zai hadiyeta da ruwan idanuwan sa mecike da tsananin nuna yarda da kauna me zafi...

maida masa irin kallon takeyi duk idanunta sun haura sunyi jaa tsabar kuka

hanmunsa na dan rawa ya tallafo ta ajikin shi yana me fadada wata sssnyar murmushi yace Allah ya maki albarka mrs mufasa, baby i swear i wll make it up to you i wll love love you koda wata rana kin koreni i will fight u and stay untill u love me over and over again

...a matukar kunyace tay murmushi me sauti sai kuma ta fada kan kirjinshi da kyau suka rungume junansu sosai tana mai sauke masa nannuyan ajiyan xuciya mai nauyi

sunfi minti goma ahaka kafi nan Ahankali ya cirota daga jikinshin

wani abu ya danna kalan wutan dakin ya komayin haske sosai a hankali ya daura hannunshi kan fuskntar ta ya shiga goge mata sauran ragowar hawayenta

sann ya Kamo hannuntan suka zauna abakin gadon suna me sauke idanunsu acikin na juna kusan babu abunda yake mata yawo akai yanxu banda fargaba da damuwar shiga sabon salon duniyar shakuwa da rayuwarsu ma aure zai dauka wanda bata san ko zaizo mata sauki ba bayan sanin mummunan tarihin data aje abaya na samun fyade da yin cikin shege da kuma zubewa..

anty razia tace mata no body has the ryt to her past or personal life..but deep within her hrt tana jin kamar javeed bazaiji dadi ba inya tabata yaji cewa ita ba virgin bace and she just cant tell him abt her past ryt now sabida yana mata mugun nauyi kuma bazata taba iya tona asirin gidansu ko na mahaifyarta agaban namiji ba duk son datake masa komin lalacewar mrs haseena ita ta kawota duniya she just cant mention her story batareda tay mummunan tona ma uwarta asiri ba.

tana mugun tsoron ace mijinta ya fahimce cewa mahaifiyrta bata kulawa dasu kuma bata da mutunci, kuma tana kan zarginta da jawo hankln mijinta har yay mata fyade...she just cant even imagine maizai faru inhar javeed yasan cewa mijin uwartam ne yay raping inta kuma har ya mata cikin shege inama ace da wani saurayi ne daban to da sauki but this is too personal and damn heavy to utter..

suna zaune abakin gadon sai yaga tadan firgita ta mike tsaye batareda ta amimce sun kara hade idanunsu ba tay sauri ta wuce bathrum ta kulle kanta
aciki tanajin wani irin matsancin rudani da damuwa mai gigita zuciya da kwakwala

tasan duk yadda akayi tunda har sun shirya kansu da javeed dolene zai bukaci yaji duminta but she just cant figure it out.

in tabarsa ya tabata yau inya tambayeta akan budurcinta me zatace masa?? and worst part what if yajita wani irin kuma be tambayar ma yafara bata silent treatment har soyayyar dake tsakaninsu yazo ya ruguje....

tunanin da takeyi kenan har javeed har ya gaji da jiranta akan gadon ya sauka ya fita domin gabatar da sallahn magrib da isha'i.

fitarsa keda wuya itama tay alwala ta fito jikinta dik a sanyaye tarasa wani shawara guda daya zata dauka shin ta nitsu tagaya mai komi ne ta zubar da mutuncin kanta dana mahaifyrta koko kawai tay shiru nata rayuwar yacigaba da rugujewa tareda wanzar da rudani da rashin yarda acikin zuciyar mijinta wanda tasan dolene zai haifar musu da rashin yarda da gushewar tasirin da son dayake mata a zuciyarsa...

duk ta rasa wanne ne guda daya zata dauka tay zugum tare da rafka uban tagumi....
[04/06, 22:54] BLUE💙: 80

Daga ta dayan bangaren kuwa gabaki daya su anty suad sun karkare shirinsu sun kashe kudi sun hada karamar liyafarsu na yima javeed suprise tun four oclk kowacce ta kure wanka ta fito wajen hidima anata jiran janet ta sanar ma javeed ya fito

cikinsu kowa ya gama kumtso makircinsa acikinsa hajy zubaida dake cikin damuwa ne kawai bata fito wajen ba

tun bayan asr suka aika acewa janet tasanar masa ya fito karamin falo abu tun na wasa wasa har biyar ma yamma yayi basuga fitowarsan ba

anty suad duk ta kule ta dauka ko shiryawa yakeyi ko jan aji ne irinna marasa lafya saidai inaaa dataga sun sha jira kusan na rabin awa ta hatsala taje sama sashensan dakanta nemansa lady sid tana biye da ita abaya

janet data san zasu iya tutsiyeta tana jin zuwansu ta boye kanta tay kamar bata nan mr aqeel kuma bai fiye son sake fuska da surutu ba koda tazo tana hucin abude mata kofa baiko mata bayani ba yabude mata haka ta duba koina dakyau ta tabbatar makanta cewa javeed bayanan sann ta fito ta wuce kai tsaye sashen nur firdaus zuciyarta na tafarfasa da tunanin nur din ce ta makale shi tahana sa fitowa.

tun basu tabbatar da hakan ba lady sid take cewa "anty ai nagaya miki yarinyar nan nunawa take kamar tafimu sanin zafin javeed idan akayi wasa wllh wallh nan gaba saida izininta javeed zaina mana wasu abubuwa agidan nan

babu kalar zugar da bata cusawa anty ba ita kuma sai huruwa take kamar kububuwa suna kaiwa sashen ko sallama batayi ma na'ima ba ta fara ihin sunan nur firdaus daga falo hoping dat in javeed yana ciki ai dolene su fito atare

na'ima tay shiru tana kallonsu har saida suka gama ihunsu sukayi bambami sukayi shiru kafin nan lady sid tafara tambayarta inda nur takai javeed naima tace ita bata gansu ba..duk tambayarsu haka naima taki gaya musu komi dan tasan karshe akanta zasu dawo da masifar tace musu itama batasan ina nur tayi ba tunda sukaje breafst bata gan nur ba

hakanan suka kyaleta suka dawo kasa wajen hidimar suka zauna sunata masifa kamar zasu daga gidan, inda sosai abin ya daure ma simran kai hakanan sukata jiran tsammani har saida aka kira sallahn magrb alhaj Attah ya bude sashensa ya fito kenan zai wuce masallaci anty suad ta tsaresa da maganan har tana huci wai ko yasan inda nur takai javeed

shi abun ma dariya yabashi yadda suka dau zafi suka haura sama da zafin zuciya suna tsammanin nur ce ta dauki javeed ta boyeshi...

dan ya kashe maganan yace musu suyi hakuri kawai amma dazun nan javeed yace masa zai dan huta baison kuma a damesa kuma tunda har baya nan zai iyayuwa yabar kasar nan ne da matarsan dan ya samu isasshen hutu bawai nur din ce ta daukesa ba..

tunda alhaj attah ya furta hakan ya wuce abunsa looking so unserious da reaction dinsu yasaka anty suad hargitsa da fushi tay fata fata da su cake din da sukayin ta haura sama da matsanancin fushi daya ci uban wanda ta shaka da safe..

yanayin borin da bacin ran data haura saman dashi yasaka lady sid ta kasa binta sama simran kuma ta zauna tay tagumi tana matsa hawaye dan ita samun hutun javeed bai dameta ba amma zuwansu da nur din shine yanzu yafi daga mata hanklinta harma fiye da zawon jini datakeyi babban fargabanta kar azo ace nur tana da cikin javeed danji take kamar ranar ne ranar mutuwarta.

tsabar damuwa da bacin rai tare da rudani batasan ma sanda takama jelar kababan kayanta data saka ajikinta ya mata muni kamar da tafito daga kabari ba tahaura sama can cikin dakinta
ta zube akasa tana kukan da bata san kalar ciwon sa ba.

wai kenan haka zata zauna wata yar kwailar yarinya tazo ta kwace mata javeed inta a idanunta????

anty suad kuwa ta inda take shiga bata nan take fita ba dan awajenta komi daya faru leifin nur ce acewarta idan suka bada fili nur sai tafi mahaifyar javeed walakantasu agidan mufasa dan haka tana nan tanajiranta zata dawo ta sameta zata nuna mata asalin wacece suad...gani take kamar sanyin datay kwana biyu yasaka ake mata wayann abubuwan ace har javeed zai dau matarsa subar gidan bata sani ba basu gaya ma kowa ba thats the height of disrespct

Abangaren nur kuwa cikin rudani da tagumi ta zauna tay zugum akan dadduma dan babu kalar lisafin da batay ba.

saidai abune mai matikar nauyi ta rasa yadda zata fara xubar makanta da mahaifyta mutunci agaban javeed snn awani bangaren mahaukacin tsoron rashin fahimta da kuma rashin yadda da zai ginu aransa inyaji ta ba cikakkiyar mace ba take jiye makanta sosai.

dan inhar tay shiru wani abu ya shiga tsakaninsu koda baice mata komi ba tasan har abada zata cigaba da zamane acikin tsarguwa da damuwa, inkuma tafada mishi komi gabaki daya batasan yadda makomar mutuncinta dana mahaifyarta zai kasance a idanunsa ba
Chapter 133 · 0% Book details