← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 195 OF 206

Sashe 195

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

washe gari sassafe wajajen karfe 6:30 result ya fito, likitan daya mata aikin dakan sa yazo gidan ya musu bayanin kalar poison din da simran tasha, ko ince aka bata tasha, da kuma harbin bindiga dake kafarta wanda alama ne na nuna she was trying to escape but got shot. yace musu nan da awa daya idan basu binneta ba zasu iya jawowa gidansu wari mai daga hankli

likitan nagama bayani
ya fice abunsa ayayin da sai ynxu mahafin simran ya amince cewa tabbas yarsa ce haka, cikin tsananin baqin ciki ya fara kuka yana tsinewa zubaida yana cewa itace ta jawo ma simran wnn kalar rayuwar.

ita kuma taki sam ta aminta da wann tuhumar tace mishi komi laifinsa ne, shiya sakalta simran ya nuna mata duk abinda take so a duniya zata sameshi, snn ya daure mata gindi da kudi, baya nuna mata tay badaidai ba, ta basa misali dayawa na yadda tadinga discouraging din simran tana mata fada akan relaship dinta da javeed mufasa amma duk taki.. karshe ma ta gaya masa cewa ai duk kudinsa dayake ji dashi din dashi simran tayi siyayyar kayan aurenta in karya take kuma ya duba ya gani he is just a sad, old, drunkard man, who is finished and broke.

maganganu masu zafi
suka gaya ma junansu saidai dake hajy xubaida tafishi gaskiya yasaka yafi gigituwa da nata kalaman bana kadan ba.

jikinsa na rawa ya dauki ipad dinsa ya duba duka business acct dinsan kuwa yaga babu komi aciki face 790$ cikin rikicewa yake tuhumar zubaida yadda akay tabar hakan ya faru ita kuma ta cigaba da gaya masa yadda ya lalata simran baijin maganar kowa sai nata shiyasa itama bata cewa komi

runtse ido tay tana gaya masa bakaken magana masu zafi wanda tun yana tsaye yana jinta har ya sare ya fadi kasa timmm
ya rike zuciyarsa tammm yana wani irin razannane gurnani gashi dama ko sallah bayayi dama..

he jerk and convulse for a minute shima sai ya rasu.

wani irin rusa ihu hajiya zubaida tay tana birgima tana furta ta shiga uku

atakaice dai wa mahaifin nata kawai akayi wa wanka simran aka yayyafa mata ruwa sabida kowa na jin tsoron gawarta, baqin ciki akan baqin ciki da mutanen anguwarsu sukaki xuwa sallahn babansu sabida ba ataba ganinsa a masallaci ba, wasu ma basu san wai musulmi bane an dauka irin free thinker din nan ne sabida
tsabar rayuwar gayu da mugun shan giya da lalata kananan yara yan university dayakeyi agidan nan nasa.

daga ita sai wasu tsirarun kawunansu da sukazo by 9:30 am aka kai simran da babansun kabari aka binne su. daga nan kowa ya kama gabansa aka bar ta ita kadai.

tsabar baqin ciki ta dawo gidan ma ta samu 90% daga wokers dinsu sun kawo takarda wai sun bar aiki sabida wata shida kenan ba a biyasu kudinsu ba gashi megidan yau ya rasu gaskiya bazasu cigaba da aiki ba.

wanda suka zauna kuma ba amfanin komi dama suke musu ba ,bottlers ne masu serving giya ba sai mai gadi, sudin ma dan suna morar Aprtment din gidan ne basuda inda zasuje.

just like dat duniya ya zama empty a idon hajiya zubaida,tay kukan tay zage zage tay kulle kullen nadama duk zafin bai ragu ba.

gashi babu wanda ya kara kirarta koda acikin yan uwa ne gabaki daya duk wani karfin zucyarta ya rushe zazzabi me zafi data jima batayishi ba shi ne ya rufeta.

daga mufasa mansion kuwa everything seem fine, washe gari da sassafe nur ta raka javeed har gaban jirgi ya wuce abuja akan cewa da yamma zai dawo ayi shagalin tare dashi.

kafin kace wani abu anyi decorating gidan an gyara koina kamar hidimar gaske

ita da razia sukayi special cakes kala kala akayi full sweet package of snacks and gifts for all the workers aciki akwai sabbin park na new uniforms da nur ta tsara musu againts fomer unform da hajiya zubaida da simran suka sauya ma kowa..

muslim wokers will now wear mini hijabs loose uniform shirt and trausers, turqoise da navy blue for all general workers, dark green and white for doctors and nurse, private workers na cikin gida kuma beige da burgendry. security da gurds all black, da charcoal grey. sai ceremonial dresses na duka wokers is eida lavender, lilac and creame.

razia ce ta tayata shirya komi da kuma yadda zatana kamewa dan tana maintaining power akansu dan acewarta true power is not in strenght but in peacful submission,wanda kake tare da shi kullum agidanka shine zaka fara kyautawa kafin na waje.

da sassafe aka raba musu uniforms dinsu and the whole wokers in the mansion were so happy about it sabida yadda aka karama wasu da saka hijabi wasu kuma da dora dankwali..

kafin kace wani abu kowa ya sauya cikin sabon uniform dinsa and they all look amazing and calm in it. dan islamiyar da ake musu sau biyu a sati acikin babban hall na gidan dacan shima sai yau aka basu damar sake budewa dan dama mhaifyar javeed ne ta kawo wann salon tana rasuwa kuma hjy zubaida ta datseshi.

fannin hajy zubaida kuwa amugun gigice ta farka daga mugun zazzabin daya rufeta gashi tun jiyan bataci komi ba sai mafarke mafarken datakeyi wai babanta ya dawo saurayi amma kuma sai tagansa acikin ruwan wuta yana ihun azaba fatar jikinshi na narkewa simran kuma an nannadeta sosai ajikin wani jaann karfe da gashin doki dake kanta wanda ta rasu dashi.

wann mugun mafarki bakaramin daga mata hankli yayi ba, ta rasa me ke mata dadi duk da kwanan yunwa datay bataji abunda ya dameta kamar mafarkn nan ba.

adan dole taci abinci waikoda abun zai fita mata arai amma ina fuskar simran dana babanta acikin wutar take kallo, hakan yasaka ta dauki giya kwalabe shida ta zauna ta dinga sha har saida ta fice ahayyacinta awajen ta fadi tay baccin mutuwa almost 8am na safe to 4;30 pm na yamma dats a whooping 9hrs nap ta farka da hang over tana neman abinci sai wayarta ya fara ringin

ko dubawa batay ba ta dauka ta dora bisa kunnenta sai taji mr manny ne, dake tana cikin wani yanayi na baqin ciki da tashin hankli masifa kawai ta masa ta hau gaggaya masa kalar ruwan balain datake ciki sann ta masa gatse tace masa zatazo ta samesa bawai guduwa tay ba

da mamaki taji wai ko tausaya mata baiyi ba yace kwana daya tal ya bata inhar batazo masa ba wallh saiya tona mata asiri a yanayin da batay zato ba he wll make sure mutuwarta yafi na simran snn ya ktse wayarsa.

wann barazanr da manny yay mata yasaka adan dole ta aje jimaminta agefe taci alwashin xuwa gidan mufasa domin taji menene asalin kan labarin,waye ya kashe simran meye tayi? dan ta rantse saita dauki fansa koma yayane saidai ita bazatay dabbaci irinna simran ba.#SURYYAHMS
Da yamma cikin gidan mufasa ya cike da yanayin nishadi gashi sun shirya hidiman yay kyau bana kadan ba nur tasaka kayan ta which is blush baby pink. Color Scheme na wajen kuma are soft, joyful colors White, gold, and sage green Baby blue, mint, silver koina akasaka Balloon Arches da soft pestel of Garlands, akay hadadden throne chair ma “Mom-to-Be” Decorated with florals, and a soft white fabric canopy me dauke da Backdrop Banner an rubuta "Glowing Mama" ajiki....

wajen sosai yay kyau paper flowers, fairy lights, neon signage, Mini bouquets in jars, Confetti, baby blocks, candles and themed plates and food napkins.

sai akayi long table of Dessert me dauke da Cupcakes, cookies, or cake shaped like baby items da ababen sha kala kala na zamani, sai katon Memory Corner me dauke da Ultrasound photo frame duk wanda yazo zai dauke hoto da mom to be, he wll gift her a baby journal, or prayer cards masu cike advice for Mama and Wishes for Baby.

tun karfe hudu da rabi aka fara taruwa by 5pm ma yamma the whole entire mufasa sukama nur suprise visit sukazo wajen dkansu akayi hidmar tare dasu.

it was such a happy and joyous party with white Smoke bomb, confetti, balloon, cake reveals and color-changing drinks ga games da akeyi tay na nishadi irinna baby powder scented candles and diffusers din nan

Razia ce kawai bare sai lady siddika amma duk sauran ahalin mufasa ne, Wani irin dan uban nishadi akeyi ana ta mosharewa manya da yara dukan su basu ko lura da isowar hajya zubaida gidan ba.

itakanta koda ta iso taga irin nishadi da shagalin da akeyi
saida taji kamar ko mafarki takeyi yadda taga anty suad da alhaj attah sun sake jiki acikin yaran ana matured and funny baby games, the baby uncles and the father himself, it freaks her out soo much to see javeed in d mist of his cousins playing games and laughing so hard wanda abune dayake nan so rare, rabonta da ganin dariyarsa me yawa ma bazata iya tunawa ba.

tafi minti talatin me kyau tanata kallonsu tanajin kanta kamar giyan ne bai gama warwarrewa bane ko ta shiga wani duniyar ne oho
,
dakyar dai ta kwaco hanklinta sai kawai tanufi sashenta a sama tabi ta haura dakin simran din ta fara tattara muhimmn kayanta da takardunta

tanayi tana kuka me tukuki wanda har kasar ranta takejin zafin komi dayake faruwaa bana kadan ba, kuma ba komi ya kara damunta face yadda tazo taga mutuwar simran yazamo banza a wann ahali, so nobody even feel remorse, or give a damn minute for her..

life just move on jiya jiya ta mutu amma suna nishadinsu kamar basu taba ma saninta ta a duniyar nan ba.

ciwon da hakan ya mata aranta saima yafi wanda taji jiya zafi
dan da wani irin fushi ta qudura cewa ta rabu da gidan nan kenan dan ita ba simran bace da bazata iya rabuwa dasu ba ko tay ta zama kamr wacce batada xuciya

she cant stay with ppl dat throw a big party untop her sisters demise taji mugun zafin abun aranta bana kadan ba.

tagama tattara iya abubuwan su masu amfani kenan zata fice sukaci karo da lady siddika data fito amsa wayar business a sama.
Chapter 195 · 0% Book details