← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 206

Sashe 143

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

anty suad datagaji da kwainanensu abazata cikin bacin rai ta fauce file din with no excuse ta mike tsaye tafara karantawa da karfi kowa najinta...

sirrikan nur ne take fayyacewa a fili dan yadda jikinta ke rawa yasaka duk suka mike tsaye lady sid ta dinga kwaroro salati tana jin kanta kamar a mafarki

..ahakan ma saida hajy zubaida ta dinga sakaya simran aciki tana mai nuna musu cewa ai simran dince taji labari sai tay bincike kuma sai taketa son taboye musu maganan dan a rufa ma javeed asiri sabida tsananin son datake ma javeed batason ace ita ta rabashi da nur firdaus dinsan tunda dai ita ya zabar ma ransa yace yana so.

tana matsa hawaye sai tace ita kuma duk dama ahalin mufasas basu dauketa uwa ga javeed ba amma gaskiya bazata iyayin shiru akan wnn maganar ba sabida wata rana in gaskya labarin nur ya fito ta kunnen makiya duk mutuncin ahalinsu ne zai zube gabaki daya.

anty suad da dama already tsanar nur din ya ginu aranta batama tsayayin wani bincike ba tasauko kasa ta fice a dakin tay hanyar falon alhaj attah babu ko takalmi akafarta fuuu kamar iska

duk matayen suka hau binta baya dan tsabar makirci simran har wani kuka take tana kama rigar anty suad din tana cewa wai a rufa ma auren javeed asiri ..

babban falon alhaj attah sukayi daidai ya shigo ciki kenan yana waya da javeed din yana daf da katsewa kenan kururuwar kukan simran ya fara katseshi wanda ko sallama baiy ma javeed dinba ya katse wayar ya juyo yana ta kallonsu yadda suka shigo masa gatsau kuma ahaukace babu sallama bare gaisuwa

ga tashin hankli da hayaniya da kuma uwa uba anty suad data gama kumbura tay famm fuskarta yay jaaaa sosai duk jikinta karkarawa yake da matsanancin baci rai..

tana zuwa a mugun zafafe ta jefa masa da file din nur din akan glass table din dake gabansa lkcin kansa na daure ko tabawa baiyi ba ya dubesu da dumbin mamaki yace kee suad lafya kuwa? daidai nan anty suad din ta sakar masa kuka mai tattare da zafin xuciya da diri

within spec of some minute ta zazzage masa labarin komi tareda tulin dumbin tsanar da takeyi ma auren javeed da nur firdaus tanamak kirar nur din da karuwa wacce tay cikin shege ta kwabar kuma babbar macuciya snn tace masa bazata taba yin shiru ba saidai ya kira javeed din suxo nan shida matarsan dan suji gaskiya abakinta dan bazata iya kallon wnn abun kunyar cikin ahalinsu ba.

kirjinsa yaji ya rike da wann labarin dan he find it very absurd ace wai nur ce da wnn mugun tarihin kai saidai in wani makirci su xubaida suka laka mata..

duk diri da zafin zuciya da kukan da anty suad takeyi anan baice mata komi ba dan yasan hanya mafi sauki na warware komi shine aji other side of the story abakin javeed a tunaninsa koma miyene game da nur dolene javeed zai sani tunda yasan dolensa zai zurfafa bincike akanta kafin ma ya tunkareta da maganan aure.

daga can javeed ya gama Re-trying lambar babansan bai dauka ba ganin lkcin da sukayi zasu hadu da nur dinsa awajwn dinner na wucewa yasaka kawai ya kama hanyarsa ya shiga gidan domin ya shirya kansa yaje private dinner din data hada musu ya sameta acan
..

bai wani saka komi aransa ba yahau shiri saidai wandonsa kawai yasaka yanakan shirin saka rigar saiga kirar babansa ya kara shigowa bai dauka ba saida ya kammala saka rigar yay tsaf jin kirar yay yawa saiya dauka sai yaji muryan babansan wani iri ga kuma koke koken anty suad dayake shakowa

tun anan yafara tambayar ko lafya amma baban nasa sai baice mai komi ba yace masa marmaza kawai yabar duk abunda yakeyi yanxu ya dauko nur firdaus sutaho gidan yanzu nan. javeed ya daga wayar a kunnensa da mamaki ganin wai har ya katse masa waya

agaggauce bai tsaya yin wani tunani ba ya dau agogonsa da jacket dinsa ya fito ya samu nur tay mugun kyau a red dress dinta tana zaune like an angel tanakan jiransa

kallo daya yay ma wajen yadda ta gyara shi yay masifar kyau duk sai yaji baiji dadin da zaiyi ruining mata wnn moment din nata ba

da murnanta ta mike data gansa yazo, sai kuma tagansa da dogon coat dinsa ahannu muryansa a tausashe ya taho yay kissing din goshinta yace mata tay kyau snn yace mata tay haquri zasuje gida ynxu amma ya mata alkwari komin dare zasu dawo suyi privte dinner dinsu zai kuma saurari abunda zata ce mai...

bata musunta masa ba tace mai okay ,ya karasa saka long coat dinsa akan casuals din dayasaka data mai kyau bana kadan ba, ya riko hannunta suka dawo dakin ta canza kaya sharply ta saka plain abaya blacl colour zuciyarsu duk ba asake ba suka shiga mota suka kama hanyar gidan agaggauce.

sai satar kallonsa nur take duk ta rasa meyene yake shirin faruwa ganin kamr shikansa hanklinsa baya jikinsa sosai

9pm on d dot suka iso cikin mufasa mansion lokcin har kura ya dan lafa sun zazzauna banda alhaj attah dake rike da file din yana tsaye yana dada latsa wayarsa yana verifying komi da secret scanner dake jikin xobben azurfa dake hannunsa.

what really borders him shine da baiga alaman fake news aciki ba..

kowa dai yay shiru banda anty suad dake karkada kafa tana wasu irin munanan maganganu akan nur firdaus tana cewa dama can tasan auren nan bazaije koina ba kawai anyi shi ne dan sabida ana daure ma javeed gindi ana fifita shi sama da uban kowa dan gani take kamar aidolene ma ace javeed yasan da wann maganar kawai boyewa yay dan ya raina musu hankali sabida baya darajasu kuma bai dauke al'adar ahalinsa da mutuncin gidansun abakin komi ba shiyasa har zaije ya auro wacce tagama watsewar ta akan titi tay cikin shege ya kawo musu gida a matsayin matarsa na aure.

ita babu ruwanta da details kawai abu biyun nan ta rike na cewa nur ta taba cikin shege ta kuma zubar shiyasa tabar gaban uwarta ta dawo zama a kaduna. iya nan kawai ta rike ta dinga zafafawa kai kace shine kawai labarin data gani bata ga cewa case na barayi da kuma rape bane.

nur bata tashi jin tsananin faduwar gaba ba har saida ta suka sauka a mota taga javeed ya wuce gaba cikin sauri like he is tensed gabanta na faduwa sosai tabiyosa abaya.

tafiya take gabanta na faduwa har suka yi sallama cikin falon wanda kafin tadaga ido taga duk su anty suad sun mike tsaye suna mata wani irin kyamataccen kallo

anty suad din tana wani huci kamar zatayo kan nur din ta kamata da duka lady sid tay marmaza ta rirriketa tanata cewa haba mummy calm down mummy dont attack her wallh wallh ba girmanki bane alhamdullh tunda zmsunzo aiyanxu gaskiyar zai fito

maganan yay ma nur wani iri jikinta sai ya fara rawa rawa kadan

rusunawa javeed yay ya gaida babansa daya amsashi dakyar
nan nur dinma ta gaishesa da sanyin murya sai kawai ya kalleta wani iri bai amsata ba..

acikin dauke kai tunma anty suad bata fara nara reaction din ba ya dago ma javeed maganar background na nur firdaus..

kai tsaye javeed ya gaya masa iyakan abunda ya sani akan halayyarta wanda tun bai idda ba anty suad tahau masa ihu tana cewa karyane.. karya ne...macucuiya ce..
watsatsiya wacce ta gama zubda kanta wa maza tay cikin shege ta xubar snn ta gudu agaban uwarta tana faking nitsatsiya..

duk dai javeed baiyi wani reacting ba duk da kukan dayaji nur ta fashe dashi sosai musmn da babansan ya fara tambayarta akan dalilinta na barin Abuja yana tuno mata batun case din cikin sam taki tace mishi ehh ko a'a kanta kawai ta sauke kasa tanata kuka maicike da radadi da kuma matsanancin tsoro..

ko dar dar javeed baiji aransa da shirun nur ba har saida babansa ya fara masa bayanin komi calmly tareda tabbatar masa cewa tabbas nur ta aikata abunda ake zarginta dashi, sabida he even scanned it,..kuma ya lura da cewa angoge information dintan ne a media news but all of it is on the dark web kuma duk sune
aciki file din nan..

anty suad kuma har iyanxu sai tambayar nur din take azafafe
ta gama hatsala wai saidai ta furta musu agaban kowa tace musu eh tay cikin shege ta zubar da bakinta..

nur kuma tay shiru ta rufe fuskrta da veil din abayarta tanata kuka sosai batace komi ba

javeed duk sai yaji ya rasa abunda zaice yay shiru dan wnn karon ne na farko dayaji brain dinsa ya kasa daukar magana a bugu daya ahnkli ya juya yana kallon nur dayaga yanayinta sai yaji komi nashi ya tsaya cak numfashin sa yazo masa har magworo yana neman shakesa dan atake idanunsa yay wani irin kadawa yay jaaa

ga ihu da anty suad take musu tana zage zage saidai nur ta bar gidan cikin daren nan saboda aganinta ai shirun da nur tay ma babban amsa ce

cikin lunshe ido da budewa javeed yay tsam yanajin how utterly shaky and dispointed babansa yake fidda wasu maganganun duk dama ahnkli yakeyin sa amma yasani in har yace zaiyi yunkurin defending din character din nur anan wajen yanxu haka bamai fahimtar sa gara yay shiru...

karasowa gaban babansa yay ahnkli yace masa yana so yabashi dama yay magana da nur din privately tunda dai matarsa ce koma miyene she wll be able to tell him amma ba agaban kowa ba...

yarje masa da baban yay ma bakaramin bori anty suad ta tayar ba saidai bai kulata ba

javeed ya juya batare da ya kalle nur ba ya fice a falon bata san ya akayi ta fara binshi cikin sauri tanata kuka ba dan kodaga yanayin tafyarsa tasan ba adaidai yake ba.

yana isa sashensa tun baikai ga kofa ya daka wata uban tsawa wa su mr aqeel cikin bacin rai inda arazane suka bar wajen ya zamo daga ita sai shi.
Chapter 143 · 0% Book details