← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 206

Sashe 160

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fannin anty suad befr 12:30 na rana ma ta gama da batun kayan da nur zata saka ta fara zancen location Abuja sabida familyn su basa hidimar bikin al'ada acikin gidajen su saidai suyi shi awani location na daban.

wani secure location ta zaba musu ta saye building din wajen gabaki daya just for the weding, All the security arrngmnts have been made sharply dan tasan ba wani gayyatar mutane dayawa zasuyi ba is alawys within family and very close allies kuma zai iya yuwa agayyace iyayen nur firdaus dan haka komi datay tana lissafe da su.

ko sau daya bata tuno da simran ba bare hajy xubaida da aka fitar dasu acikin gidan  tundazu dan haryanxu babu wanda yasan ma me suke ciki.

lady sid ne kawai dai abun ya dan dameta sai kaji tana tambayar masu aiki ko simran tana da rai ko ta mutu dan ta mummunn razana da irin abubuwan dataga ya faru dazu musmn ma nitsuwar farat daya dataga anty suad tay takama shiryawa nur da javeed aure

tasan duk yadda akayi bakaramin tozarci da  masifa aka saukar mata akai ba..

ko samun daman yin magana me nisa ba suyi ba anty suad din tadinga saka ta wasu ayyuka yinan yinan anata zancen kayan sawa, abinci, gifts da sauransu.

lady sid taje dakinta yin sallah da wanka bada jimawa anty suad ta gama waya lkcin tana kkrin itama tay wankan ta karasa suje wajen cin abinci

sai ganan mother ta shigo kamar wacce aka jefota cikin dakin fuskrta babu alamar rahma sosai gaban anty suad ya tsinke rawa rawa jikinta ya fara da suka hade ido marmaza ta tsuguna tafara gaisuwa..

mother bata amsa ta ba ta karaso ciki dan dama acike da ita take tam bata so ne tay mata magana marasa dadi agaban yara...

ko zama tsohuwar batay ba tafara tsille ta da nasiha akan abubuwan datake kullawa game da dukiyar gidan sai ta nuna mata kamar spirit din ancesstor dinsu ne suka nuna mata hakan a mafarki

cikin hikimarta da basirarta ta karance mata duk wani boyayyar manufarta tsaf akan nur firdaus

tsorata tay sosai kafin ma ta mata fada akan kalar zubda girmanta datakeyi agidan tareda ja mata kunne akan alakarta da nur firdaus snn tace inhar tanaso su shirya daga toh maza ta sake tunani ta canza hali dan babu wani babba me shekaru a ahali inba ita din ba dole ya zama ta nitsu snn daga anzo cin abinci ta bawa yarinyar hakuri akan zargin zina da batanci da suka mata koda ba agabansu ba amma dai dolene ta bawa yarinyar hakuri haka
komi na shirin bikin nan ita zatay babu me saka mata hannu.

har Mother ta fice anty suad hawaye kawai takeyi dan batay tsammanin har sun gano manufarta sosai har haka ba, sai jikinta ya karayin sanyi sosai dakyar ta rarrashe kanta tay shiru snn ta fada wanka bayan ta gama zanta tunani aranta ta fito ta shirya tasaka riga da zani milk colour da ratsin ja tay lullumi me kyau daya kara fitar da girmanta, kafin duk agama shiri agidan har akawo nur firdaus kasa gaisuwa saida aka yi sallarh asr....

hjya amira saida tay ma nur sabon siracen turaren masu qamshi takara gyara mata nude make up inta ta lullume mata jikinta da alkyaban snn ta rikota ahnkli ahnkli take takawa har suka sauko.

kusan da yamma ne sosai dan haka lokacin babu wanda baya zaune a babban falon gida, yadda kasan za'a je gasar kyau kowa ya dau sabuwar wanka an saka kaya na alfarma

lady sid ta saka bobou gown na purple leshi tana zaune shiru baqin ciki kamar zai hadiyeta dan tasan duk da simran ce aka auro yau da yanzu itace kirjin biki ba hajiya Amira ba....

dake ita neman gindin zama da kwadayi ne aranta sai take gani kamar hjya amirar ma abunda yasaka ta rike nur firdaus hannu biyu kenan dan kowa yasan javeed is the real and only Heir of the mufasa kuma yana da arziki sosai harna fitar hankali bayan duk kudin babansa dana kakansa ma still sunansa ne akan kusan duka, then kamil has the few from the rest daga gadon anty suad.

su biyun sune suke da real generational wealth duk dama babu mahadin javeed da kowa Babu wani abu mafi abun tsoro kamar kaci haqqin mutum bakajin ko dar dar aranka littafin ba kyauta bane kudi ake sawa ake karantawa ga wanda imaninsu yakeda saura chat me and pay via 08060712446
[02/07, 16:17] Ladysu: Babu wani abu mafi muni da abun tsoro kamar kaci haqqin mutum bakajin ko dar dar aranka littafina ba kyauta bane kudi ake sawa ake karantawa ga wanda imaninsu yakeda saura chat me and pay via 08060712446

koda suka doso falon tafiya nur take ahnkli gabanta na faduwa duk da rike mata hannu da hjy amira tay amma bai hana wanda suka kure musu idanu gane dan dingishin datakeyi ba

wani irin tsananin kunya ta dingaji har suka sauko kanta na kallon kasa suna daf da karasawa kasan kenan javeed ya kasa hakuri yamike tsaye bai kula da idanun dake binshi kai tsaye yajeshi snda ya kare ma nur din wata narkakken kallo kafin calmy ya tarbo hannunta ta rike nashi ya karaso da ita ciki yanabi da ita ahankli

sallama me sanyi sukayi aka amsa su lkcin kirjinta bugawa yake da karfi dan she can feel all eyes on them, yadda javeed yake mata princess treatment kamar yar kwai sam taki ta daga kai tsabar yadda ta fara jin ina ma ace kasa ya budu mata tashige ciki.

bata hankara ba taji wai har sun iso gaban mother hauwa.

gabanta ya tsananta bugu dataji alhaj attah ya hau introducing inta wa mother officially yace ma mother ga doter inlaw dinsa
Nur firdaus Haroun

muryanta na rawa rawa har zata rusuna kasa tafara gaisuwa mother tay sauri ta mike tsaye kadan snn ta tallabo kafadunta tana mata murmushi da alaman ta yafe.

cikin sanyin kalami suka gaisa, muryanta da fara'a tahau gwada kyaun siffar nur din da sai dataganta a fili kafin tasan ashe kyauntan yafi yadda suad take fada, nn tambayeta ya jiki cikin sakayawa da fara'a d komi tabata hakuri akan abunda ya farun sama sama wanda tsabar kunya nur bata ma san ya akayi har ta gama amsawa ba.

hannunta na cikin na javeed tagaida alhaj attah wanda taji baice mata komi ba face dora feather staff dinsa da yay akanta da alamar saka mata albarka gabaki daya kama ganinsa kasan kunyarta yakeji aransa

tun basu juyo ba anty suad ta mike ta fice awajen da sauri

har saida nur ta gama gaishe da duk sauran mutanen da ke wajen babu wanda bai amsa ta da sakin fuska ba face lady sid dan bayan baqin cikin dake damunta har da haushin irin yadda dataga tsantsar kyaun nur firdaus din ke dauke ma yan gidan hankli kowa na masha Allah she can swear that kan javeed bakaramin huruwa yake taciki ba.

tarasa wani dan bura uban farinjini yarinyar nan take dashi haka da kowa yake sake mata fuska ana admiring inta har da ido gashi kowa wani kaya nur ta saka komin killacewa da satay saikaga ya mata mugun kyau ga sanyin kasaita da aji kamar yar gidan sarki.

sun gama gaisuwar kenan javeed ya rike hannunta zai kaita wajen zamanta sai ganan anty suad ta dawo,yadda ta shigo da fuskrta wani iri ya saka kowa ya dan kalleta banda nur din datake kkrin zama. ta zaunan kenan ko gama sake mata hannu javeed baiyi ba, anty suad tayo wajensu suna dan hade ido nur ta fara kkrin gaisheta, shiru tay har saida nur ta gama gaishetan snn tafara tambayarta ya jiki ta kuma bata haqurin zarginta da sukayi duk dama anty suad din is alwys egoistic and hot like chilli, tana maganan ne acikin iko da nuna ita babbace but still dai saida ta bawa kowa mamakin yadda ta saka kalaman asaukake har tasaka nur tay murmushi.

dan wann abun data daure tayin kuwa saitaga ya kara mata mutunci a idon kowa

mother tay karamin nasiha na zaman lafya da rike amana daga nan akaje akaci abinci
babu yabo babu fallasa ana ci ana hira kadan kadan lady sid ce kawai a dame awajen dan tuni anty suad ta saje tana kama ajinta ana hira da ita saitay kamr ba itace dazu da safe ta zubar da girmanta agabn kowa ba..

ana gama cin abincin
Anty suad ce ta fara tashi ta haura sama tanakan amsa wayar masu decoration da masu kera kayan amarya dan bata son ayi nur din anything too much nd shouty kamar na simran shiyasa ta zabi haute
culture simple and elegant saidai za'a zuba stone na white diamonds ajiki daga an gama biki zai zama kamar historical dress da zasu iya ajewa a dress museum dinsu

hajiya amira ta maida nur sashensu tarade mother ana mata wasu gyaran jikin nan aka bar maxajen duk a kasa.

lady sid ce kawai ta sace jiki takai ma hajy xubaida abincin tare da basu labarin duk abinda ake ciki wanda ita bama jinta takey ba

babban burinta baifi a sake kawunanta snn ta samu damar zuwa gida ta duba babansu ba
dan tasan duk yadda akayi yaji labarin kalar barnan da simran tamasa na kudi toh babu shakka zcyarsa zai buga dan yanada mummunan ciwon zuciya.

hakanan lady sid ta gama gulmanta dawo gidan bata gane kan hajiy zubaida ba gashi haryanxu simran bata saka lahadin farkawa daga karamin mutuwar da tayin ba.

fannin nur kuwa babu kalar gatar da bata gani ba, ga mother tana yawan janta da nasiha da kuma tarihi na mahaifyar javeed da abubuwan datakeyi na taimakon addini da marayu. sosai nur tasha mamaki dan aranta yadda taji an fadin mother daukawa tay zatama fi anty suad zafi amma kuma sai taga she is just another version na hajy mammy abunda ya bambamta su shine hajy mammy musuluncin kawai ta riqe, mother kuma ta fi riqe al'ada sosai.
Chapter 160 · 0% Book details