← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 174 OF 206

Sashe 174

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

motocinsu na alfarma mercedez benz sunkai goma sha biyar suka hallara dasu wajen biki

suna sauka a motocin aka mika nur a hannun lady sid da hajya zubaida akan sukaita inda su hajiya mammy suke domin tay gaisuwa snn afara gabatar da wasu formaliies na al'ada dan zuwa 2pm za'a fara hidima kuma za'a kareshi ne before 5:30pm sabida yau da dare zasu wuce morocco for the main mufasa initation culture.

matar sultan mimie ce ta rike ma nur jelar kayanta har suka shigo sashen suka rusuna kasa suka gaida hajy mammy

snn suka shiga can ciki suka damkata a hannun su hjya sa'adatu Kirjin nur lokcin kamar xai balle da murna data ga kanta agaban su hjy sa'adatu

wanda suka damkatan suna ficewa nur ta yaye mayafin da tsalle ta rungumesu duk suka taru suna kuka kagansu zaka dauka shekara hamsin sukayi basuga junansu ba

babu kalar tambaya da tarairaya da basu mata ba ganin zumudin murnan nasu baxai kare ba ya saka suka nitsu suka kara gyara mata jiki suka rufeta fess hajy bilqi dama da shirinta na turare tazo

haka ta kunna turare na alfarma tabi jikin nur din snn suka fito da nur suka damkata hannun hjya mammy kamar yadda aka musu bayani angama mika nur kenan sai gasu layla da jadida sun shigo

duk layla tabi ta rude sai kalle kalle takeyi kamar batacciya

sun shigo dede hajy mammyn tana yi ma nur adduoi kenan su hjy sa'a sun kewayeta suna amsawa da ameen

hakan yasaka su layla basu samu damar zuwa kusa da nur ba gashi bawai sanin fuskokin matayen kawuntan tay ba,tazo da jiji da ka da giggiwa amma koda taxo taga yanayin kowa sai atake taji ta dawo insecure ganin kamar kowa yay wanka ne daya kere mata tunani danko bikin gaggan yan siyasa da suke xuwa bata taba ganin irin wann shigar ba.

time nayi hajy mammy takara rufe fuskar nur da veil snn ta jawo hannunta suna tafiya ahankli iyayen nabin su abaya za'aje hall din hidima jadida tabisu abaya

layla ta kasa motsi ta zuba ma nur firdaus idanu kamar bata taba ganinta ba dan azahirin gaskiya ankere fuskanta ne da wani irin nude spiking make up daya gama daukar kalar fatar ta ya fallasa sirrin kyaun ta fiye da na kullum.

Flowing hauticultural gold and caramel hand stiched wedding dresss din ta daya zube kasa yana binta An tattare sumanta an karkare shi da diamond Corchet pin, trnsprnt long and flowing head wrap din ta dogo ne kuma sharara sosai yana sharar kasa.

Ga wani tsadadden rock stud pump akafar ta dayaji jan lalle wanda da ace za'ayi auction dinsa ba karamin kudi za'a kwasa ba.

haute weding attires ba na kananan masu kudi bane dan shikansa ma wani asset ne.

layla dake tsaye kamar burar giwa ji tayi kamar wuta na bin gangan jikinta da wuyarta dan wani zafi kirjin ta ya shigayi kamar ana tsikarar ta da wuta. ganin ta tsaya adaskare kamar kungi yasaka jadida ta dawo ta fixgo hannunta sukabi bayansu hajy mammyn

laylah Bata tashi sumewa da kishi ba sanda aka shigo dasu babban hall din da za'ayi hidimar dan wani dogon rail ne me zig zig shape an cikeshi da snow white flowers da pure blood red roses here and der

dake asaka ma nur professional shapers ya kara fidda shape din ta uwa zana ta akayi da hannu.

Wani salon kyau da haduwan da tayi sosai ya girgiza ma kowa kwalwawa

layla Bata san ta ina nishi mai zafi yake kufce mata ba duhu gabaki daya yana neman ya rufe mata ido.

ahalin mufasa da bakinsu sune akasa cikin hall din all dressed in the most expensive and luxurious wears kowa ya juya yana kallon shigowar nur...

all the other mufasa brothers are wearing dark grey kowa da kalar nashi adon sai na sultan light bai shiga kalar nasu ba da few quest da sukaxo musu code din bikin is eida gold, army green or black.

javeed yana tsaye wajen babansa da wasu amintattun abokan baban nasa da suka sakoshi a tsakiya kayansa is lure black made frm all this persian theme haute knee drop royal court, typical dress na olden days persians simply very dramatic, elegant and regal wanda kagansa zaka dauka angon wani arab kingdom ne his face is glowin and shining yana ji kamar yaune xaiy aure

yan uwa da abokan arxiki babu wanda baixo da xumudi da kuma shirin bikin ba.

wasu suna tsaka da hira aka sanar da fitowar amarya duk na xaune anata karkata kai ana dan leko breath taking flowery and slow bridal enterance na tawagar amarya..

A karon farko da wajen ya dauki shiru na musamman kenan anty suad dama ta gayyato wata shaharriyar mawakiya daga can middle east wacce tayi tsaye akan red capert har saida aka fara sauko da amarya snn ta bayyana da mic a hannunta Kerarriyar Muryanta daya ratsa ma kowa tsikar jiki tana sharo wani wakar soyayya da harshen larabci musmn da aka fara saukowa kasa da amarya izuwa fili..

hajiya mammy ne agaba tana janta ahnkli iyeyenta kuma na gefen ta jadida na tayata rike jelar gown din..

matar sai wani irin kirarin soyayyah take cikin sautin waka mai tafiyar da yanayi

...,kowa sanda yaji ya mike yayi tubarkallh dan kuwa kayan da nur tasaka da irin kwalliyar da akayi matan ba karamin abun kallo bane..

anty suad tafara jin kamar kanta zai fashe musmn dataga bakin su sun shagala suna yaba kayan amarya wanda ita ta shiryashi.

kafafun Layla sai harhadewa yake abayan jadida tana jin jiri jiri kamar zata fadi kasa daga sun hada ido jadida zata watsa mata muguwar harara tsanan me tattare da murmushin mugunta

ana sauko da nur kasa gaban su mother za'a mika musu ita wato mawakiya tayi wani zazzafar stanza awakar da sunan Nur firdaus tana maimetabcewa auren soyayya da babu mai rabawa tana yi tana cewa aure yana da dadi ne in mutum ya so mai sonsa...

laylah da bawani sosai take iya tuna larabci ba amma taji wannan stanzan kuma jitayi kamar da ita kawai akeyi

haka kawai tabi ta hade rai idonta ya ciko da hawaye saidai ba wanda ma ya ke kallon ta bcos she look local ko jadida ma tafi tahawa kaya me tsada ..

cikin girmamawa da gaisuwan ban girma hajy mamy da su hjy sa'a suka mika nur wa mother hauwa ayayinda duka matayen dake wajen suka gewayesu

wani irin muguwar guda me kara wata mata acikin quest dinsu takeyi daya mugun girgiza zuciyar mahassada kamr layla da kuma hajy xubaida subiyu ne awajen gabaki daya kamar basa cikin hayyacinsu.

alhaj abbkar zai murmushi yake yana hawaye aransa yana jin inama mahaifin nur din yana raye yaga yarsa dan duk wani karammawr uba mashi kawai ake bayarwa.

har saida aka mika nur wa ahalin mufasa sann iyaye maza suka taho da ango dayake jin kamar baxai iya jira ba suna isowa yataro matarsa dakan shi in a very special way.

Dawani irin salon nuna kauna mecike da karramawa yanemi izinin karasawa da ita wajen zamanta Kowa awajen yasha mamakin yadda duk girma da kama ajinsan ya ke rawan jiki akan matarsa.

layla tunda taga javeed ta kuma tabbata wai shine mijin nur din hawayen datake dannewa zirrrr yafara bin kuncinta she look lost and alone gashi ko kulata matayen kawuntan basuyi ba sabida ko a fuska ma basu santa ba ita ma bawai saninsu tay a fuska ba.

ahnkli javeed ya xaunar da nur akan farin kujerar su na pure crown anty suad da hajya amira suka xo da wani katon hand woven morocon red and golden royal carpet madaidaici aka shimfida agaban nur firdaus.

daga nan mother ta dauko leg anklet din da ake sawa na bridal acceptance azuriar sun ta bawa javeed ya tsuguna kasa ya dora kafarta akan cinyarsa snn ya daura mata anklet din a ankle din ta.

bayan nan daga jadidah sai mimie kawai aka bari suka xauna agefenta javeed ya tsaya tare da sultan da sauran brothers dinsa

sai asann alhj abbkar ya lura da layla dake tsaye ita daya yay ido ma hjy sa'a akan taje ta kirata suna xuwa yace musu ai layla kenan, sunata mamaki, ita kuwa laylan tsabar ba acikin hayyacinta take ba sama sama tamusu gaisuwa hjy bilqi kam taki sam ta saki jiki da ita hjy saadatun ne dai babu yadda ta iya suka ajeta agefensu.

ana samun zama aka dan zantar da jawabi game da al'adar mother da hajy mmy sit dinsu iri daya ne amma ita hajy mammy a wajen dangin amarya ta xauna sai matayen familyn mufasa agefen mother hauwa.

lokacin Kishi kamar xai kashe hajy zubaida ganin kamr nur ta ta maye gurbin ta a xuciyar surkuwanta wato hajy mammy

lady sid kam shiru tay kamar bata wajen dan tasan abunda zai faru anan bazai mata dadi ba. nur will be super wealthy today and dats just a great heartache mata babu karya.

tasan mufasas sunayin wnn al'adan ne kawai dan su bawa newly weded bride dinsu kayan duniya iya kayan duniya ta inda arxikin zai isheta taji koda maqiyinsu yanu na mata awani kudi awaje bazata saida sirrikan ahalinta ba, komi da suke zantarwa a ahalinsu yana da boyayyar manufa da ma'ana

lokaci yayi na bude fuskan amarya za ayi al'adan nasu da initially wa yarinya budurwa akey dan its believe dat sai anyi wann bikin kafin ango zai yi saduwar aure da amaryansa toh tun a farko hajy mammy ne tace musu hakan bazaiyu ba, anty suad kuma sunyi zaton nur din ma bazata kai wnn matsayin a gidan mufasa ba sai gashi komi ya canxa salo

Duka Sun sha mamaki da javeed ya bita da kiss agefe da gefen kuncin ta batare da yaji nauyin kowa ba

dan hakan yana da meaning a al'adan su nufin matar sa is no longer a virgin shida ita sunriga sun dawo daya wanda hakan ya fara bude fili ma abunda ya tara su.
Chapter 174 · 0% Book details