← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 206

Sashe 123

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wajajen 3:30pm yay wanka kenan zai shiga sallahn asr sultan ya kirasa yace mai yana hanyar zuwa gidan nan da minti 20 haka zai iso ce mai yay ya samesa a masjid kawai snn ya shirya ya fita.

daga sashen da javeed yake kuwa ana shiga sallahn asr suka watse a dakin nur taji wani irin sanyi aranta dan dama sun isheta a dakin

marmaza taje tay alwala tazo ta hada ruwan maganin akan intay sallahn asr kawai wankeshi zatay tay sauka sabida kar su anty suad su sake dawowa.

tana hadawa tace ma janet tana duba mata ruwan nan ajeshi akan table ta fara sallahn har tay sujada na biyu kenan taji janet ta saka ihu tana cewa blood of jesuss blood of jesus

mummunn faduwa gaban nur yay amma haka ta daure ta cigaba da sallahn ganin likitan ya shigo da gudu shima jin ihun janet yajawo hanklin kowa har da su mr aqeel dake waje.

nur tana sallahn amma jikinta rawa yake jin yadda janet ta hau nuna musu yadda kwaryan ya cika da ruwan kumfa har yana zubowa kasa tsoro duk ya cikke idanunsu

mr aqeel ne yay ta maza yaje ya dauke kwaryan dan yaga da alaman ruwan zai iya zuba akan gadon da javeed yake kwance da gudu janet taje takira su anty suad kafin kace wani abu dakin yacika kowa yana kallon ikon Allah

nur tana yin sallama agurguje ta taho tawajen to make sure javeed is okay snn ta amshi kwaryan a hannun mr aqeel taje sink ta tsiyaye shi ta wanke kwaryan tazo ta kifasa da bisimillla duk panics da surutunsu anty batace musu komi ba tafita da taurin zuciy taje ta sake debar magaryan guda bakwai ta sake nikawa tazo da shi

tana shigowa ta samu alhj attah da sultan sun shigo shiya musu bayanin cewa ai wukar da aka cakka ma javeed blood oath ne da baqaqen aljanu har sai an rabashi da su kafin asamu sauki

nan yace musu akan azauna duka afara karatun qur'ani adakin kafin nan nur ta sake hada ruwan....
[01/06, 20:31] BLUE💙: BONUS.
nan kuwa anty suad ta jerasu akan dadduma harda likita da su mr aqeel kowa aka zauna aka debo qur'anai aka raba qur'ani za 'a fara karanta suratul yaseen hmmmm zokaga idonsu simran da hajya zubby duk yay tsuru tsuru dan saida janet ta kawo ma simran scarf ta rufe jikinta dashi snn aka bata qur'ani ta zauna kusa da hajy zubby amma badon rai yaso ba.

akan daddumar dakin akay zama aka fara rero karatun hajy zuby ta sadda kai kasa kamar zata kife fuskarta cikin qur'anin dan tasan ko cin bakin bazata iya ba iyaka sabbi karatun ta ya tsaya...simran kuwa sai bis bis bis bis min min lun lunn take da baki in akazo karashen aya taji tadan capke wani abu sai kaji tayishi da karfin tsiya da wani irin kalkalar karya wai dan ace tanada qira'a irinna nur ana gabar tana yamma duk takaici yabi cikawa anty suad ciki kamar tamata ihu ta koreta haka ta dingaji.

janet na tsaye agafen nur harta gama hada ruwan magannin alhaj alhaj da sultan suka taso suka dan tsaya agefenta yana kallo tay bismillah ta fara tsoma clean towel a ruwan magaryan tana shafawa ajikin javeed

ta shafamai sau uku zata tsoma na hudun kenan tana dagowa taga towel din yana janta tsabar yauqi ita kanta bata san sanda ta jefar akasa ba

ihun blood of jesuss da janet tay yasaka kowa ya razana ya mike tsaye sultan ne ya fara ganin jinin javeed da ya barke yahau tsikalowa daga bayansa kamar ruwa yana tsilalawo kasa gashi yay baqi kirin kamar an damashi da kwalta

mummunan faduwa gaban nur yay da wani irin karfin hali hanmunta na rawa rawa ta bawa mr aqeel ruwan dake kwaryan tacemai ya zuba acikin sink ya dawo mata dashi zata sake hada wani

yana shiga bayin kuwa kofar ya rufu dashi anyi anyi abude sai shiru alhaj atttah dayagene ba normal bane sai yacemai karya dena addua kawai

nur tay sauri ta dora hannunta akan goshin javeed tafara masa asalin ruqiyya jininsa dake zuba sai wani irin zanen abin tsoro yake a dakin akasa

atake waje ya kara rikicewa da tsoro simran data wani capko jikin hajiya zubby nan jikinta yafara rawa kar kar tana neman ta falla da gudu

hankli tashe anty suad ta daka ihu tace musu bamai fita kowa kawai ya zauna adawo kan karatu they cant back down now

jikinsu na wani irin rawa aka zazzauna bakin simran har cijewa yake tsabar tsoro dan firgita takeyi intaji muryan mr aqeel daya makale abayann gida yanata addua shidaya

Nur tana zafafa karatun jikin javeed yay wani irin zafi kafin ka hankara glasses din frame sun fara faffashewa fass fasss fassss fasss straight wani ya cakka sultan a hannu kowa ya fara yin kasa dakansa simran ce tafara wafcewa zata gudu ana kkrin rikota ta rikota akan anty suad ta turmusheta kasa nan waje ya kacame anty suad dataji wani mugun haushi wani irin tureta akasa tay tacigaba da karatun ta ita da lady sid

nan kowa ya fara neman kaucewa dan duk glass dake dakin fashewa suke kamar ana tarwatsu da bindiga kuma duk wanda suka sameshi cakkensa suke.

hannun nur da gefen wuyarta duk glass din ya cakketa amma bata dena ruqiyyar ba dan ita kanta bata san daga ina karfin halin yake zuwa mata ba.

alhaj attah ne kawai a tsaye yana rike da gadon da karfi ganin yadda yake kaduwa can yafara ihun cewa a rufe babban madubi

sultan marmaza ya cire jacket din rigarsa zaije ya rufe kenan sukaga wani sudden guguwar iska ya fettosa kasa da wani irin karfi yabugu da jikin gado duk karfin san nan saida yakasa mikewa tsaye.

wani irin ihu hjya zubaida da simran sukayi suka tashi tsaye simran ta riiike rigar lady sid tana wani irin tsorataccen tsalle kamar zata dauke nunfashinta

alhaj attah ya sake gadon yayi kan sultan da gudu zai dagasa amma yaji yakasa da wani irin karfi windon ya budu sai iska frm no where ya fara shiga dakin wanda atake komi yafara kadawa banda alhaj attah dake addua akan sultan da anty suad likita da lady sid, hajy zubby da simran da janet kam babu kanta dan banda razana da ihu babu abunda su sukeyi.

iskan sosai yaso yarike ma nur hannu dan ji take kamarma ana kkrin finciketa ne daga jikin javeed din amma hakan ta cije da iya karfinta takara danna hannunta a kanshi tana kan rero karatun ta wanda takeyinshi da rawan murya da dunbin tsoro babu kakkautawa after like 2 scdns taji kamar iskan yabar jikinta da wani irin speed ya koma kan windown

bata san inda hanklinta yay ba kawai muryan Alhaj attah taji yana ce mata karta juyo ta kalli madubin aikuwa dan firgitan datayn nan taji an shakure mata wuya kamar za'a kasheta

nan kowa ya mike a mugun tsorace simran tafara fitsari ajikinta zirrrrr ganin iskan dake fita a madubin ne fa boro boro yake jaaann wuyar nur da wani irin karfi duk wanda yazo kusa dan ya ceceta hakan iskan zai fettashi waje..

tun da aka fetta anty suad har kofa tabuga kwankwasonta bata sake iya tashi ba likita ne yaje ya dauketa ya fita da ita kofa a mugun tsorace lady sidd da hajy xubby data jawo simran dake bari kamar mazari fitsari na bin jikinta tana tafiya kamar antsoma kaza aranda tay waje itama...

suna fita kofar ya rufu kiriff shima anyi anyi yaki buduwa karshe ata jikin windon wajen suka taru suka tsaya suna leken abubuwan al ajabi da ke faruwa aciki...

banda alhaj attah da sultan daya mike da kyar suketa kkrin su kwaco wuyar nur da aka shake babu kowa sai janet data saka karfinta duka ta rike gadon javeed dake shaking kamar ana kadashi da karfin gaske

mazan suna krin jan nur anma ji suke kamar they are competing againts the army of 1000 na zaratan maza wanda suka shakureta atare

basuda wata mafita suna ta addua itama nur din da aka riga aka shakure adduar kawai takey tana fitarwa daga bakinta da kyar kafin can ayatul qursiyyu ya ceceta dan sai da sukajata tun daga gado har kasa da wuya snn suka saketa da kyar

janet tun da ta rike gadon a kangare awajen bata ko motsi dan asalin sumewar tsaye tay dan tsoro bata taba ganin wnn bala'in ba

aljanun sun sake ma nur wuya kenan ta fado kasa a rakwabe tafara wani irin tarin jini alhaj da sultan ne sukazo da gudu zasu dagata akasa sai sukaji rigib akasa janet ta fadi kasa kamar an tureta

kamar an tsakura nur ta mike tsaye ta kalli mirror sai taga wani irin fuska me mugun abun tsoro da igiyar canular da aka sakama javeed a hannun dodon yana mata dariya kusan ihu tay tajuya kan javeed din tana isa tahaura kan gadon sai taga igiyar canular kuma awuyansa an shakuresa da shi sosai

wani irin tsorataccen kuka take duk batasan ina karfin hali ke zuwa mata ba, a gurguje ta saka hannunta tafara kokawa da canular tana karanta ayatul qursiyyu da karfi muryanta na rawa cikin kuka she is nearly traumatized dan ita daya take gani sauran nasa gani

amma dataga su sultan da alhaj sun tsaya agefenta suna tayata karatowa sai taji ta samu kwarin gwiwa saida tay ayatul qur'siyun kamar guda bakwai snn taji ta capko canular da karfin tsiya ta cireshi a wuyar javeed taga wai harya masa shati da sauri ta jefar akasa ahankli ta rungumeshi tana tsorataccen kuka..

nan sultan yay saurin kunna radion karatun qur'ani wajen yay wani irin shiru iskar sai ya bace baaat nan kofar bayi yafara buduwa mr aqeel ya fito agaggauce da kwaryan a hannunsa kafin nan windown daya budun yakullu dakansa, kofar waje ma ya bude su anty suad suka shigo kowa cikinsu ya firgita yana salati mr aqeel ya daga janet akasa ta mike tanata addua simran da hajy zubby sam sukaki shigowa suka tsaye a kofa jikinsu na rawa rawa...
Chapter 123 · 0% Book details