← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 206

Sashe 59

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

jikinta a sanyaye zatay magana sai ta fashe da kuka wanda bakomi yasata kukan ba face sai yadda take tuna yadda mrs hasina take mata mugayen baki...wani abu na rauni taji ya rike mata wuya sai taji koma dai mugun bakin hasina ke binta shiyasa komi na rayuwarta yake xuwa mata baibai??

ganin nur ta kasa cewa komi tana kuka hajy saa ta amshi wayar tay sallama wa mrs haseena data gama shakar kukan nur ta amsata ciki ciki tay kamar ma bata san numbar waye bane tafara tambayr su cikin gatse da rainin hankli.

nan hajy saa ta mata bayanin kanta batace komi ba sai cewa tay ohhh to me yafaru?

...nan tahau gaya mata abunda ake ciki na cewa yarta nur zatay aure sai ta dan saka wayar a handsfree inda nur din zatanajinta

wani uban shewa hasina ta buga ta inda take shiga batanan take fita ba tanuna ita bata masan da wata wai nur firdaus ba..

acewrta inma wani taimako suke nema awajenta ita bazata iya taimakawa ba aitunda sun karbeta kawai sukarata tacen..

nan hjy bilqi ta karbe wayar da bacin rai tace mata sunfi karfin sunemei wani abu wajenta kawai de hankli ne sukafita shiyasa sukaga ya dace su sanar da ita auran yarta nan ma sukayi kamar zasuyi cece kuce...

dede nan layla ta karbi maganan ko gaishe su batay ba tafara wasu irin kininibibi tana tambayar nur wai wayene zai aureta ahaka duk dama yaji tay cikin shege?

nur bata ko amsata ba
tay shiru, mrs hasina duk ta dauka taimko ake nema ko ana su suzo bikin ne hakanan tadinga gaya musu maganan banza harda cewa ita dama ta cire hannunta tuntini akan nur koma uban waye zasu aurar da ita su aurar baidameta ba

inda da sabo nur ta riga ta saba da irin wayannan rashin mutuncin na su, su hjya saa da hajy bilqi ne kawai abun yay musu zafi bana wasa ba.

nur kuwa ko ajikinta jin wai har laylah ce ta samu bakin mata gori akan cikin shege suna tunanin duk wanda zai aureta maneji kawai zai aura ba kuma lallaine nur ta samu me kudi ko me matsayi kamar adnan ta aura musmn yanxu da bata wani daraja ba. they make sure to let her knw dat suna kano wajen hidimarsu snn layla ta samu matsayi kawai zuwa aurentan ne bazasuyi ba.

bayan sun katse wayar nur ta shiga bayi tay alwala ta fito tay addua aranta daga nan bata sake yin wani kuka ba, har su hjy suka kaita dakin shirya amarya aka hau gyarata tsaf dama retouching kawai zaayi dan haka ba awani dau lkci ba dake professionals ne.

kusan mutane biyar ne akanta waynn tay nan wann tay nan

within good 10 min an gama kimtsata tsaf aka tayata saka pure white bridal dresses dinta dayay mata wani irin kyau dama kuma komi size dinta ne

hajy sa'a ta share hawayenta tay ma nur adduoin snn ta rufa mata doguwar veil dinta sharara akai wanda ya sauko har kasa yana sharar kasa

wani irin sassanyar kyau tay kowa na tubarkallh kalamai masu dadi tareda saka albarka ake showering inta dasu while aranta ta riga fa sadaqar da komi tanai ma kanta kallon replacement bride..

she is just doing this to save her one and only family da suka taba treating inta ryt a duk dunian nan..

bayan sun mata nasiha anan aka barta su hajy suka kimtsa suma snn suka koma wajen baqinsu mata

ata falon kuwa lokacin already anfara batun daura auren komi da akeyi na al'ada da kuma laduban aure a musulunce anyi shi a tsanake.

koda aka tabbatar da lafyar amarya da ango shikenan dan dama ahalin mufasa basa fiyeson bidi'a ba snn sabida secret image insu yasa basu fiye damuwa da wani shirmen publicity ba amma duk aure in zasuyi sukan bada sadakin mace da matukar tsada..

ayau sun bada almost $53. sumting millionUS dollars a matsayin sadakin Nur firdaus tareda jakar danyen gwal mai dauke da raw gold blocks guda goma aciki...

anan aka daura auren snn aka bayyana sunan amarya da ango,

Nur firdaus haroun ciroma
da angonta javeed A mufasa.

javeed yana xaune ne kawai amma shikadai yasan irin farincikin daya shiga ciki dan Allah Allah yake a fito da ita a damka musu su tafi.

aka shigo da wasu bakaken bags guda uku dauke da 20 billion din aka bawa alhaj abbakar aciki lkcn shi duk wann be darasa ba kawai yanayin da suka ma nur auren ne agagauce ya mugun dagamai hankli.

shide kawai dauriya irint maza yakeyi, dakansa yaje ya fito da nur firdaus bayan ya gama mata nasiha sosai sunkara fahmtr juna.

duk matayen da ke aciki suka firfito falon akazo anata sambarkan succesful weding..

can saiga alhaj ya riko hannun nur daga stairs suna saukowa ahnkl tule din dress da kuma shararan veil dinta na wani irin jan kasa.

javeed ya dingajin kamar ya tashi da gudu yaje ya tarbo abarsa sultan ne yadinga taka mai kafa dan yanitsu amma inaa minti daya minti daya sai kaga ya gyara zama murmushin dayake dannewar sosai tafito a fili yakasa dauke idonsa akanta...

wani irin girma kansa ya kara yi dayaga yadda kowa yake furta tubarkalla masha Allah dan tun nur bata dago kanta ba for a moment su lady saddiqa sun dauka pure indian breed suka aura..

ryt frm the looks zaka san dukansu harda mazajen basuyi tsammanin cewa haduwa da kyaun yarinyar yakai har haka ba.

wani irin guda akeyi dan tun kan su iso cikin falon javeed ya kasa kama kansa yamike tsaye har sanda aka mika masa hannunta anashi bai iya dauke idonsa akanta ba yay hamdala.

gaban dad dinsa ya fara kaita aka saka musu albarka aka musu addua yakaita wajen eldest brothrs suma sukayi turbakllah da ita.

kafin nan ya mikata wa hajya mammy muryansa na fita ahankli yace hajya this is ur surprise..

tana murmushi ta amshe hannunta nur ta tsunkayar dakai can kasa aka fara zancen siyen bakin amarya nd all those stuffs na al'ada.

atake hajiya mammy ta bada 100million in cheque dan kawai ta matsu taga fuskar amaryan sauran matan ma duk suna Allah Allah kowa ya zuba mata idanu..

ana mikawa su hajy bilqi chque aka fara guda...

hjya mammy tay addua snn ta bude fuskar nur ahnkli

suna hade ido tace "fiddausi!? tun kan nur tay motsi tay wani irin kabbara tarungumeta
murna da farin cikin da aka mugun jima ba agani akan fuskarta ba shi ya bayyana akan fuskarta dan atake ji tay kamar gurbin mahaifyr javeed aka sake cike matashi ayau din.
[08/05, 20:03] BLUE💙: EPISODE 36🦋
Arewabooks@surayyahms
nur kuwa banda hawaye masu sanyi me hade da bugun zuciya da kuma tsananin faduwar gaba babu abunda take fama dashi...

a duk dama ta sadaqar da komi ta rufe zucyarta daga wani tunani me kawo karayar xuciya da rauni saidai duk dahaka bakaramin tsoron hukuncin data yanke ma rayuwarta ayau din takeji ajikin ba.

saidai ganin wann tsohuwar ma kawai ya rage mata wani abu atleast zata samu wacce raayinsu ya zo daya wajen harkokin addini maybe iya abunda zaibada ma'ana auren nan kenan.

hajy mammy tasha mamaki snn tay farinciki matuka dataga wai nur firdaus ce wanda iya shaidar ta bayar akan nur awajen kawai saida ya jawo kusan kowa ya soma mata wani irin kallon mutunci da darajawa na musmn.

hajy amira mufasa sai masha Allah takeyi tana turbarkallah da nur firdaus sabida komi na yarinyar ya gama burgeta yakaita cloud nine tunda kan physical appearance to her unwavering beautifl reputations tay checking inta out da kyau takuma tabbata cewa takai kuma tacika ta shigo cikin ahalin su.

lady saddika kuwa mamakine yagama rufeta dan rabonsu da
suga tsohuwar nan tana farinciki haka da wani hidima na ahalin mufasa kai tun bayan rasuwar mahaifyar javeed data yanke alaka da kowa.

ryt frm now tasan cewa nur zata zame musu wata kashin kifi awuyarsu tunda har uwar masu gida tana kaunarta, tasani sarai tunda hajya mammy ta nuna tana yin nur a fili toh babu shakka nur firdaus zata samu automatic wajen zama tareda wani babban gurbi a zuciyar mahaifin javeed mufasa...

Allah Allah take suje gida ta baza kanun labarai wa anty suad dan dama saida sukayi harsashen cewa hala bazasu kaunace yarinyar ba

toh ashe ma ga babban dalili yaxo musu da alama wata sabuwar me hali irinna mahaifyar javeed din za'a sake kawo musu cikin ahalinsu.

nur tunda take a duniya bata taba samun karbuwa tare da yabo nakai tsaye kamar nayau ba..

and its all thanks to hajy mammy dan bata san da cewa hajy mamyn ta sakata aranta haka sosai ba

wanda wnn yanayin ne yasaka hanklin su hjy saa da hajy bilqi ya dada kwanciya koba komi ynxu dai sunga haske tunda alamu sun nuna cewa nur ta samu karbuwa sosai

kudin gaisuwar uwa da uba da na siyen baki da duk wani abu da akeyi aka tarkata aka damka musu..

haka suma suka bada tukuicinsu na bugun girma.

sadaqin nur da blocks din gwal duk alhaj abbakar bai bari an taba mata ba yace duka nata ne dan haka da kayanta duka aka hada wanda zaa wuce mata lagos dasu.

anan falon aka ma amarya da ango nasiha masu shiga jiki..
kusan kowani nishi ta sauke zaka iya rantsewa javeed yana jinsa har cikin kokon ransa dan wani irin matsanancin halin farin ciki yake ciki ayanzu.

koda suka tashi tafiya nur taga soyayyar datasan har ta mutu bazata samesa kwatan kwacin irinsa awajen mrs hasina ba wajensu hajya bilki da hjy saa,

dan kuwa babu wani gata da kalamai masu dadi da uwa take gayawa yarta aranar auranta wanda basu rarrasheta dashi ba.

rabuwarsu was very emotional da kawunta sabida har ga Allah aransa yaso yabata wani rayuwar na daban saidai baiyi tsammanin haka Allah zai juya lamarinsu ba duk dama nur ta nuna masa cewa ya isa da ita kuma ta daukesa uba abunda yakejin har ya mutu bazai mance da shi ba.
Chapter 59 · 0% Book details