← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 206

Sashe 144

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

suna isa kofar dakin sa tun bai bude ba ya juyo ya kalleta jikinsa har na rawa rawa...

muryansa kasa kasa da tsananin tashin hankli da bacin rai ya kalleta yace "is it true?

tun kafin ta amsa yaji ya kasa daurewa cikin daka mata wani irin borataccen tsawar daya kusa sumar da ita tay baya kamar zata fadi ya fizgota yace answr the damn question is it true?wani abu me kama da haka yafaru dake nd i dint know?...

numfashinta kamar zai bar jikinta take kuka sabida ta tsorata

jikinta na rawa tabi ta runtse idon sabida kallon dayake mata sai batace mai komi ba ta gyada masa kai cikin kuka sosai, wani cak taji ya dauke baya motsi dan sai da yay kamar 3 minutes kafin nan taji ya saketa tun kafin tadago ta masa wani bayani yabude dakinsa da mugun sauri ya shiga ya barta anan atsaye bata hankara ba saijin karar buguwar kofar wanda saida ta kara razana ta kankame jikinta sosai tana kuka

ta tsaya cak awajen tanata buga kofar tana kiran sunan sa
amma bai kulata ba

dan yana shiga ya kwanta akan gadonsa ruf da ciki shikansa bai san lkcin da zazzfr hawaye ya fara sauka masa ba, how did he not even knw this??? koda shike shine nan ya hana kansa yin bincike akan yanayin rayuwarta na baya sosai dan aganinsa zai iya fahintar nur tunda ya aureta batare da sai ya zafafa wasu bincike past akan files dinta.

baisan yana mata wani irin muguwar so ba sai yanxu dayaji kusan kominsa na neman tsayawa cak sabida ita dan wani irin matsanancin zafin kishi yaji ya rufesa.

babu kalar rokon da batay masa akan ya saurareta ba amma sai shiru..

karshe kasa motsi tay tanemi waje ta zauna bakin kofar akasa tanata kuka har saida hawayen ta ya gaji dankansa ya dena zuba ga dan uban zazzabi dataji ya rufeta atake.

washe gari da asubah kawai tsintar kanta tay akan gadonta an saka mata drip she dont knw why and who tadai ga na'ima da janet suna tsaye akanta
[11/06, 16:28] BLUE💙: Arewabooks@surayyahms

tana gama bude ido ko tsayawa sanin awani duniya take batay ba takama igiyan drip din ta tsinke ta sauka akan gadon batama jin me suke cewa takoma kofar dakinsa ta dinga bugawa tana kirar sunansa tana kuka yana jinta daga kan sallayar daya zauna akai amma bai ko motsa ba sabida rabonsa dayay hawaye akan wata ya mace tun mutuwar mahaifyarsa..

yana masifar sonta snn yanada tsananin kishi amma babban damuwarsa ba labarin tay cikin bane shide yadda komi daya farun zai iya jawo mutuwar aurensu ne yake damunsa dan koda maza dubune suka rabe nur bayajin hakan zai iya goge masa son dayake mata aransa

tunaninta ya kwana yi ya kuma kikira duka lambar wayar sultan amma dukkansu suna akashe, yau din ko runtsawa baiyi ba bare ya samu sukuni aransa,.

it took him a great deal of emotional outbust kafin nan ya samu dan karamin nitsuwa duk ya kasa fitowa waje da umbin fargaban haduwar sa da mahaifinsa acikin masjid dan yasan by now duk jiran maganan bakinsa kawai sukeyi akan nur kafin nan ayanke musu hukuncin raba aurensu, tunda dai kakkarfan doka ce a ahalin su kan cewa basu taba auren macen da wani da namijin daban ya fara saninta tun awaje gashi shikuma ji yake kamar bazai taba iya rabuwa da nur firdaus ba.

yanaji nur tanata kuka tana ambatar sunansa daga kofar dakin san abun na konashi mishi rai amma baijin zai iya sake kallon idanunta sabida tsananin kishi da mahaukacin son dayake mata aransa

anan bakin kofarsan nur ta sulale kasa ta zauna atakure tana kuka na tsawon lkci har saida numfashinta ya dena fita, few more minutes taji bata san inda kanta yake ba kawai tingling pains na yadda ake soka mata alluran bacci taji daga nan sai bata sake sanin inda take ba.

cikin tsananin damuwa na'ima data tay taurin kai taje ta daukota daga kofar dakin tazauna tay summm agefenta tanata nazarin meka faruwa tsakanin nur da javeed dan har yanzu basu san meke faruwa ba tukuna.

koda yajita shiru babu sautin kukantan awaje nan sai ya mike tsaye ya bude kofar da sauri ya dudduba sai yaga babu kowa awajen face janet data tsaya acan gefe tay tagumi duk ta ta kasa gaba ta kasa baya sabida tsoron kalar tsawar daya musu jiyan ya koresu a sashensan me gabaki daya.

suna hade ido ta rusuna kasa a tsorace tafara gaishesa

fuskarsa a shake be ko kulata ba yace mata taje ta kira masa na'ima, da mr aqeel dukansu su ukun su samesa a daki yanxun nan..

jikinta na rawa ta amsa snn ta mike taje tasame na'ima azaune agefen nur dake kan bacci tagaya mata general na neman su hakanan suka fito atare suka kira mr aqeel sukaje dakin suka sameshi yana zaune yanata latsa wayarsa gabaki dayan su basu gane kansa ba.

yana gama latsa wayar ya dan kallesu su ukun sai ya mike tsaye ya dauki wata abu acikin envelope ya mikawa Mr aqeel yace masa yahau jirgi ynxu yaje Abuja idan ya isa zai gaya masa mezai masa acan.

witout any question mr aqeel ya karbi aikan ya fice a dakin agaggauce.

nan ya kalle su janet fuskarsa ba asake ba yace mata karta sake barin nur tazo sashen bare ta tsaya a kofar dakinsa har sai ya bata izini.

ita kuma naima ce mata yay ta tabbata ta kulamishi da ita, ta bata magani, tasaka ta taci abinci da duk sauran kulawa kar ta sake yaji labarin cewa nur tana ciwo ko wani abu na lahani ya sameta.

daga haka yay dismissing insu
janet tafita tahau saka wasu extra security restriction asashen ta inda nur bazatana samun damar shigowa cikin wajen batare da izininta ba

na'ima ma hakan ta koma kan bakin aikinta thinking of ways da zata saka nur ta samu notsuwa tana cin abinci da sauran su kamar yadda ya bata oder.

yau ko breakfast ba ayi a gidan ba tsabar yadda anty suad take exxergerting komi ga nan su simran agefe da sukejin mugun matsuwa akan komi

dan sunso ace yau yau din nan ayima nur firdaus korar kare agidan kowama ya huta dan hatsaniyar da suka tayar agidan jiyan bakaramin dadi ya musu ba..

hakanan maganan yaki karewa saima dada zafafashi sukeyi ta kasa kasa sabida zuga lady sid da hjy zubaida da simran sukey a boye dan sunsan itace kawai zatana karawa anty suad din wuta.

hakanan suka taru a falon Alhaj attah tun safe anata jiran javeed da nur su fito

javeed bai samu wani notsuwar fitowa ba har saida ya gama magana da mr aqeel da already ya turasa neman masa sultan a Abuja dan shima so yake ya gudanar da nashi tsattsauran binciken akan rayuwar nur firdaus musnmn wnda tay a abuja da bai bada hanklinsa sosai akai ba.

he kept hoping dat ba saurayintan can bane yay ma nur dinshi fyade har da ciki ba

yana idar da sallahn azhr ya shirya kansa tsaf snn ya taho sashen mahaifinsa kai tsaye dan ya nemi wata alfarma.

fuskarsa a matukar daure ya shigo sashen yanayin sallama wani wufff anty suad ta mike tsaye tanafa kallonsa da wani irin fushi da takaici dan ko kadan bataga dalilin da har yanxu ake maganan nur ba

kawai tunda gaskiya ya bayyana so take ataru a zage nur din sann a kulleta ko ma akama familynta duka snn a saketa saki uku atake snn a muzantasu.

javeed baiko gaishe ta ba jin yadda ta fara tuhumarsa tana cewa ina munafukar take and why is she still under our roof bafa zaiyu ta zauna mana a gida ba.

shareta yay saidai duk dama gaban mahaifin sa ya dosa dan ya gaishesa yanayin yadda anty suad din take diri take zafafa lamarin al'adarsu da dokokin aure ahalinsu yaso ya jawo wani hayaniyar na daban.

javeed yay shiru yana jin yadda kowani kare da doki acikin duka matayen gida suke magana akan nur firdaus kowa na fadin albarkacin bakinsa ko wani dar dar basuji acikin ransu

musmn ma hajy zubaida datake kan claiming cewa ai wann abun ba abun rufa asiri bane tunda dai mutuncin gidan gabaki daya za'a zubar.

sanin cewa javeed bacewa komi xaiyi agabansu ba yasaka alhaj attah ya dakatar da hayaniyar tareda sallamarsu harda ma lady sid ya zamo daga shi sai anty suad da javeed din dake tsaye.

kai tsaye baban nasa yahau tambayarsa dan yaji ko nur ta gaya masa wani abu game da abunda suke hayaniya akai dan shi abun ya ishesa.

javeed yay shiru for a while kafin can ya kalle mahaifinsa yace
masa a'a basuyi maganan ba tukuna, amma zai kyautu a masa adalci abashi kwana uku dan yay nashi binciken tunda dai matarsa ce

tun kafin nan alhaj attah ya amsa anty suad ta tuma tace sam bata amince ba kawai javeed yana neman wata hanya ne da zai rufawa matarsa asiri sabida baison ace yay kuskuren auren watstsiya kuma karuwa arayuwarsa

nan tafara aibanta dabiun javeed din, kamar dama wann damar take jira all her life dan tagaya masa kalar haushin dayake bata acikin kokon ranta..

she called him names like egoistic,selfish, spoilt brat who is non chalant akan dokokin su na ahali dan yaga kawai an dorashi akan dukiyarsu da komi komi nasu kuma mother hauwa tana karramasa fiyeda kowa an dauki son duniya anzuba akansa shikadai...

wasu irin manyan maganganu take furtawa tana impliyn cewa ai dama can akan hanyar nuna warayya da fifiko aka gina adalci agidan dan da danta kamil ne ya kawo mace kamar nur firdaus da yanxu an dauki mummunan mataki akansa batare da bata lokaci ba.

haka ta gama koke koke da zage zagenta tabar musu falon tare da masa barazanar cewa bazata taba xuba ido a danne gaskiyar nur firdaus agidan nan ba saidai duk abunda xai faru ya faru.

sanadiyar wann baqaqen maganganun datay yasaka bai samu wani fuska ko fahimta a wajen mahaifinsa ba.

hakanan suka rabu ya dawo sashensa da damuwa aransa dan baban nasa baice masa eh ko a'a akan batun da ya masa na bincike ba.
Chapter 144 · 0% Book details