← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 206

Sashe 120

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hajiya zubaida da duk wann bai darata ba dan tafi tsorata da asirinta zak zak daya fara mata barazana dashi haryau batasha mmakin yadda suka san komi ba tunda ma saratun ne takashe mata bokanta na abuja.

tunda yace mata yana jiran call dinta batace komi ba ga katse wayar cikin sauke wata nannauyr ajiyar zuciya...

zaman minti biyar tay akan gadonta tana nazari kafin nan ta sauka taje tay alwala taxo tay sallah raka'a biyu tukun ta fito

tunanin yadda zata saka a daga javeed xuwa boyayyen hospital dinsu dake cikin anguwar takeyi
sanin cewa ba lallaine aji maganarta ba

tay tunanin duniya bataga mafita ba ga fargaban abunda  su manny zasu iya mata da sirrikanta na kashe mahaifyar javeed da ya hanata sakat.

mikewa tay da karfin zuciya ta shirya kanta cikin wata doguwar rigar atamfa ta sha lulummi sann tazo dakin simran ta tashe ta marmaza tasakata tay wanka domin suje su duba jikin javeed din

simran tana shiga wankan hajy zubby ta zauna ta rafka tagumi cikkn tunanin ko ta gaya mata ne ko a'a hala ko zasu samu wani hanyar shiga ta wajen lady siddika.

har simran ta fito a wanka aka shiryata  hajy zubby batace uffan ba sai da masu aikin sukabar wajen snn simran ta karaso da mamaki ta zauna ta kalli hajy zubby tace "yaa zubby lafyarki kuwa? kafin ta amsata cikin wata iriyar tuntsirewa da dariya simran tace badai ciwon javeed ne yake damunki ba sabida nasan baki dandanin kaunarsa

da wata makiritaccen sanyin murya hajya zubby ta kalle simran tace "Uhumm ke ni bata javeed nake ba ta mijina kawai nake dan idan javeed ya mutu kinga mijna zai lallace bazan gane komi ba dan haka kawai nake son javeed ya samu sauki amma bawai dan inasonshi ba, simi kinsan dai bani da wata datafiye minke agidan nan so u need to help me muyi wani abu da zau saka akaisa asibiti dan ya samu sauki da wuri kinga likitar can da aka kawo wallh bata iya komi ba itace wncan karon akan mamansa amma ta kasa sanin cewa da poison na kasheta sai daga baya da aka fadada bincike

simran tace humm yaa zubby nima dai ban yarda da likitar ba bakiga sai bubbude wa mutane ido take ba? but i dont think she is quark doctor, badge din saint george ne fa ajikinta the scnd best univesity in the world haba yaa kema ai kinsan bokan ki ne dai ya hanata ganewa ba rashin iya aiki ba.

cikin yatsina da rashin jin dadin abunda simran din tace ehh toh naji yanxu zaki tayanin ne ko bazaki tayani ba? its for ur own good too kema can asibiti zaifi miki samun kulawa kema kuma zaki iya bude wuta ana barinki kina shiga kina ganinsa duk yadda kikeso kowa zai yabeki a family yoo in kuma bakison javeed ya samu sauki ne ai shikenan na you sabi ni xan wuce inje inga meye munafukar yarinyar can takeyi ki zauna anan kiiyita dabbanci.

nan simran ta mike cikin bambami tana cewa u dont have to gaslight me yaa zubby wallahi na damu da javeed kinga jiya ko bacci banyi ba..

tace wann ke tashafa kawai in zaki taimaka min muyi muyi musaka akai sa asibiti yau insani inkuma bazaki taimaka min shikenan abarsa anan din ya mutu kowama ta huta

da sauri simran tace aa'a haba yaa zubby i want to have a life with javeed kidena cewa zai mutu..yanxu dai mekikaso muyi? shud i cause a drama

cikin mata wani irin kallo hajya zubby tace "drama me ma'ana ba irin jiya da kike nuna kamar kinfisu jin zafin dansu ba pls try to have some class.

rolling mata idanu kawai simran tay batace komi ba har suka fito dan karamin scarf tay simran ta dora akanta.

wajajen 8;40pm suka isa wajen lokacin har Nur taje tay wanka ta canja kaya zuwa wata plain black abaya ta dawo ta samesu anty suad wanda tun barin su waya kawai takeyi da mr haidar Ali dake jiyan duk matsuwarta bata samu mother hauwa a waya ba

shidinma nemanta yake kanyi dan most of the time haka takan bace musu taje wani tsauni wajen da suke ajiya ancestral books na magabata domin neman mafita..

anty suad duk ta damu dan tasan mother ce kawai zata iya gaya musu meye dace ayi agaggauce domin acire wannan mummunan dafin sihirin dake jikin wukar sabida ciwon javeed ya samu ya warke akan lokaci

shigowar su simran ya sakata katse wayar suka gaisheta ta amsa su ciki ciki dake tun jiya take famar daure fuska da kowa kamar su suka sama javeed ciwon dan ita tana mugun son jininta no matter the level of selfishness batason wani abu me sunan mutuwa yazo ya dauke wani acikin yayansu maza.

simran duk ta kasa sakewa dan banda hararar nur dake zaune agefensa babu abunda datakeyi atake kuma sai taji wasu magannun zubby ya fara shige mata kwakwala gara kawai akaisa asibitin dan ta samu damar kwace jinyar javeed a hannun wann yarinyar kaga inya warke yatashi ya gan itane mai hidima dashi zatasamu abun da zai kara kusantasu

tanaji lady sid tana bayanin yanayin jikinsan atake tafara matso hawaye duk inda akace da sauki sai ta kushe tace sam ita tafison akaisa asibitinsu tunda akwai tsaro asaka kamr likitoci goma akansa haka suna dubashi

lady sid har tausayin simran takey intaga tana kuka sai duk ta dauka damuwane yay mata tafara fadin haka.

da wasa da wasa har dayan babban likitan su na gidan shima yazo simran sai shige mai take harta so ta rudashi ya rasa gane wayene asalun matar javeed atsakanin nur da simran, duk wani abunda nur tace mai yayi sai simran ta gaya mai opposite kuma tafi zakewa sosai take daga hankli musmn idan su anty suad sukadan bada baya dama kuma tun bayan shan shayi alhaj attah da sultan suka tafi port domin karkare case din tare da tabbatar da cewa an gama wiping abunda akacemusu suyi na sauran remain din abubuwan nagaza da ya rage.

snn suka tabbata aka fito da dead fried bodies dinsu daga cikin tokan wutar aka kai forensic akayi DNA aka tabbata su din ne kafin nan gwamnati ta saka hannu aka saka acikin record din javeed aka fara turowa relvnt authorities like all these organinsation na FSB da CIA dake da boyayyan cade da nagazas

ana tsammanin kowa gwamnti tay reviewing mutuwar nagaza snn ta rubuta report da medals da sauran promotion da za'a karawa javeed mufasa duk dama basu gayawa kowa cewa javeed baida laifiya sai amintattunsu daidaiku..

wannan shirun ya bawa simran dama ta dinga matsawa tana kawo maganganu wa lady sid akan jikin javeed baya wani motsi kawai akaisa asibiti batace musu komi sabida anty suad itama tana can waje tanata kiraye kirayen can morocco ana neman mother hauwa daga lady sid sai simran sai hajy zuby ne awajen banda zugata akan akai javeed asibiti babu abunda takeyi

Nur tana jinsu taki tace komi tahade rai sabida tasan duk tsiya dai simran bata isa tasaka a daga mata mijinta anan akaisa wani waje ba Allah Allah ma take wani abu ya hadasu tagaya mata magana me ciwo sabida mugun zakewar datake mata akan mijinta ya fara isarta sai take ganin kamar rainin wayo ne kawai.

kusan ince yunwa ne kawai ya korasu a dakin simran ta fita da baqin ciki rashin samun daman taba koda hannun javeed dake nur tay babakere ta zauna a kusa dashi

sunje cin abincin kenan nur ta umarce likitan da akan ya kulle kofar shiga zata ma mijinta ruqiya tunda daxun karatun qur'ani tay jikinsa ya fara responding..

Dake suna girmamata kai tsaye yasaka ma kofar biometrics inda zallan jinin mufasa ne xasu danna kofar ya bude wani daban ba iya shigowa ba.

banda janet dake wajen da shi likitan babu kowa nur tay alwala tay sallahn azhr tana idarwa ta dawo gefensa akan gadon ta zauna tareda cigaba da karanta suratul baqararta

likitan da janet dake ciki suna zaune shiru sunata lura da monitor din ko zai motsa

wajajen karfe uku dede sai ga lady sid da ayarinta sun dawo simran hartaje ta canja wani kaya ta saka riga da wndo

mr aqeel na tsaye awaje tareda masu gadin kofar suna kallon su basuce musu uffan ba suka dinga danna kofar suna masifa amma bai budu ba,...

lady sid ta kira mr aqeel shikuwa ya gaya musu ai matar general tace kar abar kowa ta shiga ciki daga nan sai bai kara musu wani bayani akai ba.

wato tsabaragen masifar da lady sid da hajy xubby sukayi har bakinsu na tara kumfa duk tsiwarsu kuwa ba abude kofar ba.

har can da suka gaji suka je sama suka kira anty suad suna ta masifa sun harhada sharri cewa ai nur ta musu rashin kunya ta koresu a dakin tasaka an kullesu awaje

haka tazo itama sai sukaga tana dannawa kofar ya budu...

tama lady sid din wani mugun kallo a mugun hatsale tace siddika kikacemun kofa baiya buduwa?? kafin lady sid ta amsa taja tsaki tana shiga ciki suka bita yuuuuu sai samu sukay nur tanakan masa karatu zufa ya fetso masa ajiki

likitan duk ya rikice yana kan masa kwaje kwaje dan tunda aka kawosa kamar dutsi yake jikinshisa kuma is cold harsai nur ta fara karatu sai kaga yay dumi yau kuma sukaga har zufa yake fitarwa..

anty suad dataga haka sai bata bari sun katse  karatun nur ba ido kawai tama janet ta kadosu duka suka fito har waje

nan janet take mata bayanin komi agbansu ran hajy zubaida ya turmushu ya mugun baci dan harta kasa boyewa musmn dataga anty suad ta dada aminta da cewa ciwon javeed akwai sihiri aciki dan haka dolene abar nur tana karatun akai akai kafin asan nayi dan itace kawai yanxu hope dinsu kafin mother hauwa ta fito.

wa janet kawai ta bude kofar tace ta zauna tana lura mata da komi idan wani abu ya canza ko ya fara yin tsanani tazo maza ta gaya mata tana falo
Chapter 120 · 0% Book details