← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 154 OF 206

Sashe 154

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kowa ya kama kansa with deep sense of maturity har aka shigo babban falo javeed ya taimaka ma mother har ta zauna akan dogon kujerar tsakiya but as a sign of immense respect yasaka babu wanda ya zauna kusa da ita infact saida aka bada ratar kusan kujerar gefe da gefenta kafin nan aka zazzuna ana biyun, maza a gefe guda,.. Hjy amirah agefe daya.

da daddaya da daya aka fara gaisuwa a mutunce kowa ya gaida kowa har gaban mother ake xuwa a rusuna ayi gaisuwa ita kuwa sai albarka take saka musu tanamai tambayr javeed jikinsa tana kara sakamai albarka akan rabasu da ahalin nagaza da yayi.

ana cikin gaisawar ne
private servant suka hau cike wajen da ababen ci da sha ana jefa hira kadan kadan nan take kowa ya fara serving kansa da abun sha javeed ne kawai yamike tsaye ya fara zubawa mother wani all fresh green drink of pure turkish grape zai mika mata kenan suka ji taku me tattare da zazzafar huci anty suad dinne ta shigo a fusace kamar an wurgota cikin wajen idonta a rufe wanda tsabar bacin rai da zafin kai tana shigowa azafafe ta wurga ma javeed bedsheet din ajikinsa saida juice din ya zuba ajikin mother gabaki daya..

tsaye kowa ya mike anata kallonta da mamaki musmn ma danta kamil da haukar zafin ran mamansan ya fara bashi haushi

mother ce kawai bata ko motsa ba bare tadaga ido ta kalli me suad din takeyi..

cikin daka tsawa alhaj Attah yace 'suad meye haka... are you out of ur mind? da wani irin ihu me tattare da zafin kai tace masa yess,.. i am out of my mind ya attah.

ahaukace tabi tasake wawuso bedsht din sama ta rike snn kalli javeed da already yacire farin hankynsa daga aljihunsa ya fara goge ma mother stain din juice din dashi da alamar kamar baisan ma suad tana magana da shi ba...

zatay magana cikin katseta danta kamil yace haba mummy what the hell is this dan Allah control urself mana.

juyowa tay a fusace ta nunasa da yatsa snn tace zanci ubanka in baka min shiru ba anan wajen ba da javeed nake magana i am not talking to u..

ran kamil abace ya koma kan seat dinsa ya zauna ya cigaba da shan drink dinsa

javeed ya mike a nitse suna hade ido yace wai meyafaru ne anty... is evrything alryt

tace "meyafaru ma kake tambayana? like really?.

daga zanin gadon sama tay ta hau nuna ma kowa ana kallo a mugun zuciye tace meye wann abun da ka aje min akan gado na.

adan shashance yace ohhhhh its the blood price did u like it?

tun be rufe baki ba ta saka ihun hatsala tace "karka rainamin wayo agaban mutane javeed niba saarka bace did u hear me

ganin he is still calm bai ko kulata ba yasa tadada harzuka tafara kame kamen masifa

hawayen datake dannewa ya fara xuba a zucye take cewa karya kakeyi wallh, yarinyar can ba virgin bace tay ciki takuma zubar we all knw dat javeed nafi karfin kaci mutuncina agaban kowa i know what i saw, this stain proofs nothing wallh baka isa ka maida mu kananan mutane ba..

muryansa a nitse still yace cmon anty this isnt a trophy or any damn proof its the apology u've been waiting to happen...
kece kikayi fushi akan matar dana aura u keep calling me names and insulted me every little chance u got, baba kuma yace kece da gaskiya na baki hakuri shine ynxu na baki hakuri, so why are u mad at me dan na baki abunda kike so??ko ba akan wann abun kike fushi damu ba..

zatay magana cikin katseta yace...a piece of paper kawai wasu na daban suka nuna miki, wasu wanda ba jininmu ba, ba masoyanmu na gaskiya ba, kuma kin san da hakan amma kika runtse ido kika karba gaskiyarsu kika hau kai, just so that u can humiliate my wife, demoralized her and touched her dignity with dirt, shine na dawo miki da zarginki all wrapped in her blood dan bansan me kikeso nayi ba, nide nasan it wasnt my wife ure fighting or humiliating, it was me, infront of all those strangers. u called this family meeting by urself yanxu saiki gayawa kowa abunda ni nake miki persnally and i promise i will apologise to you ryt now..

budan baki tayi jikinta harna rawa zatay magana cikin wani irin daka musu tsawa alhaj attah yace suad is enuf...both of you..javeed isa haka have some respect.

javeed ya mugun hade ransa yakoma wajen zamansa shima ya zauna abunsa aka barta ita daya atsaye agaban mother da bedsheet din ahannu akangare kamar wacce bata motsi..

wani irin shiru falon ya dauka for a while ayayinda sauran ma duka suka xauna kamil ya dada sunkuyar dakansa kasa yay shiru bai sake iya daga kansa sama ya kalli kowa ba

cikin dauriya tare da tattaro makanta nitsuwa tadan rusuna kasa amugun raunace zuciyarta akarye tay da kanta kasa tafara gaishe da mother wacce bata nuna komi akan fuskarta ba ta amsa ta normally ba fushi ba komi, tana mikewa kamar zata fita mother ta umarce akan ta aje stained bedsheet din agabanta snn ta nemi waje kusa da amira ta zauna..

kanta na kasa ta nannade bedsheet din ta aje agefen mother snn ta nemi waje kusa da hajy amira ta zauna tay shiru dan kodaga yanayin yadda kowa ya hada rai ya dauke ido akanta tariga tasan furucin javeed ne yay tasiri a zukatan yan uwansa.

atakaice dai kamar daureta ya dadayi da jijiyar wuyarta a idon kowa dan dolenta tay shiru dan ita kadai tasan meke mata ciwo aranta yanzu..

daga bangaren su simran kuwa tun ficewar lady sid sashen javeed dazo sukahau tada hatsaniya da hajya zubaida a dakin kamar wanda zasu daku da juna.

dan kwata kwata hjy zubaida batasan cewa da duka duka kudin ubansu simran tay facakar kayan aurenta ba gashi ta tattara valuables dinta duk tay kyauta dasu da ya kure ma hajy zubbyn tunani da tsammanin inta aure javeed zata samu fiye da irinsu awajensa

almost all her expensive designer bags, da valuable jeweries, da kayan sawarta masu shegeb tsada kai kusan wadrob dinta ma emptyn dinsa ta kusa yi dan kawai ta burge kawaye susan cewa ba baki take cika musu ba zata aure javeed mufasa kuma tunda javeed ne dole kyauta yayi nauyi dan haka tabayar da masu shegen tsada waidan kar araina mata aji.

hajy zubaida kamar numfashinta zai bar jikinta haka nan take azazzala masifa wa simran suna cacar baki me zafi kamar zasu bugu dan dama daurewa kawai takey agaban lady sid din tana nuna babu komi amma yanxu haka bata san ya baban su zaiji inyasan abun da simran tay da kudinsa ba.

simran dake jin kanta amarya tabi ta nace tanata cewa ai ana gama case din nur firdaus za'a bada sadakinta zata dawo musu da abun da yafisshi har gori saida tay ma hajy zubby tace mata me baqin hali duk dama tana cikin gidan mufasa amma ai bata ma ubansun komi ba bayan siya musu gida da abinci datakeyi.

bakaramin zage zage da rigima sukayi da juna a dakin ba har saidai lady sid ta dawo snn sukay shiru suka wanye..

ita ta gaya musu cewa ai ahalin mufasas din duk sun bayyana ana can anata tattaunawa

tana gama rufe baki taga simran ta mike zumbur da rawa rawan jiki da tumin kayan amaryanta daya maida kamar bebin robber yana janta tana janshi wai zataje tay gaisuwa gata amarya

lady sid ce marmaza ta kwabeta tace mata ai idan mufasas suna tare dukansu musmn ma inda mother aciki wani wanda ba jininsu baya zuwa wajen har sai sun nemi mutum dan haka su rufawa kansu asiri su zauna anan din kawai harse an nemesu dan tana fita sheik haidar ma kadai zai iya harbeta kuma ya harbe banza and they will not pay or apologise kawai za'ayi dumping dead body dinta ne at the sea.

iyaka wann maganan kawai ya saka simran nitsuwa dan a mugun matse take taji an kirata ko ance an daura aurenta da javeed ko zama batay ba tay nan tay nan tana kallon kanta a mirror dan duk dama an mata kwaliiyar da saida tafita a hayyacinta amma gani take kamar bata gama haduwa ba.

jin gidan ya dau shiri tafara matsawa hajy zubaida akan akira babansu ko kawunsu kawai ace musu su dauko hanya suzo yanzu aganinta ai case din nur dinma bazai dau wani lokaci ba tunda da shaida a hannu.

hajiy zubby abun ya isheta da bacin tace ma simran din a ina ne tataba jin iyayen amarya sunzo gidan ango tun iyayen ango basu nemesu ba...?

simran taki jin wann yqren sam tanata kawo dalilai waigata ita wayayya lady sid kuwa tun abun bai mata sense ba har ta fara biye ma simran dan gani take daga zarar simran ta aure javeed she will request a rare piece of diamond stone daga wajenta tunda kowa yasan javeed kadai yake da makullin ajiyesu. shiyasa bata damu ba duk abunda simran ta fada ko shirme ne sai tahau bin bayanta tana bata gaskiya..

duk yadda hjy xuby tay fushi kuma taki jinin akira iyayensu amma hakanan suka fi karfinta simran ta kira babansu tace masa kawai suzo adaura aurenta ynzu ai mother din tazo tanacan falo yanxu za'a gama case a fara zancen aurensu.

babanta yace toh ai mufasa ne zasuzo neman aure wajensu basune zasu je ba.

tun be rufe baki ba simran ta fara masa ihu da kuka gashi dama itace autarsa ya sakalta ta sosai..

karshe dai ya gaji da kukanta yace mata toh shidai bazaizo ba dan haka mufasa ya auri zubaida da zallan sadaki daya bata a hannu akaskance kamar wata karuwa ko marar gata haka a dora auren agaggauce ba'azo gida ansamesa ba karshe shine ya zo

yanxun ma haka zai turo uncle dinsu ne kawai guda biyu in auren yay yuwa toh shidei yace bazaizo ya kurbi walakanci ba.
Chapter 154 · 0% Book details