← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 206

Sashe 15

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

jadidah dake kallonta cikin sanyin jiki ta share dan guntun hawayenta snn tace
"koma miyene nur i am so hppy seeing you like dis. this is the best gift u can ever give to urself. nikaina ban samu sukuni akan maganan zargin da ake miki wai anmiki fyade kinyi cikin shege ba, sai kuma ga auren laylah da adnan...i know this wont be easy on you my friend
amma bakomi Allah yana nan. lets us not talk abt the past nide kawai Allah yay ma kawunkin nan albrka
sabida bansan ya zan gaya miki yadda kika canza ba wallh kamar bake ba.

nur tay murmushi me nauyi tace Mungode Allah jd...and thank you soo much for being a true friend to me, bazan taba manta ki ba. daga haka suka dan rungume junansu

kafin nan jadida taje ta kawo musu ruwa nur bata wani sha ba suka danyi hirar schl da abubuwan da suka dan faffaru musmmn yadda mahaifyr malika tazo tay ma malam bello gori akanta har makanrta.

tace kawata amma karki damu many ppl defended you..kuma kinga da akay auren adnan sai yasaka aka kara yarda cewa layla karya kawai take miki dan ta aure miki saurayinki, shikenan kuma case dinki yazo yay sanyi a makaranta
..infact i have sumting to show you..nur na kallonta har taje daki ta dauko wani jaka, ta mika mata tace these are ur awards. duk da baki schl kuma ana ta cece kucen amma Allah bai yadda wani abu ko wani mutum ya tozartaki ba, inagama kinfi kowani dalibi samun karramawa, toh malam bello sun nemi mamanki taki zuwa shine kawai da muka gama exams akay graduation aka bani akace in aje miki abubuwanki

Nur tasha makurar mamaki dan da can gani take kamar sunanta yagama baci a schl ashe ashe Allah ya rufa mata asiri ata yanayin da batay zato ba..

atake kuwa tay sujudur shukru ta mika godiya wa Allah da ya killace mata sirrinta baikuma so ta tozarta a idon duniya ba duk da mummunn qaddarar da rayuwa yazo mata dasu...

bayan nan hira suka sha da jadida kamar bazasu rabu ba har suna ma juna alkwarin sake haduwa dan jd din tariga ta cika ABU zaria zata karanta medicine nd surgery

sunakan hirar kira daga Kd yabi ya ishe nur tay marmaza tama Jd sallama tare da bata kyautar kudi inda ta kwashi tarkacen gifts da awards dinta ta rakta dasu har mota snn sukayi sallamaa cike da kewar juna...

acikin sauri Driver yake tukata sabida suy catching in flight inta on time sabida kusan baifi minti 30 ya rage jirginsu ya tashi ba. she was on call da hajya sadaatu throut har suka iso gate na filin jirgin, tana aje wayar tasaka hannu tabude hadadden white colour valentino garavani bag dinta wanda yake nan dede da kalar hadadden wandon falazonta ta dau setting powder ta dankara gogawa snn tadada gyara kwalliyar dake kan lips dinta ta fetsa seting spray just to refresh her classy and gorgeuos looks dan babu karya ynxu tafijin dadin taga jikinta soo neat and groomed barinma da kawarta jadidah ta bala'in kara mata karfin gwiwa ayau.

banda sanyin iskan A.C hade da sabuwar qamshin turaren data fetsa ajikin elegant blazer dinta dayake refreshing dinsu a motar bakajin shaukin komi, koda ta dada kimtswa sai fuskarta ya dadayin haske tare da mahaukacin kyau wanda tunda ta dire kafafunta kasa idanu ke bibiyarta yuuuu kamar anga wata sabuwar halitta...

she cant even tell weda kayan jikinta ake kallo ko fuskarta koko wann sanyin ajin tare da kasaita dake yawo ajikinta dat speaks alot of classy girl volumes..

batare da tay lkcin kallon uban kowa ba acikeda kwarjini take tafiyarta calm-slow nd majestic yayin da ta karaso lounge din jirgi tana duba ticket dinta,

tagama gyara zaman farin specs dinta bisa idanuwanta kenan zata juyo Idontan ya sauka a wata rukuni da ke gefe dauke da zugar Iyalan Shehuri.

da alama dawowar su daga qasar paris din kenan an dawo daga hutu.

Adnan Shehuri idonta yafara hangowa jin gabanta ya fadi ganin yadda adnan din ya dan rame ya lalace babu wani kwalliyar big boys daya saba atattare da shi kamar dai ba shi ba.

yana sanye da simple kaftan baiko saka hula ba yana gefen wani dan uwansu yana duba wani abu a wayarsa can daga Gefensa ata gaba kadan sai taga yar uwarta Layla, cikin wata abayarta data bar mata tun agida da makeup mai nauyi a fuskarta wanda duk da haka kwalliyar bai boye rama da rashin walwala da jin dadi dake dawainiya da ita ba, saikuma taga Mahaifyar Adnan din da aunties dinsa guda biyu sun dan zauna jiran kayansu suna dan hira.

cikin sauke ajiyan zuciya tare da tattaro makanta nitsuwa tare da kwanciyar hankli kai tsaye cikin yarda dakanta ta tunkaraso
cikin wata iriyar nitsutsiyar tafiya me aji tare kasaita inda kusan dukansu suka dago kai sunata satar kallonta tunma basu sancewa wajensu ta nufa ba, adnan ne kawai be daga kai ba
dake tunda ya rasa nur a dame yake takaicin duniya sun cike masa kansa

sauran members na familyn da suka saka hanklinsu akan isowar nur ji suke Kamar lokacine ya tsaya musu cak musmmn ma da bata cire spec din dake idonta ba har saida ta iso daf dasu

layla tuni ta tsaya durus cikin wani nauin rudewa tanajin brain dinta kamar zaiyi exploding sabida zazzafar muhawarar da kwakwalrta yake dan takasa yadda da abunda idanuwanta suke gani ahhh ahhh nur ce, ba nur bace duk dai ta kasa tsayawa akan tunani daya ji kawai tay iska datake shaka ta dauke mata walwalan komai.

da wani irin calm killer smiles nur ta tsaga cikn securitynsu snn ta iso garesu lkcin hjy mairam ta bude baki cike da mamaki..

tanata kallon nur din data taho garesu kamar wata Sarauniya cikin kwayar idonta na tattare da nutsuwa da calm voice dinta me aji acikin jam'i kawai tace musu sallam alaikum, nan take Aunties din adnan suka kalle juna da yanayin wacece wannan a fuskokinsu.
dan ko kadan basu ga kamanninta da laylan bama.

ganin sun kureta da kallon kauyanci basu amsata ba cikin kyabe baki tabarsu da shakar muguwar dadin qamshin turarenta acikinsu, kai tsaye tay wajen Adnan da tunda yaji sautin muryanta komi ya tsaya masa cak yabi yazura mata ido yana jin wani bugun zuciya da bai taba jin irinsa a rayuwarsa ba

shikasan da yanayin kokonto yake kallonta irin anya Shin wannan Nur dina ne kuwa?

lura da hakan yasa tay murmushi tace hey Assalamu Alaikum, Adnan.”

a rikirkice Adnan ya sake kallonta da dan murmushi mai nauyi duk dai ya rude yace
“Wa alaikum salam habib..ty?
tana murmushi ta dan kashe masa ido..yace ”oh my god, da dan karfi da kuma mugun murnan ganinta a muryansa ayayinda yake kokarin hadiye dumbin mamakinsa.

baisan sanda yataho kamar zai hadiyeta ba
suka tsaya dukansu suna ma junansu murmushi..

ahankli tace yaya kake how are you?? kasa iya danne hawaynsa yay idonsa yay jjaaa muryansa nadan rawa yace i am good..u look, u look...god damn..kawai saiya dan shafe kansa ahnkli cikin rasa mema zai fasalta ta dashi.

kkrin hade ido take dashi dan ta kara masa karfin gwiwa amma inaa ai saida ya sauke hawayen sann yabi yashare shi da sauri yacigaba da mata murmushi.

itama murmushin ta masa cikin jin mugun tausayinsa aranta tace i am lucky to have seen you here you qalbi ashe da dalili da Allah yasaka na buga latti...dariya yay dan qalbi data fadan duk dama a acikin raha ne amma har ransa yaji mugun dadi har yadan dawo hayyacinsa..

kai tsaye ya fara kkrin zaiyi introducing dinta ma familynsa dama inba a hoto ba ko mum dinsa bata taba ganin nur firdauus a reality ba. wacce tin tsayuwarta awajen gabaki daya suka zuba mata ido da imaninsu suna kallon tundaga kyaun halitatr izuwa hadadden dressing inta da uwa uba wann dan uban kasaita da ajin da sukagani na zuba ajikinta gwanin burgewa.

sede tun kafin nan yay magana nur ta juyo gefensa Ta matsa kusa da Laylah wacce fuskarta already ya gama nuna alaman radadi gamida da karaya, dan fadin halin mamakin da ta shiga data san wai nur ne wann bazaima fasaltu ba. dan koda ta kalle kanta takalle nur din sai dataga tay kama da wata baba me kosai a kauye gashi abun kunyar ma waifa tsohuwar bayan nur dinne ajikinta.

suna hade ido tahau zuba fake smiles wanda dakyar ma yake fitowa muryanta akakkrye tace big sis?

ko ajikin Nur firdaus tazo har gabanta calmy tay mata murmushi me sanyi snn tadan rungumeta slightly tay resting agefen kunenta ahnkli snn tace mata good to see you little sis, lallai aure ya karbeki.

wani gulloton baqin ciki layla taji ya tsaya mata a wuya batama iya cewa komi dan tasan inda bude baki kawai gani zaayi tana kukan da bata san dalilinsa ba yanzu

nur tana zare jikinta suka sake hade ido tace layla naga sakon mummy wai kinyi ciwo, to Allah ya kara sauki ..ta fada da nutsuwa bata tsaya jin me laylan zatace ba
..ta juya kan adnan dake washe baki yana Allah Allah ta juyo ya nunata ma uwarsa abunda tay masa asara shidai babban damuwarsa kenan mum dinsa taga nur ta gane cewa tabbas ta cucesa shiyasa kuma haryau bazai dena bata ciwon kai ba.

nur tana juyowa ya fara nuna musu ita mummy ga habibty, itace nur firdaus..
yabibbi anties dinsa da dan uwansa duk ya nuna musu ita.

hajy mairam gabaki daya tarin baqar magana ne abakinta amma yanayin dataga sanyin aji da kuma haduwar nur din yasaka ta kasa iya cewa komi sai yake take ma nur tanamai saka mata Albarka na dole. lallai haseena ta iya haihuwa dayan antyn tace toh ai wann din ma tafi haseenan kyau...dayan ma ta dinga cewa eh wallah masha Allah ai banyi tsammanin yadda Hasina take da kyau dinnan har zata haifi yar da zatafita aji ba wow tubarkallah..

ana cikin haka saiga attendant excuse me ma'am, ur flight is abt to take off. ke kadai ake jira...nur batace komo ba ta gyada kai alaman tana zuwa.
Chapter 15 · 0% Book details