← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 122

Sashe 97

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mu je.." Ta bi su da kallo sanda suka fice ɗin, a ranta tana jin daɗin hakan, ko babu komai ta san mazan gidan za su shigo sashen ba tare da sanin Mommah ta fita ba. Ita kuma dama irin wannan damar take so. Se dai abin da ba ta sani ba Mommahn tare suka fita da su Gwani gaba ɗaya, dan za su je su gaida su Ummeeyn ne kafin su baro su Mommahn a can. Da farko da ba ma tare za su je da su Lulu ba, se dai Mommah ta san duk lokacin da ba ta gidan Areef kan iya amfani da wannan damar wajen zuwa wajen Didi. Shi ya sa ƙafarta ƙafarsu.

.. "Yallaɓai lafiya na ganka haka?" Mommah ta faɗa tana kallan Daddy. Se ya yi murmushi kafin yace

"Abin da zan tambayeki kenan kika riga ni. Ko dai kin saka damuwa ne cikin ranki?" Girgiza kai Mommah ta yi kafin tace

"A'ah.."

"Idan ma dai damuwar abubuwan da suka faru ne, toh ki kwantar da hankalinki tun da komai ya warware. Idan kuma komai ya sake lafawa se ku je ku ziyarci dangin mahaifinku." Jinjina kai Mommah ta yi cikin na'am da zancen Daddyn sannan tace

"In Sha Allah.. Amma kuma Yallaɓai ka kautar da tambayar da na maka." Rufe idanunsa Daddy ya yi kamin ya buɗe. Be san ta ina ze fara ba, har yanzu ya kasa mantawa da abin da Mom ta aikata. Zuciyarsa har yanzu ta kaasa samun sukuni. Ban da wannan babu abin da ke damunsa.

"Kar ka ki wani damu. Babu abin da ke damun mijinki." Ya ƙare cikin barkwanci. Dariya Mommah ta yi cikin ranta tana fatan Allah Ya yaye musu damuwarsu gaba ɗaya. Se suka ƙarasa wajen motar duk suka shiga. Areef da ke zaune a wajen zaman driver ya ja motar suka fice daga gidan.

Sosai Ummeey ta ji daɗin ganinsu cikin gidan, musamman da ya kasance dukansu ne suka zo. Dan haka babu ɓata lokaci ta shiga hidima da su. Lokacin da suka je, sun samu Abeey zaune a kan tabarma da pillow a bayansa. Ba ya jin daɗi, se dai kamar ko yaushe nunawa yake tamkar babu abin da yake damunsa. Se dai da yake Gwani ya san hali hakan ne ya sanya shi ƙarasawa kusa da shi yace

"Abeey ko dai ba ka jin daɗi ne?" Lalubo murmushi ya yi ya wanzar a kan fuskarsa kafin yace

"Kar ka damu.. Babu abin da ke damuna. Ciwo ne dai irin na yau da kullum da ka riga ka san shi."

"Shi kenan kuma?" Gwani ya sake tambaya. Se ya jinjina kai yace

"Ehh In Sha Allah.." Ya faɗa cike da tabbatarwa. Dan da gaske a lokacin ba ya jin komai, se dai da ciwo sosai ya kwana. Da safen nan ne dai kuma se ya ɗan ji sauƙi. Bayan wani lokaci Bad Man da Gwani suka yi sallama da Mommah da Abeey saboda zuwa da za su yi aike da Daddyn ya musu.

"Toh ku gaida gida Allah Ya tsare.." Ummeey ta faɗa tana murmushi.

"Ameen Ummeey.." In ji Gwani. Se ya maida su amsa kan Abeey yace

"Abeey.." Kallansa Abeey ya yi kafin yace shi ma da murmushin a kan fuskarsa

"Allah Ya tsare hanya yarana."

"Ameen Allah Ya ƙara lafiya. Yau babu karatu ne Abeey?" Gwani ya yi maganar duka a lokaci ɗaya. Girgiza kai Abeey ya yi kafin yace

"A'ah akwai.. Amma Abbati ne ze gabatar yau ɗin.. In Sha Allah se zuwa gobe zan fita." Addu'a Gwanin ya sake yi, kafin ya bi bayan Bad Man suka fice daga gidan. Ko a gidan Ummeey su Didi ba su matsa daga kusa da Mommah ba har se bayan da su Bad Man suka bar gidan sannan ta barsu suka shiga ɗaki. Se a lokacin sannan Daddy ya gyara zama, bayan ya sauke ajiyar zuciya yace

"Wato da ma mun zo ne mu sake godiya a kan abin da aka mana.. Muna sake godiya, Allah kuma ya saka da alkhairinsa. Se kuma magana a kan ragowar abubuwanku da ke hannuna.."

"Godiyar ta isa haka Yallaɓai.." Abeey ya faɗa yana murmushi. Hannu Daddy ya saka ya ciro keys daga aljihunsa ya ajje su a gaban Abeeyn sannan yace

"Waɗannan mukullan na gidaje ne guda biyu.. se kuma motoci guda biyu.. Waɗannan kuma kuɗi ne a ciki, se dai abin da nake so ka sani ba ni ne na baku ba. Ba kuma ita mahaifiyar yaran nan ce ta baku ba.. har yanzun dai daga cikin kyaututtukan da abokaina suka muku ne. Ina fatan ba za ku ce a'ah ba." Girgiza kai Abeey ya yi kafin ya soma faɗin

"Haba.. Wannan se kace kuna neman biyanmu abin da muka muku ne? Mun yi haka ne don Allah ba don komai ba.. Ba kuma dan a biya mu ba.. Saboda haka don Allah ka riƙe waɗannan kayan sun yi yawa. Waɗanda muka karɓa ma Allah Ya amfana." Girgiza kai Daddy ya shiga yi.

"Wato Malam har abada ba za mu taɓa iya biyanku abin da kuka mana ba.. Su kansu ba sun yi hakan ne dan su biyaku ba, se dan kawai su nuna farin cikin abin da kuka mana. Se kuma abu na gaba.. Mun duba na duba, Mun ga me ya kamata mu yi muku da ze sa ku shiga makamancin farin cikin da muka shiga dalilin wannan abun alkhairin da kuka mana. Shi ne muka yanke shawarar biya muku aikin Hajji ku je ku sauke farali.. Amma don Allah kar ku ce a'ah. Bayan ita ma ina so don Allah ku faɗa min idan da akwai abin da kuke so ko mene ne shi ku faɗa min, ni kuma In Sha Allah zan samar muku shi idan dai har be fi ƙarfina ba." Kallan Daddy Abeey kawai yake yi cike da mamakin abubuwan da ke ta fitowa daga cikin bakinsa. Makkah? Su yau su ne ake faɗin za a basu kujerar Makkah? Shin da gaske ne ko kuwa dai mafarki ne? Lallai Allah me yadda ya so. Lallai Daddy mutum ne har da rabin mutum. Wato shi ne kuma bayan duk wannan abubuwan yake tambaya idan akwai abin da suke so? Su kuwa me za su buƙata bayan irin wannan tarin alkhairan da Alhaji Matawalle da makusantansa suka masa? Kuka kawai Ummeey ta fashe da shi, dan ta rasa me ma za tace ita kam. Wannan abun alkhairin har ya yi yawan da ta kaasa furta komai.

"Haba.. ki dena kukan nan haka mana.." Mommah ta faɗa tana kallan Ummeey. Girgiza kai kawai Ummeeey ta yi ba tare da tace komai ba. Dan har i zuwa lokacin ta rasa me za tace. Godiya sosai Abeey da Ummeey suka musu cikin matuƙar farin ciki. Har lokacin ganin abun suke kamar mafarki. Kafin su tafi Daddy ya shigarwa da Abeey maganar da yake da ita.

"Wato da so samu ne.. da duk gidajen se ku saka haya a ciki.. Zan saka a gina muku wani gidan a kusa da nawa se ku dawo nan ku zauna." Daddy ya faɗa cike da fatan su amince da hakan. Dan kamar hakan se ya fi musu. Ko babu komai sun zama kusa da juna kenan. Musamman da yanzun ya fara tunanin sakawa a ginawa Gwani da Bad Man gida su ma duk a kusa da nasa, dan ba ya so iyalansa su rabu.

"In Sha Allah se a yi hakan." Abeey ya faɗa. Murmushi Daddy ya yi yace

"A'ah fa Malam shawara na bayar.. Kuma yanzu haka tafiya za mu yi idan ka yi shawara se ka sanar da ni. Idan kuma akwai unguwar da kake son zama ne a ciki duk se ka sanar da ni."

"In Sha Allah." Abeey ya faɗa jikinsa a sanyaye. Har lokacin yana jinjina irin alkhairansu Daddyn a gare su.

.. A ɓangaren Bad Man jira kawai yake yi su Mommahn su dawo. Se dai sam se be san lokacin da suka dawo ɗin ba. Dan haka kai tsaye sashen Mommahn ya wuce, cikin zuciyarsa yana sake mamakin wannan lamari. Abu se kace wanda aka jefa, gaba ɗaya ya bi ya chanja tamkar ba shi ba. A kan mace ne yake ta wannan abun se ka ce almajiri. Se dai zuwansa sashen Mommahn ma se ya yi danasanin zuwa. Dan kuwa yana shiga ya yi daidai da fitowar Mommah daga ɗakinta kenan. Ta kalle shi dan ba ta tsammaci shigowarsa ba.

"A'ah.. Areef.." Ta faɗa tana kallansa.

"Na'am Mommah.. Ashe kun dawo?" Ya ƙare yana ɗan babbasarwa. Kallansa ta yi sosai yanda ta ga yana ta wani ɗaɗɗauke kai ya sa ta fahimce shi. Ta girgiza kai tana murmushi a kan laɓɓanta ta furta

"Za ka gane kurenka ne." A fili kuma se tace

"Ehh.. mun dawo.. Ƙaraso ka zauna mana.. Ko dai akwai wani abun ne?" Ta tambaya lokacin da ta ƙaraso cikin ɗakin. Girgiza kai ya yi kafin yace

"A'ah fa.. babu wani abu.. Kawai na zo na duba ne ko kun dawo." Ya ƙare yana maida hannayensa cikin aljihun wandonsa yana sake basarwa. Murmushi Mommah ta yi, duk wani take-taken Bad Man ɗin ya nuna abin da ke ransa. Wato se bayan ya gama wahalar da su sannan ze dawo ya ɗauka ze sameta ne cikin sauƙi. Kamar yanda ya yi wasa da su su ma se sun yi wasa da zuciyarsa. Ganin yanayin Mommahn kamar yau ɗin za ta ba shi goyon baya ya sanya shi faɗin

"Mommah don Allah.." Se da ta sauke numfashi kafin ta katse shi da faɗin

"Kaa ga in dai dan yarinyar nan ne kar na sake ganin ƙafarka cikin sashen nan. Idan wajena ka zo ka zauna a first palour zan fito mu gaisa. Ba za ka kuma shiga ɗakina ba har se na mayar musu da 'ya." Be fahimci abin da zancenta na ƙarshe ke nufi ba, hakane ne ya sa be ba shi muhimmanci ba. Se hankalinsa ya karkata a kan maganarta ta farko. Kenan ba ze din ga ganinta ba? Yana shirin cewa wani abun se nemar Mommah ya yi a wajen ya rasa, dan idan ta cigaba da kasancewa wajen tausayin ɗan nata ka iya sakawa ta janye maganarta.
Chapter 97 · 0% Book details