← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 122

Sashe 107

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na bar maka." Murmushin gefen baki ya yi kafin yace

"Ba na so.. Mu je ki kwanta ko kuma na.." Tun kafin ya ƙarasa maganar ta juya da sauri saboda ganin da ta yi yana maganar yana matsowa kusa da ita. Hawa kan gadon ta yi da sauri ta kwanta. Ta ja ƙaton blanket ɗin da ke ajje gefen gadon ta kima a kanta. Be san sanda dariya ta ƙwace masa ba.

"Wannan yarinya.." Ya faɗa yana girgiza kai. Ya ɗauki fiye da awa ɗaya zaune cikin ɗakin bayan kwanciyarta yana karatun Alqur'ani. Bayan ya idar ya shiga istigfari. Abin da ya zamar masa jiki kenan yanzu. Kullum kafin ya kwanta se ya yi. Haka kuma duk lokacin da ya idar da Sallah ma se ya yi, saɓanin da da se ya kwana fiye da 3 ma be yi karatun ba. Ninke daddumar da ya tashi daga kanta ya yi ya maidata inda ya ɗauka kafin ya kalli kan gadon. Fuskarta a buɗe take, ya yin da ilahirin jikinta ke a rufe ruff. Bacci take hankalinta kwance, kai ba za ka ce akwai abin da ke damunta ba. Ya lumshe idanunsa yana ji kamar kar ya dena kallan kyakykyawar fuskarta. A hankali ya ƙarasa ya hau kan gadon. Kai tsaye hannu ya saka ya yaye bargon da ta lulluɓa da shi ɗin. Dan garin ba zafi ake ba haka kuma ba sanyi ake ba. Gyara mata kwanciyar ya yi, saboda yanda ta kwanta ɗin a takure. Ji yake tamkar ya barta a jikinsa ko da ze samu baccin yau ɗin ya kasance na daban, ya yi baccin da ya daɗe be yi irinsa ba. Se dai ba ya so ya zama sanadin hanata bacci, hakan ne ya sanya shi komawa gefenta ya kwanta. Se dai duk da haka kasa ɗauke idanunsa ya yi daga kanta. Cikin ransa yana ji damuwar da ke cikin ransa kaso me yawa na raguwa daga cikinta.

Washegari.. Sauri sauri take ta fito daga wankan ta shirya kafin ya shigo ɗakin. Dan tun ɗazu take so dama ya fita, amma be fita ba se yanzu. Hakan ne ya sa tana gamawa ta fito, kai tsaye wardrobe ta nufa inda ɗazun ta gan shi ya jera mata kayanta ciki. Daidai lokacin ya shigo cikin ɗakin hannunsa ɗauke da babban tire, wanda ya karɓa yanzun nan daga hannun Baba Atine.

"Good morning my dear.." Ya faɗa yana ajje abun hannunsa a inda ya dace. Ita dai kawai se ta bi shi da kallo ganin fuskarsa ɗauke da annuri kamar wanda aka yi wa albishir da gidan aljanna. Se dai ba ta sani ba duk farin cikin dawowarta cikin rayuwarsa ne ya kasa ɓoyuwa. Se da ya ajiye kafin ya juyo inda take tsaye ta kasa aiwatar da komai. Cikin kulawa yace

"Kin tashi lafiya?" Ya faɗa yana zuba mata idanun nan nasa. Duk se ta dibirbirce ta ɗan soma gyara tsayuwarta. Murmushi ya yi yana kallan cikin wardrobe ɗin. Hannu ya saka ya ɗauko wata riga coffee colour da adon milk colour a jikinta.

"Zan iya taimaka miki?" Ya faɗa dan ba ya so ya yi wani laifi kuma. Da sauri ta girgiza kai tana saka hannu ta riƙo rigar hannun nasa.

"Zan saka don Allah.." Ta faɗa a marairaice. Sakar mata rigar ya yi yana yin gefe ya bata hanya wai dan ta wuce. Da sauri ta ɗaga ƙafa dan matsawa daga wajen ko ta samu ta saka rigar a nutse. Se dai yanda ta tafi ɗin da sauri, ya sanya ba ta lura da abin da ke gabanta ba, ta kuwa yi tuntuɓe, se kawai ta yi baya kamar za ta faɗi. Daidai lokacin da shi kuma ya zo zama a kan gadon se kawai ganinta ya yi za ta zube a ƙasa. Ya yi azamar tareta da hannayensa, se kuwa suka koma kan gadon gaba ɗayansu. Ajiyar zuciya gaba ɗayansu suka sauke. Didi ta lumshe idanunta dan ta riga ta gama saddaƙarwa a ƙasa za ta jita. Miƙewa ta zo za ta yi, ya saka hannu ya maidata, yana juyo da ita sosai ta koma kallansa.

"Kin gani ko jikinki be amince ki yi nisa da ni ba." Ya faɗa yana kafeta da idanunsa. Duk da ta ji abin da ya faɗa ɗin, amma ta basar tana kuma sake yunƙurin tashi ya sake yin baya, wanda hakan ya bata damar sake ƙarasa faɗowa jikinsa gaba ɗaya. Ya saki wani miskilin murmushi yana kallan fuskarta da ta yi rau rau kamar za ta fashe da kuka.

"Don Allah ka sake ni."

"Na ƙi ɗin." Ya faɗa yana kwaikwayon yanda ta yi maganar a shagwaɓe. Ɗauke kai ta yi, dan ta lura so yake ya din ga kunnata. Ba ta ankara ba se ji ta yi ya zame rigar hannun nata. Ya gyara mata zama a jikinsa. Fahimtar abin da yake ƙoƙarin yi ne ya sanyata saurin dafe hannunsa tace

"Don girman Allah ka sake ni.." Ta faɗa tana kallansa da narkakkun idanunta. Sauke numfashi ya yi tuna cewar har yanzu fa shi me laifi ne. Daga dawowa jiya ya kamata ya kama kansa kar ta kwaɓe masa. Hakan ne ya sanya shi faɗin

"Shi kenan.." Ya faɗa yana miƙewa bayan ya saki rigar. Ita kuma ya zamar da ita daga jikinsa ta koma kan gadon. Se a lokacin Didi ta sauke ajiyar zuciya. Se da ta tabbatar hankalinsa ba ya wajen kafin ta saka rigar.

Mamaki ya cigaba da bata, lokacin da ya tasata a gaba ta ci abinci. Abin da be sani ba ita duk kasa sukuni take idan yana wajen. Haka dai ta haƙura saboda yanda ya takura ta tsakuri abincin saboda idanunsa da suka hanata sakat. Sosai ya cigaba da kula da duk wani motsinta. Ko da ƙwaƙwƙwaran motsi ta yi se ya kalleta yace

"Ki na buƙatar wani abu ne?" Ita dai binsa kawai take yi da kallo. Yanda ya chanja cikin ƙanƙanin lokaci se ta ga kamar ba shi ba. Haka duk yanda take ta babbasarwa dan kar ya gane ta haƙura amma se da ta sassauta saboda abin da yake yi. Kwata kwata a ranar be fita ko nan da can ba. Idan ban da masallaci da ke fitar da shi babu inda yake fita, yana nan zaune da ita yana kula da ita. Dan gani yake kamar idan ya yi nisa da ita ze dawo ne ya tarar ta sake barinsa. Tana jinsa ɗazu ma yana waya da Kaseem ɗin da yanzun ta gano ɗan uwansa ne, a kan ba ze samu fita ko ina ba saboda wani ƙwaƙwƙwaran dalili. Ita mamaki yau ɗin nan ya kusan kasheta. Yau ita ce ƙwaƙwƙwaran dalilin da ze hana fita? Lallai Allah me iko.

.. A kwanaki uku da ta yi tare da Bad Man cikin ɗaki ɗaya, se da ta fahimci lallai da gaske ya sauya. Ya zama kamar ba shi ba. Idan ya yi wani abun har mamaki yake bata. Wata irin kulawa yake bata ta musamman. So yake ya fanshe rashin kulawar da be baya ba tun auransu. Komai take ji yake kamar ya maidata ciki. Ita kanta har mamakin irin soyayyar da yake nuna mata take yi. Shi kansa wani sa'in ya kan zauna ya yi ta mamakinsa shi ɗaya, se kuma idan ya tuna abin da ya yi da kuma yanzu abin da ke faruwa, se ya ga kamar Allah ne ya sakawa Didi ta hanyar jarabtarsa da matsanancin sonta, ya yin da ita kuma ta nuna ba ta yinsa. Sosai take lura da duk wani motsinsa. Ta riga ta san idan wani abun ze sha ba kunyarta ze ji ba tun da hakan ta faru a da. Se dai yanzun ma kafin ya fita ana daɗewa. Idan ba abu muhimmi ba ma ba ya matsawa ko nan da can daga cikin ɗakin. Yana nan kusa da ita yana kulawa da ita. Dan ya ɗauki maganar Mommah, idan dai har kulawa na janyo soyayya toh In Sha Allah za ta jawo masa a wajen Didi. Ze zage damtse, ze yi aiki tuƙuru da jiki da hannayensa, ko da Allah ze dube shi ya sauƙaƙa masa ya sanya Didi ta karɓi soyayyarsa ko ze samu su fara gina rayuwarsu.

... Ƙarar da ta ji wayar ta sake yi ne a karo na barkatai shi ne ya sanyata ɗaga kai ta kalli inda wayar ke ajje. Ta ɗan sauke numfashi cike da ƙosawa da yanda ringing ɗin ke katseta daga zarar ta soma karatunta. Ajiye littafin ta yi ta miƙe ta sake kallan ƙofa ko za ta ga shigowarsa, se dai har yanzu shiru. Kawai se ta ƙarasa inda wayar take ta sanya hannu ta ɗauka. Ba tare da ta damu da ganin me kiran ba ta ɗauka ta kara a kunnenta. Wata ƙatuwar ajiyar zuciya aka sauke daga ɗaya ɓangaren. Kafin a kai ga cewa komai Didi tace

"Ba ya kusa.."

"Don Allah.." Muryar wata budurwa ta daki dodon kunnenta. Zame wayar ta yi da nufin ajjeta inda ta ɗauketa tun da dai ta riga ta faɗi abin da za ta faɗa. Daidai lokacin da ya ƙaraso wajen. Tana jin yanda bugun zuciyarta ke ƙaruwa amma ta basar, tana juyowa ta gan shi. Se ta fasa ajiye wayar ba tare da ta kalle shi ba ta miƙa masa, a sanyaye tace

"Ana kiranka.." Binta ya yi da kallo yana ƙoƙarin fahimtar yanayinta. Kafin daga bisani ya mayar da dubansa kan wayar da take miƙa masa. Hannu ya saka ya karɓa kawai, ba tare da ya kalli me kiran ba ya kara a kunnensa.
Chapter 107 · 0% Book details