Sashe 108
A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Salamu Alaika kyakykyawa.." ɗin da aka faɗa cikin wayar shi ne ya sanya shi sauke wayar daga kunnensa cike da mamakin jin muryar mace, se kuma ya kalli me kiran nasa. Kamar yanda ya tsammata kuwa baƙuwar number ce, abin da ya sanya shi jan tsaki kenan yana katse kiran ya jefa wayar inda ta ɗaukota. Duk da yanda ransa ke neman ɓaci, hakan be hana shi juyawa ya kalli Didi ba. Duka idanunta na kan littafin da take karantawa. Se dai duk yanda ta yi ƙoƙarin ɗauke hankalinta daga kansa zuwa kan littafin abin ya citira. Ya kafeta da idanunsa kamar wanda ya soma ganinta a yau. Soma takowa ya yi zuwa inda take, har zuwa lokacin be dena kallanta ba. Gaba ɗaya se ta kasa sukuni saboda yanda take jin idanunsa a kanta. Hakan ne ya sanya ta fara ɗan gyara zama kamar wadda ke shirin tashi daga wajen. Se dai ko kaɗan yanayinta ne chanja ba daga yanda take karatu tun ɗazu.
"Wai ko kaɗan ba kya kishina?" Ya yi tambayar a raunane, kai se ka rantse ba Bad Man ba ne. Tambayar da ta sanyata ɗaga kai ta kalle shi kenan cikin mamaki, dan ita ma se da ta yi tantamar shi ɗin ne ko ba shi ba. Ba ta san amsar da za ta ba shi ba, idan kuma ta cigaba da zama toh tabbas yanayinta ze iya fallasata. Dan haka ta miƙe ba tare da ta kalle shi ba tana ƙoƙarin barin wajen ta ji ya sake faɗin
"Da gaske ne kenan abin da na faɗa? Rashin son nawa har ya kai haka? Wata ta kira ni a waya babu damuwa ko kaɗan kika sanar da ni kika kuma cigaba da harkarki ba tare da kin damu ba.. Shin ni kuwa me na miki? Wace kalar tsana kika min haka? Wane laifi na miki da na cancanci irin wannan tsanar? Wane irin rashin so ne wannan?" Kawai kafe shi ta yi da idanunta ƙirjinta na bugawa, lokaci ɗaya kuma wani irin tausayinsa na kamata. Sosai kalamansa ke cigaba da lugude a cikin kunnuwanta. Zuciyarta na cigaba da bugawa da ƙarfin gaske. Kalamansa sun matuƙar tsoratata, sun kuma sanya ta ji duk wani ƙwarin gwuiwarta na zagwanyewa. Ta rasa yanda za ta yi ne. So take ta sake tabbatarwa da gasken ya dena shan komai ko kuwa dai ya yi haka ne dan ta amince da shi ya koma halinsa na baya. Wannan dalilin ne ya sa har yanzun take nuna tamkar ba ta amince da shi ba. Take cigaba da banzartar da shi, take cigaba da share shi. Take kuma cigaba da wana shi. Se dai ba ta sani ba ashe hakan na dab da yiwa zuciyarsa illah. Ba ta tunanin a yau ɗin za ta iya barin wannan ranar ta wuce ya cigaba da kasancewa da tunanin ba ta ƙaunarsa. Ya cigaba da tunanin tsanarsa ta yi. Idan kuwa har ta bari hakan ta faru toh tabbas da ta kasance butulu, muguwa kuma mara tausayi. Runtse idanunta ta yi tana ƙoƙarin buɗewa ta sake jiyo muryarsa yana faɗin.
"Kin ƙi amince min, kin ƙi amincewa na dena shan komai, kin kuma ƙi amincewa ina ƙaunarki. Har yanzun na gaza jin kalmar ina sonka daga bakinki, kalmar da nake ta jira ta fito daga bakinki. Se dai har yanzu shiru. Na yi tunanin zan iya jurewa tsawon lokaci cigaba da kasancewa da ke ba tare da ki na sona ba. Ashe zuciyata ba ta da wannan juriyar. Ban kuma tashi gasgata hakan ba se yau, a yanzun nan. Saboda haka ina so ki sani duk ranar da aka wayi gari aka ga na mutu, toh zuciyata ce ta buga kuma a dalilin sonki." Ya ƙare yana fidda wani huci wanda yake fitowa tun daga zuciyarsa dake zafi. A zabure ta ɗaga jajayen idanunta ta kalle shi. Zuciyarta na wani irin bugawa. Kallansa take yi kalaman da suka hamma fita daga cikin bakinsa na yi mata amsa kuwwa cikin dodon kunnenta. Cikin ƙanƙanin lokaci bugun zuciyarta ya sauya, jikinta ya ɗauki rawa, hawaye suka shiga saukowa a kan kuncinta. Wani irin jiri ta ji yana neman kayar da ita cike da tsoro fargaba da kuma tsananin tashin hankalin da maganar da ya faɗa ta jefata. Kawai se ta tafi da gudu ta rungume shi, ta saka hannayenta duka biyu ta riƙo wuyansa tana fashewa da kuka.
"Ina sonka.. wallahi ina sonka.. Don Allah ka dena faɗar hakan, ka yafe min don Allah.." Cakk numfashinsa ya tsaya na wucin gadi, wanda hakan ne ya sa gaba ɗaya tunaninsa ma ya dakata. Se da ya yi azamar kai wa numfashinsa wata cafka kafin ya dawo fita da sauri sauri. Ji yake kamar ba gaskiya ba ne abin da kunnensa ke jiyo masa. Tsoro yake yi kar ya je wani daddaɗan mafarki ne ke neman yaudararsa. Se dai haka nan kawai zuciyarsa ta ƙi aminta da mafarki yake yi. Shin da gaske ne abin da ke faruwa? Da gaske ne abin da kunnuwansa ke ji? Wannan rungumar da ta masa, jinta da ya yi a cikin jikinsa shi ne abin da ya sanya shi tabbatar da abin da kunnuwansa ya ji gaskiya ne. Ƙatuwar ajiyar zuciya ya sauke yana gyara tsayuwarsa wani irin farin ciki mara misaltuwa na mamaye ilahirin jikinsa. Cikin azama ya saka duka hannayensa ya rungumeta da ƙarfi kamar wadda za a ƙwacewa ita. Wata irin runguma ya yi mata kamar jaririn da aka haifa yau, wanda muddin aka sake shi ze faɗi ne ƙasa. Idanunsa a lumshe suke, har kuma lokacin zuciyarsa ba ta bar harbawa da ƙarfin gaske ba. Dan kuwa ita da ke jikinsa kowanne bugun zuciyarsa se ta ji shi a jikinta. Tsoron da ta ji ya sake ziyartarta shi ne ya tilasta mata sake ruƙunƙume shi kamar za ta koma cikinsa..
✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO80*
___Daga runguma fa se ga ɗan mutumunku ya soma zarmewa. Dan kuwa yana rungume da ita ya ɗagata gaba ɗaya, be dire ko ina ba se kan gado. Ba ta san shirme ta yi ba se da ta ji sabbin al'amura, ta kuma fuskanci inda Bad Man ɗin ya dosa. Se a lokacin sannan ta soma ƙoƙarin janye jikinta cike da tsoro, kar abin da ta guda rannan yanzu ya faru. Se dai shi kam ya yi nisa ba ya jin kira, gefe guda kuma wutar soyayyar Didi na ƙara masa ƙaimi. Duk da yanda take ji a zuciyarta tana son shi, za kuma ta so abin da yake so tun da har tana son shi, amma yanzu se da ta ji komai na neman sire mata. Ta ji tamkar ma tace ta dena son na shi ko ze rabu da ita. Se dai fa Bad Man yau ɗin be ji wani kira ba, dan kuwa toshe kunnensa ma ya yi, kar a sake maimaita abin da ya faru rannan. Kar kuma tausayin abar ƙaunar ta shi ya hana shi maidata tasa gaba ɗayanta. Hakan ne kuwa ya faru, dan yau ɗin se da Bad Man ya maida Didi ta zama tasa halak malak.
Wata irin soyayyar Didin ke ratsa duk wata gaɓa ta jikinsa, ya rungumeta cikin jikinsa yana ji tamkar ya maidata ciki. Ji yake zuciyarsa na azalzalarsa kamar me, be san me ze ce ya ji sauƙi ba. Kawai se ya lumshe idanunsa yana sake rungumeta. Yana jin yanda numfashinsu ke fita kusan a tare. Daidai lokacin da tulin hawayen da suka daɗe da taruwa cikin idanunta suka sauka a kan ƙirjinsa. Ya runtse idanunsa yana jin yanda zuciyarsa ta harba. A hankali ya ɗan gyara zamansa, ita ma cikin takatsantsan ya gyara mata tata kwanciyar a jikinsa.
"Yi haƙuri my dear.. Kukan nan na min illa a zuciya." Ya faɗa yana ɗan runtse idanunsa, dan tabbas yana nufin abin da ya faɗa ne. Ba ta san me za tace ba, ba kuma ta san ya za ta yi ba. Ba ita take barin hawayen su zuba ba, da kansu kawai suke zubowa, saboda yanda take jin jikinta. Ita da ta san haka ne ma ba za ta taɓa sanar da shi tana son shi ba. Da ta san haka ne ba za ta taɓa rungumarsa ba. Ga shi nan daga runguma an jawo mata jangwangwana, dan ba ta ji ko iya motsa jikinta za ta iya yi. A hankali kuma se ya soma zameta daga jikinsa, ta yi azamar riƙe shi sosai tana runtse idanunta. Ya fesar da iska daga bakinsa yana faɗin
"Ohh sorry babe." Ya faɗa har jikinsa yana jin wani irin tausayinta na sake ratsa shi. Se da ya sauke numfashi yana tunanin ta ina ze fara, kafin daga bisani ya yi amfani da hannunsa wajen ɗagata gaba ɗaya ya kwantar da ita gefe a hankali, kana ya miƙe. Se da ya ranƙwafo ya manna mata kiss a goshi yana kallan jajayen idanunta da yanzu suke a rufe. Ya sake fesar da numfashi a wahalce yana cigaba da kallanta, kafin ya tashi ya shige toilet. Kai tsaye wanka ya yi, ya kwashi mintuna masu dama kafin ya fito, bayan ya cika bathtub da ruwa me ɗumi. Fitowa ya yi ya ƙarasa ya ɗauki riga da wando marasa nauyi ya saka. Ƙarasawa ya yi inda ya bar Didi, kamar yanda ya barta yanzun ma a nan ya sameta. Ya ɗan yamutsa fuska yana sake jin tausayinta. Ƙarasawa ya yi a nutse, be ce da ita komai ba ya saka hannu da niyyar ɗaukarta. Ta buɗe manyan brown eyes ɗinta da suka ɗan yi ciki ta kalle shi, se ta maƙe kafaɗa da sauri tana kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka. Da sauri ya janye hannunsa, ya kai kan kunnensa ya riƙe da duka hannayensa. Ya ƙanƙantar da idanunsa kafin yace
"A yi min afuwa Sweerie.. Na san na yi laifi, amma a yafe min Uhmm?" Ya faɗa a marairaice. Juyar da kanta ta yi tana ƙoƙarin rufe idanunta ya sake faɗin
"Don Allah fa na ce.." Ya faɗa kamar wani yaron goye. Sake maƙe kafaɗar dai ta yi ba tare da ta juyo ba.