Sashe 34
A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Toh.." ya faɗa yana sake kauda kansa gudun haɗa ido da Daddyn. Ɗan tsayawa Daddy ya sake yi na tsawon sakanni kafin ya taka ya fice daga ɗakin. Se da Daddyn ya fita sannan ya miƙe da sauri ya ƙarasa ya kulle ƙofar ɗakin kafin ya dawo cikin ɗakin ya soma duba kan kujerar da yana da tabbacin a nan ya barsu kafin bacci ya kwashe shi. Se dai me? Sam babu ko da bottle 1 ne a wajen. Jefar da kujerar ya yi gefe da hannunsa, cike da fatan ganinsu a ƙasan kujerar. Se dai nan ɗin ma babu su babu alamarsu. Hannunsa ya cusa a cikin sumar kansa yana fesar da iska daga cikin bakinsa.
"Kenan Daddy ya gani?" Ya tambayi kansa cikin sarewa. Yamutsa sumar kansa ya yi yana neman waje ya zauna cikin rashin sanin abin yi. Numfashi ya sake ajjewa yana sake tuna idan dai har Daddyn ya gani me ze faru? Ko shi ya sa yace ya zo yana son ganinsa? Ya aka yi ya yi wannan saken? Miƙewa ya sake yi ya shiga zagaye ɗakin, se kuma ya sake komawa ya zauna har lokacin hannunsa ɗaya na cikin sumar kansa. Gaba ɗaya ransa a ɓace yake, ya rasa ma abin da ya kamata ya yi. Sam ba ze wani iya zuwa wajen Daddyn ba anjima, dan be san da wane ido ze kalle shi ba, and idan ya titse shi kuma ya gano ya daɗe yana kwalɓewa ba tare da saninsa ba, wane hali Daddyn ze shiga? Ya san Daddyn da saka abu a ransa, ya kuma san shi da fushi da zafin zuciya, sam be san yanda za ta kaya tsakaninsu ba. Ya ja tsaki a karo na babu adadi cike da haushin kansa da ya kasa tsayawa ya kulle ɗakin ko kuma ya kwashe kwalaben kafin Daddyn ya gani. Miƙewa ya yi ya shige toilet dan watsa ruwa, saboda baccin da ya fice masa a rai gaba ɗaya. Kamar yadda ya saba ɗaukar mintuna masu yawa idan ya shiga wankan, yanzun ma haka ya ɗauka, ya fito ya shirya cikin ƙananan kaya har lokacin ransa be koma da daɗi ba. Kai tsaye inda ta saba ajje masa Coffee ɗin ya nufa, kamar yanda ya tsammata ta riga ta ajje, dan haka ɗauka kawai ya yi ya soma sha a tsayen da yake, dan yanzu ba shi da sukunin zama. A hankali yake sha yana cigaba da tunanin yanda za su ƙare da Daddy. Har ya gama sha be gama yanke yanda za su yi ba, ya ajje cup ɗin yana girgiza kai lokaci ɗaya yana ɗan lumshe idanunsa, se kawai ya koma kan gadon ya kwanta ba tare da ya fita daga ɗakin ba.
.. A ɓangaren Didi kuwa babu ɓata lokaci ta je ta zubar da bottles ɗin a bayan part ɗin nasu. Duk da yanda tsoro ke ƙoƙarin mamayeta amma hakan be hanata jefar da su ba sannan ta koma cikin ɗakin. Kai tsaye kan gado ta nufa ta zauna ta cure waje ɗaya tana jin wani kuka na taho mata. Tausayin kanta da rayuwarta na kamata. Anya kuwa Abba ya san wanda ya aura mata? Shi ne tambayar da ta tsaya mata a cikin kwanyarta. Ta cigaba da kukanta kawai ko zata samu ta ji sauƙin abin da take ji cikin zuciyarta. Se dai memakon ta ji haushin Bad Man ɗin ya kamata, se ta ji wani irin tausayinsa ya mamaye zuciyarta. Me ya sa yake shaye_shaye? Me ya sa ya fara tun farko? Shin ba yana da iyaye uwa da uba ba? Amma ya aka yi yake shaye_shaye? Shin basu sani ba ne ko kuma sun sani, saboda wasarere da kuma dukiyar da Allah ya basu shi ya sa suka ƙyale shi ya yi abin da ya ga dama? Tambayoyi rututu su ne suke ta yawo a cikin kwanyarta, se dai ta rasa wanda ze bata amsa. Hakan ne ya sanya ta samawa kwanyarta hutu ta haƙura da jerowa kanta tambayoyin da babu me amsa mata. Kwanciya kawai ta yi cikin rashin sanin abin yi. Se dai duk wani motsi da za ta yi se ta tuna da abin da ta gani, haka nan kawai ta ji tana so ta san dalilin da ya sanya yake shaye_shaye. Ta kuma ji tana so ta yi wani abun da ze sanya ya dena yi ko da kuwa hakan na nufin barinta gidan ne. Gaba ɗaya ranar wuni ta yi ba ta da sukuni, hankalinta gaba ɗaya ya ƙi kwanciya, se bugun zuciya da take ta ji, da kuma hawayen da yau ɗin kamar arharsu take yi. Dan kuwa motsi kaɗan se ta ji ƙwalla kawai ta cika mata idanu.
.. Fitowarta kenan daga cikin ɗakin Baba Atine ta shigo cikin sashen. Da murmushi a kan fuskarta ta kalleta tace
"Afrah.." Maida mata da murmushin ita ma ta yi tana gaisheta cike da ladabi. Amsawa ta yi cikin kulawa sannan ta ɗora da
"Ba dai yanzu kika tashi ba?" Se da ta ɗan cuno baki sannan tace
"Bacci ne ya ɗauke ni fa.."
"Toh ya yi kyau.. Hajiya Sa'adah tace gobe idan Allah ya kai mu ki shirya za a aiko a raka ki sashen Hajiya Salma." Rashin gane wace ce Hajiya Salman shi ne ya sanyata amsawa da
"Toh Allah ya kai mu." Ba tare da ta ji komai ba. Baba Atine tace
"Je ki zauna bari na zo na ɗora miki abin da za ki ci." Buɗe idanu Didi ta yi tace
"Kaiii. a'ah Baba Atine ki bar shi zan ɗora da kaina." Girgiza kai Baba Atine ta yi tace
"A'ah wallahi 'yata ki je ki zauna ki huta.." Sake girgiza kai ta yi ta sake nuna mata ta gode. Da dai ta fahimci ba barin nata za ta yi ba, se ta yi murmushi tana sake yabawa da hankalin Didin ta mata sallama ta fice daga ɗakin. Se a lokacin sannan Didin ta wuce kitchen kai tsaye ta ɗora tukunya. Tana tsaye tana ɓare maggi tana cigaba da tunani kamar yanda ta saba. Sam ba ta ji shigowar mutum ba se lokacin da ta ji muryarsa a shaƙe yace
"Kee!!" Ya faɗa a kaurare. Ba ta san lokacin da ta jefar da maggin ba tana juyawa ta kalli inda ta ji maganar. Yana tsaye jikin locker hannayensa duka biyun harɗe a ƙirjinsa. Fuskar nan kamar ko yaushe babu annuri. Ganinsa da ta yi babu shiri ya sanya ta ƙoƙarin ficewa daga kitchen ɗin da sauri. Taku ɗaya ya yi ya saka hannunsa ya riƙo tsintsiyar hannunta dake cikin hijab ya dawo da ita baya jikin locker. Idanunsa ya zuba mata a kan fuskarta ganin yanda ta yi saurin rufe idanunta a matuƙar tsorace
"Buɗe idanun ki." Ya yi maganar cikin bayar da umarni. Girgiza kai ta yi daidai lokacin da kuka ya taho mata ta buɗe baki da ƙyar tace
"Don Allah ka yi haƙuri.."
"Ohh ashe kina sane.. Buɗe idanun ki nace.." ya yi maganar a tsawace se dai ba cikin ɗaga murya ba. Babu shiri ta buɗe idanun nata da suka gama cika taff da ƙwalla. Lumsassun idanunsa suka shiga cikin brown oily eyes ɗinta dake wani sheƙi musamman yanda ƙwalla ta cika su. Ji take kamar ta janye idanunta saboda yanda ta ji bugun zuciyarta na daɗuwa, waɗannan idanun nasa masu kama da na en iska sun mata mugun nauyi cikin nata. Se dai yanda ya tsatstsareta da nasa idanun ya sa ta kasa yin hakan, se barin hawayen ta yi suka soma saukowa zuwa kan kuncinta.
"Me ya hana ki kawo Coffee yau?" Ya yi maganar yana sake riƙe hannunta sosai dan mugunta. Ƙara ta saki saboda yanda ta ji kamar hannunta ze tsinke. Ita wallahi gaba ɗaya ma ta manta yau ɗin nan, wani irin bacci ne ya kwasheta, kuma kafin ta tashi ta manta. Da ta tashi kuma yunwa ce ta tasota ya sa ta sake mantawa gaba ɗaya.
"Open ur mouth and talk.." Ya faɗa a fusace dan ya fahimci kamar iskanci take ji da shi.
"Wallahi mantawa na yi." Ta faɗa muryarta na rawa. Jinjina kai ya yi yana faɗin
"Ohhh.." Ya ɗan yi shiru se kuma ya saki hannun nata da ya riƙe. Gaba ɗaya ta yi ƙasa ta zube a wajen, duk da yanda ya ji ta faɗi ƙasa hakan be sanya shi ƙoƙarin riƙota ba. Se ma watsa mata kallo da ya yi yace yana murza yatsun hannunsa
"Ki sake mantawa kin ji?" Ya ƙare yana wani murmushi da yafi kama da na mugunta. Be sake cewa komai ba ya fice daga kitchen ɗin a ransa yana jinjina taurin kai irin na yarinyar nan. Amma ze koya mata hankalin da ba za ta so ta sake cewa ta manta ba ta masa abin da ya sakata ba.
Riƙe ƙugunta ta yi bayan ya fita daga kitchen ɗin tana fashewa da kuka. Duk da ta ji abin da yace ba tace komai ba saboda haushin abin da ya mata. Se da ya fita sannan ta bishi da kallo tana faɗin a kan laɓɓanta
"Mugu kawai.." ta yi maganar tana miƙewa tsaye saboda motsin girkin dake kan wuta da ta ji.
Ta yadda za ta cigaba da kai masa Coffee ɗin, se dai wallahi ze ga ɓarna a kan kayansa. Se ta yi amfani da wannan damar ta hana shi sakat dan kuwa ta ci alwashin ko sau nawa za ta ga wani abun da ya danganci shaye_shaye a cikin ɗakin nasa se ta ɗauka ta zubar se dai ko me ze yi ya yi.