← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 122

Sashe 61

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Na haɗaka da Allah fa.." ta faɗa kamar ba Lulu ba. Saboda yanda hatta muryarta ta koma ta waɗanda za a tausayawa. Se a lokacin ya saketa yana sake riƙe dariyarsa ya sauka daga kan gadon. Yana sakin nata ta yi saurin komawa gefe ta takure waje ɗaya kamar me jin sanyi. Duk wani tsoron Gwanin da ta ji a ranar nan ya sake dawo mata sabo. Amma duk da haka da ta ga ya saketan se da ta saci kallansa ta jefa masa harara tana sake jan bargo ta lulluɓe ilahirin jikinta. Sarai yana lura da duk wani abu da take yi. Shi dai har yanzu ya kasa dena dariya saboda tsoron nan nata ya ba shi dariya ainun.

... Da sallama Baba Atine ta shigo ɗakin. Didi ta amsa sallamar da murmushi kan fuskarta.

"Sannu da zuwa Baba Atine.." Didi ta faɗa.

"Yawwah ɗiyata.." Ta yi maganar tana neman waje ta zauna. Suka gaisa cike da sabo.

"Ina kwana..?" Little ya faɗa yana kallan Baba Atinen. Hannu Baba Atine ta saka ta janyo Little ɗin da murmushi kan fuskarta tace

"Lafiya ƙalau yarona.. ka na lafiya..?"

"Ehh.." ya faɗa yana gyara zamansa a kan cinyarta.

"Kin shirya ne 'Yata?" Baba Atine ta tambaya bayan ta maida dubanta kan Didi. Ɗan ɓata fuska Didi ta yi sannan tace

"Ki yi haƙuri Baba.. kin ga yanzu nake so na shirya." Murmushi Baba Atine ta yi kana tace

"Ai babu koma 'yata. Bari kawai na ɗauki Areef mu je sashen Hajiya. Idan kin gama se ki iskemu a can."

"Tohm shi kenan.." Didi ta faɗa. Miƙewa Baba Atine ta yi hannunta riƙe da na Little.

"Didi se mun dawo." Little ya faɗa yana ɗaga mata hannu bakinsa kamar ze faɗo dan dariya. Duk saboda za a fita.

"Toh Little.." ta ba shi amsa ita ma tana ɗaga masa hannu. Daga haka Baba Atine ta ja hannun Little ɗin suka fice daga ɗakin. Hango Bad Man da ya yi kafin su fice daga ɗakin ya sanya shi sakin hannun Baba Atine ya tafi da gudu wajen shi. Ita sam ba ma ta lura da Bad Man ɗin ba. Dan haka da sauri tace

"Areef!!" Dakatawa ya yi daga inda yake. Ya ɗaga idanunsa ya sauke su kan Baba Atine da yake da tabbacin ita ce ta kira sunan shi. Daidai lokacin kuma da Little ya riƙo hannunsa yana faɗin

"Uncle.." Se a lokacin Baba Atine ta lura da shi. Cike da girmamawa ta ƙaraso kanta a ƙasa tace

"Barka da wannan lokaci Yallaɓai.."

"Barka.." Ya amsa a taƙaice. Se ta maida dubanta kan Little tace

"Taho mu tafi.." Maƙe kafaɗa ya yi yana wani cuno baki lokaci ɗaya kuma yana sake riƙe hannun Bad Man ɗin da kyau. Sauke idanunsa Bad Man ya yi a kansa yace

"Me ye sunanka?"

"Areef.." Murmushi ne ya wanzu a kan fuskarsa jin da ya yi sunansu iri ɗaya. Karon farko kuma da ya ji yaron ya burge shi. Se ya saka hannunsa ya riƙo shi, daidai lokacin da ya maida dubansa kan Baba Atine yace

"Ki je kawai.." Babu musu ta amsa da

"Toh Rankayadaɗe.." Daga haka ta fice daga ɗakin. Shi ma ficewa ya yi daga ɗakin har lokacin hannunsa riƙe da na Little. Kai tsaye parking space ya wuce inda yake da tabbacin Kaseem na jiransa. Aikuwa yana tsaye hannunsa sarƙe a ƙirjinsa yana jiran fitowar Bad Man ɗin. Tun daga nesa yake sake buɗe idanunsa yana kallan yaron da ke hannun Bad Man. Har dai zuwa lokacin da suka kusa ƙarasowa.

"Laaa!!" Little ya faɗa yana kallan Kaseem bayan ya dakata. Se kuma ya ƙarasa da gudu ya rungume shi. Tabbatar da lallai wannan ɗin Little ne ya sanya Kaseem saka hannu ya rungume shi. Kafin ya buɗe baki yace

"Areef.. Ya na ganka a nan?"

"Wajen Didi na zo.." Ya faɗa bayan ya ɗago yana kallan Kaseem ɗin.

"Didi kuma?" Kaseem ya faɗa cike da mamaki. Cike da mamakin dai Bad Man ke kallansu. Se dai hakan be nuna ba a kan fuskarsa. Tambayar da ke ta masa lugude cikin kai ita ce ta sanya shi gyara tsayuwa yace yana kallan Kaseem

"Da ma ka sansu ne?" Se da ya kalli Bad Man ɗin sannan ya soma faɗin

"Ehh.. na sansu sosai.. Musamman ma yayar tasa. Dan mun yi soyayya da ita a da, amma Allah be yi zan aureta ba. Se dai kuma a yanda na sani yanzu haka ta yi aure shi ya sa ban fahimci maganar Areef ba." Harɗe hannayensa a ƙirji Bad Man ya yi yana kallan Kaseem kamar me son gano wani abu daga kan fuskar tasa. Kaseem na shirin sake yin magana Bad Man ya katse shi da faɗin

"Ni ne mijin nata.." Ya faɗa cikin basarwa. Ɗaga ido Kaseem ya yi ya kalli Bad Man irin kallan mara hankalin nan. Duk da be san Bad Man ɗin na shaye shaye ba amma tabbas yau yana da yaƙinin ya sha wani abu. Ta yaya ma shi ɗin ze kasance mijin Afrah? Ta yaya ma hakan za ta faru? Cigaba da masa kallan tuhumar nan ya yi yana jira ya sake jin wani abu ya fito daga bakinsa. Se dai shi ma ɗin kawai kallansa yake yi ba tare da yace uffan ba. Daidai nan Didi ta fito daga sashensu sanye cikin doguwar riga da hijab ɗinta madaidaici. Ta yi wani shahararren kyau kamar wadda ta kwashe awanni tana shiryawa. Kamar wanda aka ce ya ɗaga kai yana ɗagawa kuwa idanunsa suka sauka a kan Didin da ke cigaba da takawa. Haka nan kawai ya ji zuciyarsa ta buga. "Ka da fa a ce da gaske Bad Man ɗin yake masa?" Ya tambayi kansa cike da fargaba. Haka nan kawai ta ji ido na yawo a kanta. Duk se ta ji ta tsargu, dan haka ta ɗaga kanta dan ganin me kallan nata. Cikin sakannin da basu wuce 5 ba suka yi 4 eyes ita da Kaseem. Babu shiri ta dakata a inda take zuciyarta na soma gudu. Kawai se aka shiga kallan kallo tsakaninsu, kowa da abin da yake saƙawa a ransa..

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO56*

___ A hankali Bad Man ya ɗaga idanunsa ya kalli inda Kaseem ɗin ke kallo, dan shi sam be san da wanzuwar Didi a wajen ba. Se kuwa idanunsa suka sauka a kan Didi wadda zuwa yanzun ta sauke idanunta daga kan Kaseem ɗin. Ya yin da shi kam Kaseem ko gezau har zuwa lokacin idanunsa na kan Didin. Wato lokacin da Bad Man ya maido da dubansa kan Kaseem. Haka nan kawai ya ji ransa ya sosu, ba kuma dan komai ba se dan yanda ta kasance matar aure. Duk da shi dai ya san ba sonta yake yi ba, amma kuma abin da Kaseem ɗin yake yi sam be dace ba. Ya kuma zama dole ya taka masa burki tun kafin ya ƙarasa fusata shi. Ya ɗan runtse idanunsa kafin ya buɗe su. Cikin takun nan nasa ya soma takawa zuwa inda Didi take. Ba tare da ta lura da hakan ba. Se kawai tsintar shi ta yi dab da ita kamar wanda ke shirin rungumeta. Cike da fargaba ta yi saurin yin baya a ranta tana jin haushin kanta da ta tsaya kallan Kaseem ɗin. Yanzu idan ya ganta da wane ido za ta kalle shi? Duk da ta san be ɗauketa matsayin matarsa ba amma ko babu komai hakan da ta yi be dace ba. Sake matsawa ya yi kusa da itan, daidai lokacin da ƙirjinta ya wani irin bugawa ta ji ina ma ƙasa ta tsage kawai ta shige da dai wannan mutumin yace ze hukuntata. Ba ta yi tsammani ba se jin tattausan hannunsa ta yi a tsintsiyar hannunta ya riƙe da ƙarfin gaske. Ba ta san lokacin da ta ɗaga kai ta kalle shi ba. Ya watsa mata wani kallo da ba ta taɓa ganin ya yi kalarsa ba. Duk se ta sake jin jikinta ya yi mugun sanyi har ba ta san lokacin da ta tara ƙwalla cikin idanunta ba. Ba tare da yace komai ba ya sake riƙe hannun gam yanda ya san za ta ji zafi. Aikuwa se da ta runtse idanunta tana ji kamar ta fashe da kuka. Se ya soma takawa zuwa sashensu. Ba tare da ya sake kallan inda Kaseem ke tsaye ba suka shige cikin ɗakin. Se a lokacin ya saki hannun nata sannan ya juya da niyyar ficewa. Se kuma ya juyo ya kalleta kamar wanda aka wa dole yace

"Idan na sake ganin ƙafarki a wajen sashen nan za ki ga abin da zan miki.." Ya ƙare yana yin ƙwafa. Be jira tace komai ba ya fice dan zuwa ya ji da Kaseem. Hannunta ta riƙe tana ji kamar har yanzu be saketa ba saboda zafi. Ta kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka. Duk haushin kanta ya ƙi sakinta. Tuna abin da ya faɗa ne ya sanyata wucewa ɗakinta ba tare da sake tunawa da inda za ta je ba.
Chapter 61 · 0% Book details