← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 122

Sashe 45

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

... Cikin matuƙar farin ciki take kallan ko ina na cikin ɗakin lokacin da ta sake ƙyalƙyale shi, yanda ya yi matuƙar kyau kamar ba shi ba. Da ma kuma ga shi en Nepa sun bar wuta se ya kasance ɗakin ya haskaka ga wani ƙamshin furniture wanda ya haɗe da ƙamshin turare ɗan tsinke da Ummeey ta ba ta ta saka cikin ɗakin suke ta tashi gwanin daɗi. Murmushi kawai take saki saboda babu ƙarya ɗakin ya mata. Ta yi iya bakin ƙoƙarinta dan kar ta tuna da inda take. Se dai hakan ya citira. Dan kuwa cikin lokaci ƙanƙani zuciyarta ta soma kitsa mata gidan wanda take ciki har take farin ciki irin wannan. Cikin lokaci ƙanƙani gaba ɗaya annurin dake kan fuskarta ya ɗauke. Ta lumshe idanunta tana jin wata ƙwalla na taho mata. Se kawai ta sanya hannu ta ɗauketa tunawa da ta yi ba ta da wata mafita. Dan haka gwara ta bari kawai ta yi farin cikinta. Dan babu ƙarya kayan nan da Abba ya saka aka kawo mata ta mugun jin daɗinsu. Kuma za ta so ta samu damar yi masa godiya shi da Ammi. Kawai se ta sake yin murmushi lokacin da idanunta suka sake sauka kan gadon da ta gama gyarawa tass tass kamar ba hannu ne ya gyara ba. Ƙarasawa ta yi ta ɗauki zani da hijab ta shige banɗaki dan yin wanka. Ba ta wani ɗauki lokaci ba ta fito se ƙamshin sabulun Gwani me daɗi take yi. Kamar yanda ta saba yanzun ma a cikin banɗakin ta shirya duk da ba ya ɗakin sannan ta fito. Kai tsaye kan dadduma ta wuce ta yi sallahr isha'i da ba ta yi ba sannan ta yi addu'ointa kana ta miƙe dan komawa ta kwanta kan lafiyayyen gadonta da ta gama tamawa. Dan babu wai yau ɗin ta san za ta baje ta yi bacci cikin kwanciyar hankali. Se dai me?? Tana ida ninke daddumar ta juya da niyyar isa kan gadon ta kwanta se ganin shi ta yi zaune kan gadon yana buɗe Al_qur'an, da alama karatu ze yi. Wani irin ɓacin rai ta ji ya taso mata saboda sam ba ta yi tsammanin ganinsa a irin wannan lokacin ba. Se dai kuma se ta yi saurin kwaɓar kanta tuna kirkinsa gareta. Duk da haka dai ji take kamar ta buɗe baki tace ya tasar mata daga kan gado. Ba dan mutuncin da ya mata ba, ya ƙi sanar da Abba abin da ya faru, da kuma ɓoyewa kowa ma abin da ya faru ba da abin da ze fara fitowa daga bakinta shi ne ya tasar mata daga kan katifa tun da dai tata ce ba tasa ba. Se dai tun da ta san ba za ta iya faɗa ba a yanzu kam ya sanyata komawa gefen gadon ta nemi waje ta shimfiɗa daddumar ta zauna dan jiransa ya gama karatun ya koma inda yake kwana. Tun da dai tasa katifar ma yake bar mata ta kwana ballantana tata. Ba tare da ta kalle shi ba ta yi zamanta tana jiransa. Se dai jefi_jefi ta kan ɗaga kai ya kalle shi ko ya idar? Se ta ga ba haka ba. Sarai ya ganta, ya kuma fahimci abin da take jira amma ya basar ya cigaba da karatunsa. Shi da ya yi niyyar karanta izu ɗaya se ga shi har ya shiga izu na uku har kuma lokacin tana zaune. Zuwa lokacin har wani bacci bacci ya fara fuzgarta, amma har lokacin ba shi da niyyar tashi ya bata waje. Da dai ta fahimci be san zarau ba se kawai ta shiga ɓata rai tana wani ciccin magani gami hararar gefe, tun da dai ta san yanzu ba za ta iya masa tsiwar tata ba. Se da ya idar da karatun sannan ya buɗe wani littafi na addini ya shiga karantawa. Shi ne daidai lokacin da ya saci kallanta lokacin da take ta ciccin magani tana wani tura baki ita a lallai dole ya ɗaga mata katifa. Murmushi kawai ya yi dan shi dariya ma ta ba shi. Hakan kuma da take yi shi ke sanya shi ƙin tashi ya bata wajen. Ba ta ƙara minti 20 a haka ba wani nannauyan bacci ya saceta a inda take zaune. Se da ya gama muraja'ar inda ze yi sannan ya sake dubanta. Kanta na jingine da bangon bayanta tana bacci kamar ba ta da wata damuwa a rayuwarta. Numfashi take saukewa a hankali wanda hakan ze alamta maka yanda baccin nata ya yi nisa yake kuma mata daɗi. Ya ɗan furzar da iska yana ɗauke kansa daga kallanta. Har ya buɗe wani littafin da niyyar cigaba da karantawa se idanunsa suka sake kaiwa inda take zaune tana baccin. Ajje littafin ya yi a kan gadon ya miƙe a nutse zuwa inda take ɗin. Tsayawa ya yi na tsawon minti 2 yana kallan wani wajen kamar me tunani. Se kuma ya dawo da dubansa kanta still dai kamar me tunanin. Ranƙwafawa ya yi daidai lokacin da ya kai dukka hannayensa biyu inda take. Se kuma ya dakatar da hannun yana maida idanunsa kansu kamar me son ganin wani abu. Se kawai ya sake fesar da iska daga bakinsa kafin ya sake maida fuskarsa kanta. Babu ɓata lokaci ya saka hannayen nasa duka biyun ya ɗagata a hankali cike da fatan ka da ta farka. Dan ya san idan ta farka ɗin rigima ce za ta biyo baya. Shi kuma ya ji daɗin yanda ta koma a kwanakin nan kamar ba ita ba, kamar wadda aka chanjata. Cikin takatsantsan ya kwantar da ita a kan gadon bayan shi ma ya zauna inda ya tashi. Fahimtar da ya yi baccin nata ya yi nisa ne ya sanya shi saka hannu ya maido da kanta kan cinyarsa a nutse kuma cikin kula ya zame hijab ɗin dake jikinta har ƙasa kamar wadda za ta fita. Tana sanye cikin wata doguwar riga mara nauyi. Hannunta ba shi da tsayi, hakan ne ya baiwa fararen maidaidaitan hannayenta damar fitowa tun daga sama har ƙasa. Gashin kanta dake a tsefe yana ɗaure cikin wani ƙaramin ribbon. Se dai saboda yawansa da kuma tsayinsa kuma kasancewar babu ɗan kwali a kanta ya sanya yana ida cire mata hijab ɗin kwantaccen gashin kan nata ya samu masauki a kan cinyarsa. Be lura da hakan ba se shirin zameta da ya soma yi zuwa kan gadon. Cikin magagin bacci ta sanya tattausan hannunta ta gyarawa nasa hannun zama a kan cinyarsa gami da ɗora kanta a kai ta cigaba da baccinta. Binta ya yi da kallo kamar ba shi ba. Yanda take baccin ba ƙaramin wani shahararren kyau ta yi ba. Kamar wanda ake umarta se ya ji ya kaasa ɗauke idanunsa daga kan fuskar tata. Tsawon minti 1 yana kallan fuskar tata kafin zuciyarsa ta tunasar da shi abin da yake yi. Ya ɗan ja ƙaramin tsaki yana ɗauke kansa lokaci ɗaya kuma yana sauke wata ajiyar zuciya lokacin da bugun zuciyarsa ya sauya. Ɗayan hannun nasa ya kai saitin zuciyarsa cike da mamakin abin da ya sauya shi haka, har lokacin idanunsa a lumshe. Se da ya ji numfashin nasa ya saitu kamin ya buɗe idanun nasa. Ba tare da ya kalleta ba ya ja littafin ya soma karantawa. Se dai yanda take yawan gyara kwanciyarta tana kuma sake riƙe hannunsa ba tare da sanin abin da take riƙewa ba ya sanya yake ɗan dakatawa da karatun. Be dai bari wani abun ya yi tasiri a kansa ba ya cigaba da karatunsa. Se da ya ida littafin sannan ya rufe baki ɗaya ya ajje su gefe dan babu damar miƙewa saboda yanda ta yi kane_kane a kan cinyarsa. Cigaba da zama ya yi bayan gama karatun kamar me tunani. Can ya ɗan shafa buɗaɗɗiyar kyakkyawar sumar kansa kafin ya lumshe idanunsa cike da fatan bacci ya ɗauke shi saboda yanda yake jin jikinsa gaba ɗaya a sanyaye. Ko minti 2 be yi da rufe idanun nasa ba ya soma jin mutsu mutsunta ya ƙaru fiye da ɗazun. Se ya yi saurin buɗe idanun nasa a kanta dan ganin dalilin hakan. Daidai lokacin da ta ida buɗe idanunta se kuwa suka sauka a cikin na Gwani da shi ma ya sauke nasa idanun a kanta. Saboda baccin da ke kanta ba ma ta fahimci waye ba. Cikin sauri ta miƙe zaune dirshan a kan gadon tana maida idanunta kan hannunta da ta ji alamar abu a ciki. Tana kai idanunta dake cike da bacci kan hannun nata se ganin wani hannun ta yi a ciki. Cikin matuƙar gigicewa ta runtse idanunta da har yanzun bacci be sake su ba ta jefar da hannun a matuƙar razane, ta kuma soma ƙoƙarin miƙewa dan dira daga kan gadon. Fahimtar abin da ze biyo baya tun da ta yi wannan tsoratar ya sanya shi saurin saka hannunsa ya janyota. Cikin en sakanni se ga ta a jikinsa. Ta buɗe baki za ta yi ƙarar da ta saba yinta, babu zato babu tsammani se jin tattausan laɓɓansa ta yi a kan nata red lips ɗin...

MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO48*
Chapter 45 · 0% Book details