← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 122

Sashe 101

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi ganinta ma gaba ɗaya ya sa ya manta abubuwan da ya ajiye. Duk kuma da zubar da abin da ta yi shi kam wannan ba damuwarsa ba ce. Damuwarsa ɗaya a ce duk sun yarda da ya tuba ya kuma yi laushi. Matsawa ya yi kusa da ita ya saka hannu ya riƙo hannunta cikin nasa. Ita dai kallansa kawai take yi jikinta na cigaba da rawa, idanunta na soma tara ƙwalla.

"Me ya sa kike min haka Afrah? Me ya sa ba za ki tausaya min ba? Me ya sa ba za ki ji ƙaina ba? Ki kalle ni ki ce kin yafe min kuma kin amince da soyayyata ba? Na faɗa miki wallahi ina sonki. Ina sonki, ina sonki. Ya kike so na yi da zuciyata Uhmm?" Ya ƙare maganar gwanin ban tausayi. Duk da yanda zuciyarta ke rawa hakan be hanata fuzge hannunta ba. Idanunta sun cika taff da ƙwalla. Ko ba dan abin da Mommah tace mata ba, ita ma kanta za ta so a ce mijinta ya zama kintsatstse shiryayye wanda za ta yi alfahari da shi. Cikin ƙarfin hali da kuma dakewar zuciya tace

"Ka ba ni mamaki.. Ashe har yanzu ba ka dena ba? Ashe har yanzu ka na cigaba da shan wannan abar? Ashe ka yaudare mu ne da kalaman bakinka? Abin takaicin ma har ka saka Mommah ta yarda da kai, ta amince da kai? Har kuma ta tabbatar min da ka dena ɗin? Se ga shi ka watsa mata ƙasa a ido? Ka cigaba da abin da ka ga dama? Shin wai ka manta wace ce uwa? Ba ka san wace ce uwa ba ne? Ko kuwa ba ka tsoron haɗuwarka da Allah? Toh bari ka ji har abada ba zan taɓa amincewa da kai ba, ba kuma zan taɓa sonka ba har se ka dena shaye-shaye." Daga haka ta juya a guje ta fice daga ɗakin. Shiru ya yi na tsawon minti 1 ba tare da ya motsa daga inda yake ba. Kawai abubuwan da ta faɗa ne ke ta dawo masa a cikin kwanya. So ya yi ya gama fahimtar abin da take nufi ya bata amsa. Se dai tun kafin ma ya gama fahimta har ya fice. Cikin ƙanƙanin lokaci kansa ya shiga sara masa kamar ze rabe gida biyu. Jikinsa har wani rawa yake yi tamkar wanda zazzaɓi ke shirin rufewa. A hankali ya juya ya kalli inda ya ajje bottles ɗin nan, se a lokacin ya gane duk dalilan Didin na waɗannan maganganun nata da ya ji su can can cikin zuciyarsa. A hankali ya kai hannunsa ya kama kansa lokaci ɗaya yana runtse idanunsa. Wani irin zafi zuciyarsa take masa, kansa na cigaba da sarawa. Kawai se ya koma ya zube kan gado ya runtse idanunsa da suka yi mummunan ja, sam kansa ya kulle, ƙwaƙwalwarsa ta tsaya cakk da aiki. Komai ya koma masa a baibai. Ji yake kamar duniyar ma ta koma masa ƙasa a sama.

Sosai ya cigaba da kallansa yana nazarinsa.

"Duk yanda aka yi ba lafiya ba." Ya faɗa a kan laɓɓansa. Se ya ƙarasa da sauri ya ja side drawer ya zauna. A hankali ya ɗora hannunsa kan kafaɗar Bad Man ɗin yace

"Areef.." Har bayan shuɗewar fiye da minti 1 Bad Man be buɗe idanunsa ba. Se da Gwanin ya sake taɓa kafaɗarsa sannan ya buɗe jajayen idanunsa, har lokacin zuciyarsa babu abin da take yi ban da wani irin bugu. Hakan ne kuma ya sa ƙirjinsa ke ɗagawa da wani irin sauri.

"Ba ka da lafiya ne?" Gwani ya faɗa a ruɗe saboda yanda ya ga idanun nasa. Runtse idanunsa Bad Man ya sake yi har lokacin be ce komai ba. Sam ya ma rasa me ze ce. Shin wace kalma ze buɗe baki ya faɗa a yanzu? Ashe da ma ta ƙi shi ne saboda shaye shaye? Ta kuma sakko ta amince da shi saboda a tunaninta ya dena. Se ga shi a ranar ya jawa kansa. Wani rikitaccen al'amari ya faru. Shin da wane ido ze kalleta ya yi mata bayanin ba sha ze yi ba? Shin wace kalma yake da ita wadda ze iya kare kansa a wajenta? Ta yaya ze kalleta yace mata tun ranar da Mommah ta kama shi yana sha har yanzu be sake sha ba? Bayan ga shi ta kama shi dumu dumu da kwalbar giyar a hannunsa.

"Wai ba za ka faɗa min ba ne? Me ya faru? Wani abun na damunka ne?" Gwani ya sake tambaya a karo na barkatai. Se a lokacin ya lumshe idanunsa kafin ya buɗe, a hankali ya saka hannunsa a saitin zuciyarsa kafin yace komai Gwani ya katse shi da faɗin

"Uhmmm..?" Ya yi maganar cike da tsoro yana cigaba da kallansa.

"Bro ka taimaka min. Na rasa yanda zan yi, ban san abin da ya kamata na yi ba kuma. Na yi na yi iya ƙoƙarina amma abin na neman fin ƙarfina.. Ban san me ye laifin zuciyata ba da ta kamu da ƙaunar Afrah ba. Tabbas na san a da ba na sonta ko kaɗan, amma a hankali a hankali na fara koyon sonta, tun ba na yarda daga baya na haƙura na yadda haka ɗin ne. Se dai a yanzu ba na tunanin zuciyata za ta samu sukuni idan har ban sameta ba. Se dai na sani ko me ya faru laifina ne.. Amma wallahi na tuba, na kuma dena abin da take so na dena. Ka taya ni yi mata bayanin abin da take tunani ba haka ba ne. Wallahi ni kaɗai na san yanda zuciyata ke min zafi, na rasa yanda zan yi." Ya ƙare a raunane yana sake kwantar da kansa jikin gado yana ƙara dafe saitin zuciyarsa. Kallansa Gwani kawai yake yi, lallai Allah me yadda ya so da bawansa. Kwata kwata idan ka san Bad Man ba za ka taɓa cewa shi ne yanzu a gabanka ba. Ba za ka taɓa yadda shi ne mace ta juya ya yi laushi haka ba. Wani irin tausayinsa ya kama shi. Lallai tabbas yana buƙatar shawara, ga kuma dukkan alamu sun nuna abin da ke fitowa daga bakinsa haka yake a zuciyarsa.

"Shi kenan.. Ka dena saka damuwar nan a ranka, in Sha Allah komai ze yi daidai. Wannan damuwar sam ba ita ce mafita ba." Gwani ya faɗa a tausashe. Murmushin yaƙe ya yi wanda iyakarsa kan laɓɓansa bayan ya ɗago yana kallan Gwanin yace bayan ya girgiza kai.

"Ya zan yi?" Nan ya faɗa masa abin da ya faru ɗazun da zuwan Didi cikin ɗakin. Shiru kawai Gwani ya yi dan shi kansa ya ji abin sosai. Wato duk wannan abun ne ashe ya sanya shi cikin damuwa? Ya girgiza kai kafin ya sauke ajiyar zuciya yace

"Ka tabbatar ka dena abin da kake yi Areef?" Iska ya fesar daga bakinsa kafin yace

"Me ye ze sa na yi ƙarya Uhmm? Na dena wallahi In Sha Allah.. Ka taya ni da addu'a." Wani ƙawataccen murmushi ne ya wanzu a kan kyakkyawar fuskar Gwani. A kan laɓɓansa ya furta

"Alhamdulillah.." A fili kuma se yace

"In Sha Allah.. Allah Ubangiji Ya ƙara shiryaka.. Ya daidaita tsakaninka da Afrah. Afrah na da kyakkyawar zuciya, wato ka godewa Allah da ya baka mace irinta, macen da ke janyoka daga halaka, take nuna fushinta saboda ka dena saɓawa Ubangiji.." Daidai lokacin Mommah ta ƙarasa shigowa cikin ɗakin jikinta a matuƙar sanyaye. Duk suka kalleta kamar wasu marasa gaskiya. Se ta maida dubanta kan Bad Man da ta gan shi tamkar wani mara lafiya. Ta girgiza kai tana jin jikinta na ƙarasa mutuwa gaba ɗaya. Kamar ya san ta ji abubuwan da ya faɗa se ya maida dubansa kanta shi ma yace a hankali

"Mommah!" Se da ta sake kallansa cike da tausayawa sannan tace

"Na'am.."

"Mommah na yi nadama, Mommah na yi nadama wallahi.. Sam ban san dagewa da waccan matar ta yi na tafi ƙasar waje cutata ta yi ba. Se yanzu da na gaza samun abin da nake so saboda ɗabi'ar da na koyeta a U.S. Mommah har na bar ƙasar nan ban taɓa sha'awar ko da shan taba ba ne ballantana a kai ga giya. Se da na je U.S na haɗu da abokai kala kala, waɗanda shan giya da neman mata a wajensu ba komai ba ne, a lokacin ne ni ma na soma shan giya. Ashe ban san babbar illa na yi wa kaina ba. Ga shi kuma tuntuni na san abin da nake yi ba daidai ba ne, shi ya sa ba na taɓa barin wani ya sani. Se dai ga shi Mommah kin sani kuma ki na fushi da ni saboda haka, Afrah ta sani ita kuma ta guje ni saboda hakan. Toh ya haɗuwata da Allah kuma kenan? Mommah na yi nadamar zuwana U.S, wallahi na yi nadama. Don Allah Mommah ki yafe min." Ya ƙare muryarsa a raunane kai ba za ka taɓa cewa Bad Man ba ne. Shiru Mommah ta yi lokacin da idanunta suka ida cika taff da hawaye, wani irin tausayin ɗan nata ya cigaba da nuƙurƙusar zuciyarta. A hankali ta ɗora hannunta a goshinta ta dafe, wani irin ƙunci cikin zuciyarta take ji. Haƙiƙa Mom ta cuceta, ko mene ne ya faru silar Mom ɗin ne. Shi kansa Gwani ya ma rasa me ze ce saboda tausayin ɗan uwansa. Yau soyayya ta sa duk ya zubar da makaman yaƙinsa, soyayya ta chanja shi, ta sauya shi gaba ɗaya. Ita kam Mommah tunani take ma me za tace masa? Shin bayan duk waɗannan abubuwan da ya faɗa za ta buɗe baki ne tace ba ta yafe masa ba? Kuma ba ta goyon bayan komawar Didi wajensa??

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO77*

___Shin ita kam da ta kasance wata irin uwa kenan? Uwa mara tausayin ɗanta? Ko kuwa muguwar uwa wadda ba ta amsa sunan uwa ba? A hankali ta kamo hannun Bad Man tace muryarta a sanyaye

"Na yafe maka Areef, na yafe maka. Allah Ya ƙara shirya min ku gaba ɗaya." Se ta dakata a nan

"Ameen." Gwani ya amsa da hakan. Se a lokacin wani guntun murmushi ya suɓucewa Bad Man. Ya runtse idanunsa yana saurarar bugun zuciyarsa, kafin a hankali ya buɗe idanun nasa yace
Chapter 101 · 0% Book details