← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 122

Sashe 102

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na gode Mommah.." Ita ma murmushin ta masa kafin ta ɗora da faɗin

"Afrah amana ce a wajenka Areef.. Yarinya ce nutsatstsiya, kuma me hankali. Tun farkon aurenku na so ka karɓeta hannu bibbiyu amma Allah be ƙaddara hakan ba."

"Mommah yanzu na karɓeta hannu uku uku ma.." Ya yi maganar da iya gaskiyarsa yana marairaice fuska. Dariya Mommah da Gwani suka yi jin abin da ya faɗa. Mommah tace

"Na ji, na kuma amince.. Se dai ka sani ba komai da kake so ne kake samu a lokacin da kake so ba. Ka na sonta, se dai ita kuma ta kafa maka hujjar za ta soka ne matuƙar ka watsar da wannan ɗabi'ar. Saboda haka abin da nake so da kai ka yi ƙoƙarin karɓo soyayyarka daga wajenta. Ni kuma zan tayaka wajen fahimtar da ita ka dena abin da ba ta so. Kar ka ba ni kunya don Allah.. Na kuma yi maka alƙawarin idan dai har ta amince ni ba ni da matsala ko a ranar zan iya baka matarka.." Wata ƙatuwar ajiyar zuciya ya sauke, yana jin wani ɓangare na damuwarsa na raguwa. Duk da ba ita da kanta Didin ce ta masa magana ba, amma maganar Mommahn ta mugun kwantar masa da hankali, ta kuma tafi da wani kason daga cikin damuwarsa.

"Ba zan ba ki kunya ba in Allah Ya yarda Mommah.. Wallahi ina sonta sosai." Ya ƙare maganar yana dafe saitin zuciyarsa. Sakin hannunsa Mommah ta yi tana kai masa duka lokaci ɗaya tana murmushi. Kaucewa ya yi yana faɗin

"Oouhhh Mommah.." Ya yi maganar yana yana ɗora hannunsa a kan fuskarsa. Dariya dukkansu suka yi har da Gwani dake mamakin Bad Man da ba ya iya ɓoye ƙaunar da yakewa Didin har yake iya bayyanata gaban Mommah.

... A ɓangaren Didi kuwa tana shiga ɗaki se ta kasa riƙe kukan da ya taho mata. Kawai se ta fashe da kuka tana faɗawa kan gado. Haka nan kawai ƙirjin Lulu ya buga da ƙarfi. Ta miƙe ta ƙarasa inda Didin take da sauri. Hannu ta saka ta ɗago kanta tana faɗin

"Didi me ya faru?" Ta faɗa muryarta a raunane kamar me shirin fashewa da kuka. Se a lokacin ma ta ida sakin kukan gaba ɗaya. Ta shiga raira shi zuciyarta na mata zafi. Ruɗewa Lulu ta yi dan ba kasafai ta saba ganin irin haka ba. A karo na biyu ta sake yin ƙarfin halin faɗin

"Don Allah me ya dame ki Didi? Ki dena kukan nan kin ji?" Ta ƙare tana kallan fuskarta. Jin yanda Lulun ta yi magana ne ya sanyata soma rage kukan nata. Dan ta san halin Lulun yanzu za ta fita shiga damuwa. A hankali ta koma sauke ajiyar zuciya duk da hawayen ba su dena zuba ba. Hannu Lulu ta saka tana goge mata hawayen, daga zarar sun sakko se ta ɗauke su da hannayenta.

"Didi ki faɗa min me ya faru?" Ajiyar zuciya Didi ta sauke bayan ta ƙarasa zama sosai. Ta lumshe idanunta kafin ta buɗe a hankali tace

"Lulu har yanzu be dena ba.. be dena ba ashe.." Ta ƙare wasu zafafan hawaye na sake sakkowa daga cikin idanunta. Rashin fahimtar zancen Didin ne ya sanya Lulu ƙura mata idanu tana nazarinta, gefe guda kuma tana nazarin abin da ta faɗa ɗin ko za ta fahimta ko da ba ta ƙara mata wani bayani ba.

"Lulu Areef fa.. Yace ya dena shan komai ashe be dena ba." Ta faɗa tana jin zafin abin da take faɗa ɗin.

"Inna lillahi..." Lulu ta faɗa. Hannun Didi ta kamo ta soma faɗin

"Don Allah ki kwantar da hankalinki komai me wucewa ne.. Ki dena saka damuwa a ranki. Allah ze shirye shi kamar yanda kike fata. Ze kuma zama kamar yanda kike so In Sha Allah." Murmushin yaƙe Didi ta yi kawai tana kallan Lulu. Se dai ta ɓangare guda kuma addu'ar ta burgeta, se take ganin kamar ba Lulunta ba. Cigaba suka yi da zama cikin ɗakin suna cigaba da tattaunawa. Har zuwa lokacin da dukkansu suka yi shiru. Shiru Lulu ta yi na tsawon lokaci kamar me tunani. Wai an ya idan ta cigaba da abin da take yi ba ta butulcewa Allah ba kuwa? Duk kirki da kyawawan hali irin na Didi se Allah Ya bata miji mashayi. Ita kuma da Didin ta fita a waɗannan wajajen se ga shi Allah Ya bata miji kintsatstse kuma shiryayye. Me ya kamata ta yi ita kam a yanzu? Yanzun da ta gano hakan. Shin ta cigaba da jan baya da shi, ko kuwa ta karɓe shi hannu biyu a matsayin mijinta? A haka Mommah ta zo ta same su. Ta ƙaraso ta nemi waje ta zauna. Se da ta kalli Lulu tace

"Daughter ya kike? Ya jikin naki?" Hannunta ta kama ta ɗan murza bayan ta yi ƙasa da kanta tace

"Alhamdulillah.."

"Toh madallah.." Mommah ta faɗa. Se ta maida dubanta kan Didi tace

"Daughter kuka kika yi?" Ta tambaya a hankali tana kallanta. Da sauri Didi ta girgiza kai tana ƙaƙalo murmushi tace

"A'ah Mommah." Murmushi Mommah ta yi, murmushin nata da shi ma za a iya kiransa da na yaƙe kafin tace

"Ki dena ɓoyewa, idanunki, da duk wani yanayinki ya nuna kuka kika yi. Kuma na san Areef ne sila." Da sauri Didi ta ɗaga kai ta kalli Mommah, se dai ba tace komai ba. Dan ba ta san me za ta ce ba. Dan haka kawai se ta maida kanta ƙasa. Tashi Mommah ta yi ta matsa sosai kusa da Didin. A hankali ta soma faɗin

"Afrah. Kamar ko da yaushe ina miki magana ne a matsayina na mahaifiyar Areef kuma wadda take ɗaukarki a matsayin 'ya. Ina so ki sani kamar yanda wancan karon na zo na miki magana a kansa.. yau ma na dawo na miki magana a kansa. Ba wai dan kasancewarsa ɗana ba a'ah.. se dan sasanta rikici ko kuma nace rashin fahimtar da ya shiga tsakaninku.." Daga nan Mommah ta zayyane mata yanda suka yi da Bad Man. Daga nan kuma ta ɗora da faɗin

"Ina fata ina me kuma roƙon za ki amshi tubansa, ki yafe masa ko da ba duka ba ne.. Sannan duk kuma lokacin da na roƙi ki koma ɗakin ki za ki koma." Shiru Didi ta yi. I zuwa lokacin da Mommah ta kai ƙarshen zancenta na farko se ta lumshe idanunta tana jin wani irin sanyi na ratsata. Ta san Mommah ba za ta mata ƙarya ba ko da kuwa a kan waye. Ballantana ma a kan wannan abun da tafi kowa son ta ga ya dena. Idan dai kuwa har da gasken ya dena tana ɗaya daga cikin waɗanda za su fi kowa jin daɗin hakan. Dan ba ta san dalilin da ya sa al'amarin ya tsaya mata a rai ba. Har wataran ya kan hanata bacci.

"Mommah ni da ma ba abin da ya min.. Kawai ina so ne ya dena abin da yake yi."

"In Sha Allah ya dena Afrah." Mommah ta ƙare tana murmushi.

.. Gaba ɗaya ta rasa dalilin da ya sa tun da ta tashi take jinta kamar ba ita ba. Haka nan kawai take jin wani irin ɓacin rai kamar wadda akawa laifi. Didi na zaune a kan gado hannunta ɗauke da wani littafi tana karantawa. Tun ɗazu take tambayar Lulun dalilin fushinta amma tace mata babu komai. Tun tana rarrashinta har ta fusatata ta ƙyaleta ta mata banza. Ita kuma da gasken take ta rasa me ke damunta, kawai haka nan take jin haushi kowa.

"Didi.." ta faɗa tana kallan Didin. Juyar da kai Didi ta yi tana cigaba da karatunta. Kawai se ta juya ta fice daga ɗakin. Gaba ɗaya ma sashen take ƙoƙarin bari ta je waje ko sa ta ji ɗan dama dama. Daidai tana ƙoƙarin ficewa daga sashen gaba ɗaya ya shigo ciki. Yanda suka kusa karo ne ya sanyata komawa da baya tana dakatawa. Shi ma dakatawar ya yi yana aza idanunsa a kanta dan be yi tsammanin ganinta ba. Kamar ta wuce haka ta ji, se dai ta kasa kawai ta cigaba da tsayuwa. Kallo ɗaya ya mata ya fahimci ba lafiya ba. Dan yadda kafatanin fuskarta ke a haɗe kamar wadda ke shirin yi wa kowa duka.

"Lafiya..? Me ya faru?" Ya tambaya yana jin ɗan tsoro tsoro na kama shi. Kawai se ta ji kuka na son ƙwace mata ba tare da sanin takamaiman dalilin hakan ba. Hannu ya saka ya kamo hannunta idanunsa a kan fuskarta kafin ya ɗan matsa yanda ze iya jinta sosai. A hankali kuma cikin nutsuwa yace

"Me ya faru Uhmm? Wani abun na damunki ne?" Ita kam ta rasa yanda za ta yi, duk yanda take babbasarwa take ƙoƙarin ƙin bin abin da zuciyarta ke raya mata ta yi a kan Gwani ta kaasa. So take ta cigaba da tafiya a yanda suke da, ko ba dan komai ba se dan abin da ta yi tunani tun ranar farko, wato ranar da ta gane shi ɗin jika ne ga sarki, kuma da ma ga shi ɗan gidan Alhaji Matawalle. Ba ta so ya yi mata wata fassarar, ba ta so ya yi tunanin wani abun. Duk da babu ko da makamancin haka ne cikin ranta. Se dai tana tsoro. Amma duk da haka yau ta kasa cigaba da halin da take yi. Girgiza kai ta yi kafin a hankali tace

"Ba komai." Ta faɗi hakan dan ita dai ba za tace ga takamaiman abin da ke damunta ba, kawai dai ta tashi ne da ɓacin rai. Girgiza kai Gwani ya yi damuwa na bayyana saman kyakkyawar fuskarsa yace

"A'ah kar ki ce haka.. Ki faɗa min don Allah.." Ɗaga narkakkun idanunta ta yi da ke cike da ƙwalla ta zuba masa idanunta. Shi ma kallan nata yake yi. Se kuma ta lumshe idanunta kafin ta buɗe tace
Chapter 102 · 0% Book details