Sashe 33
A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Afaaf.." Duk da ta ji shi saboda ba bacci take ba, amma ba ta da ƙarfin amsa masa. Jin da ya yi shiru ne ya sanya shi sake maimaita sunan nata da a bakinsa yake fita na daban. Motsawa kaɗan ta yi se dai har lokacin idanunta a rufe suke. Miƙewa ya yi a hankali ya nemi gefen gadon ya zauna ya yaye abun da ta lulluɓa da shi ɗin. Yanda take cure a waje ɗaya ne ya sanya shi se da ya ɗagota sannan ya soma saka mata towel ɗin da ya jiƙa shi da ruwa me ɗan sanyin hankali. Bugun da zuciyarta ke yi ne ya ƙaru, ta yi ƙoƙarin tashi se dai ta san yaudarar kanta take yi ba iyawa za ta yi ba. Gaba ɗaya jikinta zafi, har wani huci ke fita idan ta yi nishi. A wuyanta ya soma dandala mata towel ɗin, daidai lokacin da ta yi ƙarfin halin komawa baya ko da faɗawa ne kan gadon ta yi, ita dai ta dena jinta a jikinsa. Ɗan ƙaramin tsaki ya yi yana sake riƙeta sosai. Ya cigaba da abin da yake yi. Da dai ta ga ta kasa yin komai se kawai ta haƙura ta cigaba da kukan da shi ne mafita kawai. Har kuma lokacin zuciyarta ba ta dena bugawa da sauri ba. Shi da yake dab da ita har iya jiyo bugun zuciyarta yake yi. Gaba ɗaya a rikice take, a kuma tsorace take. Zazzafan numfashinta dake sauka a jikinsa ya nemi saukar masa da kasala, se dai be bi ta kan hakan ba ya cigaba da abin da yake yi yana ɗan ɓata ransa. Se da ya tabbatar jikin nata ya ɗan lafa daga ɗaukar zafin da ya yi sannan ya ajje towel ɗin. Ya san idan dai har ya ƙyaleta sake lulluɓar za ta yi ba tare da ta damu da zafin da jikinta ya yi ba. Kamar ya rabu da ita, se kuma ya kasa tafiya. Se yake ji kamar idan ya tafi ɗin be yi adalci ba.
"Don Allah ka ƙyale ni.. ka sake ni.." ta faɗa da dashashshiyar muryarta hawaye na zuba daga gefen idanunta dake a lumshe. Kallan fuskar tata ya yi se ya ji wani abu na son ɗarsuwa a cikin ransa, ya yi saurin kawar da shi yana fidda iska daga bakinsa. Kamar ba ze ce komai ba se kuma ya buɗe baki kamar ba ya son yin maganar yace
"Ki yi baccin ki.." ya faɗa yana gyara mata kwanciyar ko da za ta samu ta yi baccin.
"A'ah ni dai ka.."
"Shhh..!!" Ya katseta da faɗin hakan, kafin ta sake cewa komai yace
"Na ce ki yi baccin ki koh?" Ya ƙare maganar daidai lokacin da ruwan hawaye suka zubo a kan hannunsa. Ya girgiza kansa yana sake mamakin yanda ta chanja gaba ɗayanta kamar ba ita ba. Da dai ta gaji, ta kuma ga ba shi da niyyar sakin nata se kawai ta haƙura, dan har ta gaji da yunƙurin da ta san shi kaɗai ɗin za ta iya.
Shiru ya yi yana saurarar bugun zuciyarsu dake fita kusan a tare, ya ɗan lumshe idanunsa a ransa yana tsara yanda ze cigaba da nemo daga inda hoton ma kansa ya zo wajen Abbati. Tunda abin nan ya faru gaba ɗaya zuciyarsa ba ta hutawa, kullum burinsa ya gano gaskiyar lamarin, wanda hakan ne ze wanke Lulu 100 bisa 100 daga duk wani zargi da ya so shiga tsakaninsu. Tun dai tana ta ƙoƙarin kufcewa har dai ta haƙura saboda yanda jikinta yake babu ƙwari, se komawa ta yi ta yi shiru kawai. Ba ta taɓa kawowa kanta za ta iya yin bacci ba dan har lokacin ta kasa dena kukan, se dai ba tare da ta shirya ba bacci ya zo ya yi awon gaba da ita. Kallan fuskarta ya yi lokacin da ta soma sauke numfashi a nutse, fuskarta ta sake yin fayau kamar ba ita ba. Ya ji wani abu ya tsirga masa tun daga saman kansa har ƙasan ƙafarsa, wanda hakan ya tilasta masa sauke ajiyar zuciya. Bayan shuɗewar wasu mintuna ya soma ƙoƙarin miƙewa tunda dai ta samu baccin. Se dai me? Yanda jikinta yake da zafi, yayin da na shi kuma yake da sanyi, hakan ya yi mata daɗi sosai, yana ƙoƙarin sauketa daga jikinsa ta yi saurin riƙo shi ba tare da ta sani ba. Hannunsa da ta rungumo ya bi da kallo, da alama ba ta san me ta yi ba. Ya ɗan sake ƙoƙarin zamewa se ta sake riƙo shi. Ajiyar zuciya ya sauke yana ɗan lumshe idanunsa sannan ya buɗe su lokaci ɗaya. Har lokacin jikinta da zafin, wanda cikin ƙanƙanin lokaci ya soma wasar jikinsa saboda yanda ta cukwuikuye shi tana baccinta hankali kwance. Duk da fuskarta kaɗai za ka kalla ka fahimci ba daɗin baccin take ji ba. Haka yana ji yana gani ya cigaba da zama don ta yi baccin. Har kusan bayan mintuna da dama ta ƙi sakinsa, da dai ya ga ba ta da niyyar sakinsa se kawai ya gyara zamansa kan gadon ya barta idan ta gama baccin se ya tashi. Ɗan lumshe idanunsa ya yi tunani barkatai na zuwar masa ƙwaƙwalwa..
.... Kwana biyu ta jera tana kai masa Coffee ɗin kamar yanda ya buƙata safe da daren. Kodayaushe idan ta je kaiwa ɗin kuma babu fashi za ta gaida shi.
Yau ma kamar ko da yaushe ta gama haɗa komai cikin ƙaramin cup, ta wuce ɗakin ta yi knocking. Ta saba jin shiru ko da yana ciki kuwa, hakan ne ya sanyata cigaba da tsayuwa har bayan shuɗewar wasu sakanni. Lura da ta yi ƙofar ɗakin a buɗe take ya sanyata saka hannu ta turata. Kai tsaye ta wuce inda ta saba ajjewa ba tare da ta kalli ainahin cikin ɗakin ba. Ta je ta ajje sannan ta soma takawa dan ficewa daga ɗakin. Tozali da wasu kwalabe zube a kan kujera ta yi, wata murfinta yashe a ƙasa yayin da wata take rufe da murfinta. Shi kuma yana kwance a kan gadon, ƙafafunsa ne kaɗai zube a ƙasa yayin da duka gangar jikinsa na kan gado ne. Lokaci ɗaya ta ji ƙirjinta ya buga, ta ɗan sake satar kallan kwalaben. Haka kawai zuciyarta ta bata waɗannan ɗin kwalaben giya ne, kenan ya sha su ne ya bugu shi ya sa yake bacci? Cikin ƙanƙanin lokaci jikinta ya ɗauki rawa, se ta ji komai na son sire mata. Kenan ɗan giya ne dama?
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.." ta faɗa a kan laɓɓanta tana cigaba da kallan kwalaben. Hawaye ta ji suna son taho mata, ta yunƙura da niyyar ficewa, kamar kuma wadda aka riƙo se ta dakata, ta juya ta sake kallan kwalaben. Kawai se ta ƙarasa inda suke, ta sanya hannunta ta ɗauke su, ta ɗan sake kallan inda yake kwance tana jin wani irin yanayi da ta kasa fassara shi. Duk da yanda jikinta ke rawa, zuciyarta ke a ƙuntace, tsoro na mamaye ƙarfin gwiwarta, hakan be hanata ɓoye kwalaben cikin hijab ɗinta ba sannan ta fito daga cikin ɗakin. A hankali ta cigaba da takawa dan ficewa daga sashen gaba ɗaya, karo na farko kenan tun zuwanta gidan. Daidai tana shirin fita Daddy da tun ɗazu yake kiran number Bad Man be ɗaga ba, hankalinsa ya kasa kwanciya se da ya zo da kansa dan duba shi, suka yi kaciɓus. Zuciyarta ta wani irin tsinkewa lokaci ɗaya tana dakatawa.
"A'ah Afrah.." Daddy ya faɗa. Se a lokacin ta sauke ajiyar zuciya sannan ta buɗe idanunta ta kalli Daddyn tace
"Barka da wannan lokaci.." ta yi maganar tana sake ɓoye kwalaben hannunta.
"Barka dai.. lafiya dai koh?" Daddy ya tambaya ganin yanda take a birkice kamar wadda aka biyo. Murmushin yaƙe kawai ta yi tana faɗin
"Ehh.. ehh.."
"Toh madallah.." Shi ne abin da Daddy ya faɗa kawai. Se da ya shige ciki sannan ta iya ficewa duk ta gama ruɗewa kamar wata korarriya. Kai tsaye ɗakin Bad Man ɗin Daddy ya wuce. Ya tura ƙofar ɗakin yana kallan cikinsa. A kan gadon ya hangi Bad Man, cike da mamaki yake kallansa yana tunanin baccin na meye haka? daidai lokacin da hancinsa ya shiga shaƙo masa wani ƙamshi ƙamshi na daban da ya kasa bambance na meye? Se ya ɗauke kansa daga kan Bad Man ɗin ya maida cikin ɗakin dan ganin abin da ke wannan ƙamshin mara daɗi..
✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO41*
___A iya hangensa be hango abin da ze iya cewa shi ke wannan ƙamshin ba, wanda zuwa yanzu ƙamshin turaren dake tashi tun ɗazun ya yi tasiri wajen danne shi. Numfashi Daddy ya sauke yana ƙarasawa inda Bad Man ɗin yake, ya saka hannunsa ya ɗan yi tapping na kafaɗarsa. Ko motsawa be yi ba saboda yanda baccin ya masa daɗi.
"Areef.." Daddy ya faɗa yana sake mamakin wannan baccin haka. Se a lokacin sannan ya soma ɗan buɗe idanunsa da suka masa nauyi. Be yi tsammanin akwai wanda ze shigo har cikin ɗakin tashinsa ba, hakan ne ya sa ransa ya mugun ɓaci tun kafin ya ida buɗe idanunsa. Da ƙyar ya ƙarasa buɗe idanun nasa ya zube su a kan Daddy dake tsaye yana kallansa. Mamaki ya kama shi ganin Daddyn da be taɓa zata ba. Da sauri ba tare da ya shirya ba ya tashi zaune a kan gadon ya soma jefa idanunsa cikin ɗakin cike da fatan Daddyn be ga abubuwan dake ajje ba.
"Bacci na meye haka?" Daddy ya faɗa yana kallansa. Sake wurga lumsassun idanunsa ya yi yana ɗan shafa sumar kansa sannan murya a cunkushe ya buɗe baki da ƙyar yace
"Hu..tawa.." ya ƙare yana yamutsa fuska saboda yanda yake ji ma kamar yanzu ya fara yin baccin, idanunsa har wani cigaba da lumshewa suke, se dai se basarwa yake yi kada Daddyn ya fahimci wani abun. Cigaba da kallansa Daddy ya yi, haka kawai wani zargi ya so ya ɗarsu a ransa, se dai har abada ba ya fatan hakan, hakan ne ya sanya shi kauda wannan tunanin yace
"Ka tashi haka nan.. Idan ka shirya ka same ni a parlourna ina jiranka.."