Sashe 95
A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Se da na saka aka min bincike na gano ashe ma kun bar wajen dangin mahaifiyar taku yanzu haka ku na cikin garin nan. Na yi mamaki ainun da ya kasance duk tsayin shekarun nan ashe muna cikin gari ɗaya, amma ba ku taɓa nemana ba ko ni ko ragowar en uwa. Se dai da na tuna ni kaina na manta da shafin rayuwarku ya sanya ni yi muku uzuri. Na san kuma ɗauke muku hankali aka yi daga kanmu, tun da ga shi ku kuna ganina ma a wasu lokutan amma ba ku taɓa kawo komai a ranku ba. Ashe ashe duk ba mu sani ba aikin Samira ne.." Baba Abdullahi ya ƙarasa yana girgiza kai. Mommah da Yaya Amina kuka kawai suka shiga yi, rayuwarsu ta baya na dawo musu. Sun ɗauki mintuna masu tsayi kafin suka samu suka yi shiru. Se suka koma suka shiga gaisawa da Baba Abdullahi. Kamar ba sarki ba haka ya saki jiki yana jan su da hira duk dan ya kawar musu da damuwar da ya ga sun shiga a yanzun. Babu laifi sun ɗan saki jiki duk da idan suka tuna da abin da Samira ta musu se su ji duk wata damuwa ta mamaye su. Tunanin mahaifiyarsu se ya dawo musu sabo.
Sosai Baba Abdullahi ya ji daɗi lokacin da ya ji yana da jikoki. Dan haka babu ɓata lokaci ya sa a kira masa su ya gansu. Baba Atine Mommah ta saka aka kira mata, da kanta ta je ta isarwa Twins ɗin saƙon Mommah na son ganinsu da ake yanzu. Babu ɓata lokaci kuma suka wuce kiran Mommahn. A daidai za su shiga sashen suka yi kaciɓus da su Lulu da su ma suke shirin shiga sashen. Dukkansu dakatawa suka yi. Didi ta yi wani saurin janye idanunta, dan ba ta tunanin bayan abin da ya faru kuma za ta iya cigaba da haɗa ido da Bad Man ɗin. Hannunta har rawa yake lokacin da ta yi amfani da shi wajen riƙo hannun Lulu.
"Barkanku da wannan lokaci.." Ta faɗa tana jan hannun Lulun. Kamar wata doluwa se ita ma ta maimaita abin da Didin ta faɗa kafin suka shige da sauri. Kamar waɗanda ake ja se duka suka bi su da kallo. Shi Gwani ma se yanzu ya lura da chanjawar da Lulu ta yi. Dan idan da a yanzu ka sansu toh tabbas za ka bambance su, saboda yanda yanzu Lulun ta ƙara haske, ga kuma jikinta da yafi na Didi a yanzu. A tare suka ɗaga kai suka kalli juna kamar wanda suka ga wani abu. Se kuma cikin basarwa duk suka janye idanunsu. Murmushi Gwani ya yi a kan laɓɓansa ya furta.
"Ya Allah!!" Ya ƙare yana ɗan rufe idanunsa. Se kuma daga baya ya buɗe, kai tsaye suka faɗa cikin ɗakin.
Da sallama suka shiga cikin ɗakin, suka gaisa da kowa sannan su Lulu suka nemi waje suka zauna. Kafin su Gwani su zauna Baba Abdullahi yace
"Kar dai waɗan ne Abokan nawa?" Baba Abdullahi ya faɗa yana kallansu Bad Man. Jinjina kai Yaya Amina ta yi tace
"Ƙwarai kuwa su ne.."
"Ikon Allah.. Ku zo in ganku.. Yau ga yaran Sa'adatu a gabana.." Ya yi maganar yana miƙa musu hannu. Sam ɗaukar sarautar ya yi yanzun ya ajjeta a gefe, dan ganin 'ya'yansa da jikokinsa da ya yi ya saka shi cikin matukar farin ciki mara misaltuwa.
"Wannan shi ne Kakanku.. Ƙani ne a wajen mahaifinmu ni da Yaya Amina.." Mommah ta faɗa dan haska musu waye shi. Se kuwa suka ƙarasa suka zube suka shiga gaisawa. Sosai ya sakar musu fuska yana ƙoƙarin kawo wasa a gaisawar tasu. Kallansu ta yi lokacin da suke duƙe gaban Baba Abdullahin. Ta lumshe idanunta tana jin wata ƙwalla na tarar mata cikin idanu. Ita kam ba ta san da wane baki za ta godewa Allah ba. Irin waɗannan ni'imomin da ke kewaye da ita. Abubuwan alkhairi se faruwa suke da ita ba tare da ta yi tsammani ba. Se ta buɗe idanunta a kan nasu dai, daidai lokacin da Bad Man kalli Didi se kuwa ta kama shi dumu dumu yana kallan Didin. Ta maaze tana watsa masa wani kallo tana ɗauke kai. Da sauri shi ma ya ɗauke kansa a sukwane. Shi kam be san me Mommahn ke nufi da shi ba. An aura masa mata ana so ya zauna da ita, da farko ya nuna ba ya so, yanzu kuma yana so ba shi kenan ba? Se dai da alama ya ga ba haka ba ne. Dan a yanda ya lura da take-taken Mommah tamkar wani yaƙi ne a gabansa.
Sake gaisawa Baba Abdullahi ya yi da matan jikokin nasa kafin ya maida dubansa kan en biyun da ke gabansa zaune. Abin da ya san dole za su kawo a ransu shi ne duk lokacin da ya wuce me ya sa basu san shi ba? Ina yake? Dalili kenan da ya sa cikin nutsuwa ya shiga haska musu abubuwan da suka faru a taƙaice. Shiru dukkanninsu suka yi cike da mamakin jin wannan abu da ya fi kama da almara. Lallai Mommah ta ga rayuwa. Ƙaddarori kala-kala ta gansu. Didi ma kanta kallan mutanen cikin palourn take, cike da tausayin Mommah da kuma Yaya Amina. Lallai a kowanne irin yanayi ka tsinci kanka kar ka cire ran samun sauƙi. Wato gaba ɗaya dai rayuwar Mommah ishara ce a wajen mutane. Tun daga kan iyayenta, danginta ta soma fuskantar ƙalubale. Haka kuma a kan 'ya'yanta ma. Se ga shi da ta yi haƙuri a cikin kwanaki kurkusa duka matsalolinta sun warware. Dangin nata sun bayyana, haka kuma 'ya'yan nata ma sun bayyana cikin ƙoshin lafiya. Ko wannan ya isa ya zamarwa bawa ishara. Kamar wata doluwa, kamar kuma wata mara lafiya ita kanta haka take jinta. Ba ta san dalilin da ya sa tun da ta ji su Gwanin jikokin Sarki ne ta ji wata irin kunya, sanyin jiki da kuma mamaki sun rufeta ba. Runtse idanunta ta yi ƙirjinta na bugawa. Kenan da gaske Gwanin ya kasance jikan Sarki ne? Kenan wannan ne dalilin da ya sa duk da be yi rayuwa tare da Mommah ba ya kwaso halayen gidan sarautar? Kenan shi ya sa take ganin halayensa gaba ɗaya sun bambanta da irin gidan da yake ciki? Ashe shi ya sa idan yana wani abun se ka ɗauka ɗan wani ne, ko kuma ɗan gidan wani me sarautar ne? Ko kuma shi kansa ma yana da sarautar ne? Ashe jini ba ƙarya ba ne.. Ashe da gasken shi ɗin ɗan gidan wani ne, jika kuma ga Sarki. Wanda ya yi gadon Izza tun daga kan kakansa, har kuma daga wajen mahaifiyarsa. Wasu halayen kuma ya kwaso su daga wajen mahaifinsa. Ashe ba siya ya yi ba, ba girman kai ba ne, ba kuma ɗaukar kansa wani ba ne, kawai izzar ce ke yawo cikin jininsa. Ba ta taɓa zata ba, ba ta taɓa kawo haka ba. Ita a duk lokacin da za ta gan shi, ko kuma ta ga ya yi wani abun, ba ta kawo komai se tsantsar girman kai da ɗaukar kansa wani. Ashe IZZARSA A JINI TAKE. Ba girman kai ba ne, ba kuma duk wani abu da take ɗauka ba ne. Duk da mutane da dama, ko kuma tace duk wanda ta sani kowa ba ya goyon bayanta a kan kallan da takewa Gwani, ciki kuwa har da Didinta. Dan kuwa da za ta kwana tana faɗin abin da ta saba faɗa a kan Gwani babu wanda ze yadda. Ita a duk mutanen da ta sani ma babu wanda ke ƙinsa, se sonsa da ganin mutuncinsa fiye da kima. Hakan kuma be taɓa damunta ba, a ganinta sun kaasa fahimtarsa ne kwata kwata. Se dai soyayyar da mutanen ke masa na ɗaya daga cikin dalilin da ya sa tsanarsa ta nunku cikin zuciyarta. A ganinta kowa ya kasa fahimtarta. Kowa ya ƙi bin bayanta se shi shafaffe da mai. Ba ta taɓa tunanin da gaske yanda take ɗaukarsa ba haka yake ba se lokacin da ta haƙura, ta yadda za ta zauna da shi. Wato lokacin da suka yi rayuwa a gidan Ummeey. Ba ta san dalilin da ya sa ta kasa fahimtar gaskiya suke faɗa mata ba se a lokacin, duk da a lokacin ɗin ma se ta yi ta ƙaryata zuciyarta duk sa'ilin da ta raya mata haka. Se ga shi yau an sake tabbatar mata. Bayan tabbacin da ta ƙara samu tun bayan zuwansu gidan Mommah.
"Umma ki faɗawa Baba a nan zan kwana.." Wata budurwa ta faɗa tana kallan wata babbar mace da take zaune kusa da ita. Murmushi ta yi tace
"Ba ma se na faɗa ba.. Da ma hakan za a yi."
"Yawwah Umma." Ta faɗa tana murmushi. Su uku ne za su kwana cikin gidan, ba ƙaramin farin ciki Mommah ta ji ba. Dan haka ta kira Baba Atine.
"Atine ki samu ki kai min su ɗaki.. Ba na buƙatar a yi musu komai da kaina zan yi.. Yanzun nan zan shigo.." Mommah ta ƙare tana murmushi.
"An gama Hajiya." Baba Atine ta faɗa cikin girmamawa.
... Tuntuni yake lura da yanayinta, ya kuma kasa haƙuri, be san dalilin da ya sa ya ganta cikin matuƙar damuwa ba. Dan haka suna fita be bari ta shiga ɗaki ba ya yi saurin ƙarasawa inda take. Cikin damuwa yace
"Afaaf.." Dakatawa ta yi daga inda take, dan da ma ta lura da fitowarsa daga ɗakin, bayan Mommah ta sallame su, ya yin da ta ƙi barin Bad Man ya fita. Aikuwa kawai zama ya yi amma hankalinsa ba ya wajen, dan kuwa ya san dalilin da ya sa Mommahn ta ƙi barinsa fita, dan kar ya bi Didi ne. Wai shi da matarsa amma an hana shi ko da magana ne da ita. Ko kallanta ya yi se ya samu tsarabar kallan nan na Mommah na gargaɗi. Gaba ɗaya dai Mommah ta maida shi tamkar wani kwarto.