← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 122

Sashe 18

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ai kawai ka bar shi ni da kaina zan dawo muku da shi. Yanzu dai a aiko mana da kayansa.."

"Toh shi kenan Malam.." Daga haka suka yi sallama. Fatima ta shiga motar Abba ya tada suka bar gidan cike da kewa. Fatima ji take kamar kar ta tafi ta bar ƙawar tata.

.. "Toh ka yi shiru ai dai Fatiman ta tafi.." Lulu ta faɗa tana shafa kan Little. Cuno bakinsa ya yi har lokacin hawayen ba su dena zuba ba yace

"Ba za ta kuma zuwa ba koh?" ya tambaya yana kallan Lulu. Se ta jinjina kai lokaci ɗaya tana faɗin

"Ehh.." Duk da hakan dai be saketa ba, ya sake rungumeta dan gani yake kamar idan ya saketa ba ze sake ganinta ba.

"Kawo shi nan mu je wajena. Dan da alama yaron nam ba ze yi bacci ba idan ba kya wajen." Kallanta Lulu ta yi a zuciyarta tana saƙa abin da take nufi. Kenan Little ɗin ba a wajenta ze kwana ba? Se dai ta kasa tambayarta, dan ba ta san me yasa ba matar ke mata kwarjinin da tun zuwanta ta kasa mata musu a kan komai. Maƙe kafaɗa Little ya yi yana sake rungume Lulu. Ummeey ta yi murmushi tana faɗin

"Lallai yaron nan ƙiwarka shahararriya ce.." ta yi maganar tana yin gaba. Se kawai ta bi ta har cikin ɗakin ta nemi waje ta zauna. Har kuma lokacin Little na jikinta. Ba su daɗe da zama ba Gwani ya yi sallama cikin ɗakin. Tunda ta ji sallamarsa gaba ɗaya annurin fuskarta ya ɗauke, fuskarta ta wani haɗe har da kautar da kai kamar ba ta san wani ya yi sallama cikin ɗakin ba.

"A'ah ka dawo?" Ummeey ta faɗa tana kallansa.

"Ehh Ummeey" ya yi maganar a nutse, yana kuma lura da wanzuwar wasu halittun bayan Ummeey.

"Toh sannu da dawowa. A zubo abinci ne?" Ummeey ta yi maganar lokaci ɗaya. Girgiza kai ya yi kaɗan yana ɗan yamutsa fuska yace

"A'ah.. Zan ci anjima"

"Ka tabbatar?" ta tambaya cikin kulawa, dan tafi kowa sanin halinsa. Se da ya yi murmushi sannan ya amsa da

"Ehh.." Miƙewa Ummeey ta yi ta fice daga ɗakin, dan ba ta sani ba ko ganinta da Lulu ta yi ne ya sanyata kasa furta komai tun bayan shigowar Gwani. Se dai miƙewar Ummeey ke da wuya se ita ma ta miƙe tana sake riƙe Little a hannunta. Ba ta tsammata ba, se muryarsa ta jiyo a dake yace

"Ina za ki je?" Buɗe baki ta yi da niyyar faɗar duk abin da ya zo bakinta, se ta tuna da abin da ya faru. Se ta ɗan cije bakinta kafin tace

"Toh ina ruwanka..?" ta faɗa tana hararar gefe da gefe cike da takaici.

"Wannan abincin fa?" ya tambaya tana kallan kwanon da ya gani a gabanta. Ze iya cewa tun zuwanta gidan nan be ganta ta saka wani abun a bakinta ba, dan haka be jira amsarta ba yace

"Dawo ki zauna ki ci.."

"Ba na ci." ta faɗa da sauri. Miƙewa ya yi daga inda yake, ya soma takawa kamar ze nufo inda take, se kuma ya dakata yace, lokacin da muryarsa ta ɗan kaurara kamar wanda ke fushi.

"Se kin ci.. Je ki zauna" Ya yi maganar hatta fuskarsa babu alamun wasa ko kaɗan. Jin muryarsa da ta yi a kusa da ita ne ya sanyata ɗaga kai. Se kawai ganinsa ta yi dab da ita. Da sauri ta ja baya ƙirjinta na bugawa, se dai duk da haka ji take kamar ta buɗe baki ta faɗa masa wata maganar da ze daɗe tana masa zafi a zuciyarsa. Se dai tozali da fusatattun idanunsa, se suka sanya duk wani ƙwarin gwuiwarta ya tafi. Se ma ƙwalla da ta zo ta tarar mata a cikin idanu. Ita kam ta rasa mafita a rayuwarta, kowa ba ya sonta. Tunda aka aura mata Gwani dama ta sallamawa duniya, ta san ko ba daɗe ko ba jima mutuwa za ta yi saboda wannan auran. Se dai tun kafin hakan ma ta kasance, za ta sauƙaƙawa mutuwar yanda za ta ɗauketa salin alin. Hakan ne ya sa tun zuwanta gidan ba ta ɗauki ko ƙwayar shinkafa ce ta saka a cikinta ba. Komawa ta yi ta zauna bayan ta zaunar da Little. A hankali a kuma fusace tace

"Wallahi ba zan ci ba.." Ta faɗa ƙasa_ƙasa. Ba dan ta so ba, ta saka hannu ta ɗauki cokali ta shiga bawa Little. Se da ya ga hakan sannan ya miƙe yana ɗan sakin ƙaramin tsaki ya fice daga ɗakin. Cigaba ta yi da bawa Little abincin, duk da yanda cikinta ke kiran ciroma, hakan be sanyata kai ko da lomar abinci ɗaya ba ne. Se ma sake ɗaukar ruwa kawai da ta yi ta sha. Se da Little ya ƙoshi sannan ya fara hamma alamar bacci yake ji. Daidai lokacin da Ummeey ta shigo ɗakin. Ta kalle shi ta cikin er ƙaramar fitilarsu me haske yanda yake ta lumshe idanunsa tace

"A'ah baccin ne? Mu je na kai ka toh ka yi fitsari" ta faɗa tana riƙo shi. A yanzu kam be yi musu ba se ya bari Ummeeyn ta ɗauke shi zuwa banɗakin. Babu jimawa suka dawo, kai tsaye jikin Lulu ya ƙarasa ya kwanta. Ɗan lumshe idanunta ta yi tana jin yanda cikinta ke hautsinewa yana takurewa waje guda. Ta ɗan buɗe idanunta tana sake ɗaukar ruwa ta sake bankawa cikinta. A ranta tana ji lallai wannan hukuncin da ta yanke shi ne daidai. Ko banza idan suka ga gawarta za su ɗauketa daga gidan nan, su kuma gane da gasken ba ta ƙaunar Gwani ko kaɗan. Babu daɗewa kuwa bacci ya ɗauki Little. Se a lokacin sannan Ummeey ta ɗauke shi, bayan ta yi masa shimfiɗa ta shigar da shi cikin net. Kallan Lulu ta yi tace cikin kulawa

"Ya kamata ki je ki kwanta haka nan.." Kallan Little ta yi kamar ba za ta miƙe ba, se kuma ta miƙe tana riƙo cikinta ta cikin hijab.

"Toh se da safe 'yata.." Ummeey ta faɗa da murmushi kan fuskarta

"Toh" shi ne kawai abin da Lulu ta faɗa tana wucewa, dan so take kawai ta kwanta, ta san kafin ta tashi rai ya yi halinsa. Se dai duk da haka za ta so ta sake ganin Didinta ko da sau ɗaya ne kafin ta bar duniya, ta ga Amminta ita ma ko sau ɗaya ne, haka Abbanta ma. Se dai babu wannan damar. Uwa uba kuma daga Abban har Ammin sun dena sonta. Da wannan tunane_tunanen ta ƙarasa ɗakin, kai tsaye kan gadon ta nufa. Babu ɓata lokaci ta haye, bargon dake kai ta yaɓa a kanta ta rufe idanunta. Duk da ta san dama hakan za ta faru, amma kuma tana tsoron ciwo matuƙa. Dan haka burinta a yanzu be wuce ta ji bacci ya ɗauketa ba.

.. Juyawa ta sake yi a karo na barkatai saboda yanda ta ji kamar ana ɗaukarta ana juyi da ita. Ta buɗe idanunta da sauri a tsorace. Se dai kamar yanda ta buɗe shi da sauri, haka ta kulle shi da sauri, saboda yanda wani jiri ke kwasarta duk da a kwance take, hannunta dafe da cikinta da yanzun yanda yake curewa waje ɗaya ya ninka ɗazun sau nawa. Tun tana juyi cikin bargo har se da hawaye suka taru a cikin idanunta. Ta kasa jurewa se da ta buɗe baki ta saki ƙara tana sake juyawa.

Yana zaune kan dadduma, ya idar da sallah kenan yana addu'a, se ƙarar da ta yi ta sauka a cikin kunnensa. Da ma ba tun yanzu ba yake ɗan jin kamar sauke numfashi. Se dai be ɗauka da gasken ba ne se yanzu da ya jiyo ƙararta. Se ya miƙe a nutse ya ƙarasa inda gadon yake, bayan ya yaye labulen dake zagaye da wajen. Tana cikin bargon dai har lokacin tana juyin kamar wata macijiya. Se ƙaramin kukan da take yi a duk lokacin da cikin ze juya. Haka kawai ya ɗan ji fargaba ta shige shi, ya sake kallan gadon ganin har lokacin ba ta fito daga cikin bargon ba. Se kawai ya kai hannunsa a nutse ya yaye bargon idanunsa a kanta, dan gane abin da ya sanyata kukan. Ita sam ba ma ta lura da yaye bargon ba, saboda zuwa lokacin cikin nata yafi ɗazu yi mata ciwon. Inda hannunta ke kai ya bi da kallo bayan ya ajje bargon a gefe. Ganin tana tattare cikinta ya sanya shi kallan kyakykyawar fuskarta da ta yi jazur ta cikin jan ƙwan fitila.

"Wayyo Allahna" ta faɗa wasu hawaye na zubo mata. Ita a ranta ta gama saɗɗaƙarwa mutuwa za ta yi, dan haka mala'ika kawai take jira a zare ran ta huta da ciwon cikin nan. Ɗan lumshe idanunsa ya yi dan daga tsayen nan dai da yake ya san babu abin da ze iya yi, dan haka kawai se ya nemi gefen gadon ya zauna. Ganin har lokacin dai akwai tazara a tsakaninsu ne ya sanya shi ƙarasa hawa kan gadon. A nutse ya kai hannunsa zuwa kan nata hannun da ke kan cikinta sannan cikin nutsuwa ya furta
Chapter 18 · 0% Book details