← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 122

Sashe 120

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kin gan shi Maama, daga fitowarsa har ya san abinci.. Ko da me yake ci?" Ya ƙare tsantsar farin cikin da yake ciki na bayyana a cikin muryarsa. Duka Mommah ta kai masa tana faɗin

"Ja'iri." A hankali Gwani ya miƙa hannunsa dan karɓarsu, dan shi kansa ya ƙagu ya ga yaran. Se da ya sake zame towel ɗin ya sumbaci goshin kowannensu kafin ya miƙa masa.

"Alhamdulillah!" Shi ne abin da Gwani ya sake faɗa yana kallansu, tsantsar farin ciki na bayyana a kan fuskarsa. Be ƙara minti 1 ba ya miƙawa Mommah yaran, dan su ma su samu damar ganinsu. Ta karɓa cike da farin ciki da kuma zumuɗin ganinsu a hannunta. Haka aka yi ta sanyawa yaran albarka, har zuwa lokacin da aka maida su su ma aka kwantar, musamman ma ɗan Didi da jikinsa babu ƙwari Sosai. Su ma masu haihuwar aka kai su ɗakin hutu.

"Wannan kam kamarsa ɗaya da Affan lokacin yana ƙarami." Ummeey da ɗan Lulu ke hannunta ta faɗa tana kallansa. Kallanta Mommah ta yi, abin da take ƙoƙarin ganin ta manta ya dawo mata. Ta girgiza kai murmushin nan da aka cewa ya fi kuka ciwo na wanzuwa a kan fuskarta. Ita da ta haifa kwata-kwata ba ta san ya yake ba a lokacin yarinta ballantana har ta kai ga ɗorarwa. Ba da ban akwai mantuwa ba, zuciyar mutum kuma ta musulunci ce ba, da babu abin da ze sa ta yafewa Mom.

Cikin ƙanƙanin lokaci haihuwar en biyun Mommah ya baza cikin dangi, har ma da abokan arziƙi.

.. "Abbansu ba zan iya haƙura ba.. Don Allah ka bar ni na je." Ammi da tun da ta ji labarin haihuwar en biyun nata ta kasa sukuni. Da ma tun da aka ce mata suna asibiti ta so zuwa, Abba ne yace ta bari tun da su Mommah suna wajen. Yanzu kam duk se ta kasa haƙuri, gaba ɗaya burinta ya tafi a kan ta je ta ga 'ya'yanta, ta kuma ga jikokinta. Murmushi Abba ya yi dan shi kansa yana so ya ga 'ya'yansa da kuma jikokinsa.

"Shi kenan je ki shirya ki fito mu je."

"Ina godiya Abbansu." Ammi ta faɗa tana murmushi. Lokacin da suka isa asibitin Lulu da Didi na ɗakin hutu. Bayan da Abba ya gama ganin jariran Ammi ce ta karɓesu ta riƙe a hannunta. Se take ji tamkar ranar da ta haifi su Lulu ne. Ƙaunar yaran na ratsa kowacce gaɓa ta jikinta. Abun kamar a mafarki wai yau ita ce ke riƙe da 'ya'yan Didi da Lulu. Lallai da ma aka ce idan da rai da rabo.

"Allah Ya albarkaci rayuwarku." Ta faɗa murmushi na wanzuwa a kan fuskarta. A hankali ta juya ta kalli en biyun nata da ke ta baccin wahala, duk sun yi zuru-zuru. Ƙwallar da ta ji a cikin idanunta ne ya sanyata saka hannu ɗaya ta ɗauke ta. Tausayinsu ya kamata, tabbas yaranta sun yi ƙoƙari, yau ɗin sun ƙara sanin tabbas sun girma.

"Allah Ya ƙara muku lafiya." Ta faɗa a hankali.

Cikin dare aka sallame su, bayan an ba su shawarar yadda za su kula da ɗan gidan Didi da be cika watanninsa ba. Haka suka ɗunguma zuwa gida cikin matuƙar farin ciki. Kai tsaye gidan Ammi aka wuce da masu jegon har ma da mazajensu da yau ɗin suke cikin farin ciki mara misaltuwa. Da ma tuni Ammi ta gama gyara inda za su zauna. Hakan ne ya sa kai tsaye can ɗin suka nufa.

.. "Ban taɓa kawo miki haihuwa a kusa ba Dear.. Se ga shi wai yau ɗin kin haihu.. Na kuma zama uba! Ikon Allah!" Areef ya faɗa dan tabbas abun ya ba shi mamaki ainun.

"Ni kaina ban kawo hakan ba." Didi ta faɗa tana gyara zamanta. Da sauri ya miƙe yana faɗin

"Zaman ne be miki ba?" Girgiza kai ta yi kafin tace bayan ta yi murmushin da ya fi kama da na yaƙe, saboda har lokacin ba ta dawo daidai ba.

"A'ah fa Babe.." Be yadda ba se da ya gyara mata zaman sosai kafin ya koma ya zauna, daidai lokacin da yake faɗin

"Yau na sake tabbatar da ƙaunar da ke tsakanin en biyu." Murmushi Didi ta yi tana tuna abubuwan da suka faru.

"Allah Ya raya mana, Ya ƙara miki lafiya ke da Babynmu." Ya faɗa yana hango fuskar Babyn da ya baro yanzu cikin ɗaki. Ɗan ajje numfashi ya yi kafin ya gyara zama yace

"Wato idan na tuna yanda auranmu ya kasance se na dinga mamaki sosai. Ikon Allah ne kawai ya haɗa mu, ban da shi babu wanda ya isa ya haɗa mu. Idan na tuna farkon ganinki da na yi da kuma yanda abubuwa suka soma faruwa tun bayan nan.. Ashe ban sani ba haɗuwa da ke ne silar zuwana gidanku. Da na haƙura da marin da Afaaf ta min da ban haɗu da ke ba. Se yanzu na gane ashe rashin haƙuri ma wataran yana da rana." Ya ƙare yana wani murmushi. Tura baki ta yi kafin tace

"Kai dear rashin haƙurin?"

"Ehh mana, ba gashi ya haɗa ni da ke ba." Ya ƙare cikin barkwanci. Dariya ta yi ita ma tana tuna yanda auransu ya kasance se ka ce shirin film.

"Bayan duk wannan se ga shi yau ɗin kin haifa min kyakykyawan yaro me kama da ni."

"Wai da kai yake kama?" Ta faɗa tana tura baki. Murmushi ya yi yana cizar gefen laɓɓansa yace

"Ehh mana, kar ki ce min ba ki gani ba?"

"Ni dai ban yadda ba ka min wayo.. Ni na gama shan wahalar kuma ka ce yana kama da kai.."

"Iyeeee!!" Areef ya faɗa hadda riƙe haɓa.

"Yana so ne ya nuna miki ya fi ƙaunata.." Ya ƙare maganar cikin salo na tsokana. Dariya ta yi tana kallansa saboda jin yadda ya yi maganar. Ganin yana gyara zamansa kamar me shirin kwanciya ya sanya ta faɗin

"Babe wai kwanciya za ka yi?" Ta faɗa tana kallansa sosai.

"Aou kora ta kike yi?" Waro idanunta Didi ta yi kafin ta marairaice fuska tace

"Ni ɗin wa?" Ta faɗa a marairaice. Se da ya gyara zamansa sannan yace

"Toh a nan zan kwana." Ya faɗa kamar irin da gasken nan.

"Babe..!" Ta sake faɗa dan ita da gaske ta ɗauka da gasken yake. Be san sanda dariya ta ƙwace masa ba saboda yanda ta yi maganar. Ya kai hannu ya lakuci kumatunta yace

"Ke dai ko Babe..? Wannan tsoron naki.." Se ya girgiza kai har lokacin da murmushi a kan fuskarsa. Bayan shuɗewar wasu mintuna ya danna kiran number Gwani. A ɓangarensu Gwani kuwa yana riƙe da hannunta ya ƙarasa da ita har kan gadon a nutse. Ya taimaka mata cike da takatsantsan ta zauna a kan gadon, ya gyara mata zaman sosai yanda za ta ji daɗi kafin ya nemi gefenta ya zauna.

"Sannu.." Ya sake faɗa a karo na barkatai. Murmushi kawai ta yi tana zuba idanunta a kan fuskarsa. Ya lumshe idanu yana sake buɗewa a kanta.

"Sannu.. Allah Ya miki albarka."

"Ameen." Lulu ta amsa a hankali har lokacin da murmushi ita ma a kan fuskarta.

"Kin yi ƙoƙari sosai Ƙalb, na san halinki, kwata-kwata ban yi tunanin za ki iya haihuwa da kanki ba.." Shagwaɓe fuska ta yi tana faɗin

"Me ne halin nawa toh?" Ta tambaya tana kallansa. Se dai ya yi murmushi kafin ya kamo hannunta ya buɗe baki ze yi magana, daidai lokacin wayarsa ta soma ƙara. Se ya maida dubansa kan wayar, ya kalli me kiran kafin ya ɗaga ya kara a kunne.

"Wai a nan za ka kwana ne?" Areef ya faɗa bayan ya kara wayar shi ma a kunnensa. Se da ya kalli Lulu da idanunta yanzu ke kan Babies ɗin da ke kwance suna bacci hankalinsu kwance. Idan ba ka san mutane biyu ne suka haife su ba, se ka yi tunanin daga mahaifa ɗaya suka fito, saboda kamanceceniya da suke yi.

"Ba ni minti 1 yanzu zan fito." Gwani ya faɗa, be jira Areef ɗin ya sake cewa komai ba ya katse wayar. Ya maida dubansa kan Lulu yace

"Ya kike jin jikin naki?" Ya tambaya yana kallanta. Ƙura masa idanu ta yi tana kallansa kamar wadda ta soma ganinsa yau. Shi kansa se da ya yi mamakin irin wannan kallan, har se da yace

"Ƙalb.." Sannan ta lumshe idanunta ta buɗe su lokacin da suka ɗan sauya kala.

"Subhanallahi! Me ya faru? Wani abun na damunki ne?" Ya tambaya cike da kulawa. Girgiza kai ta yi kafin tace

"Don Allah ka yi haƙuri.." Cikin rashin fahimta yace

"In yi haƙuri? Me kika min?" Ya ƙare yana kafe ta da idanunsa cikin son jin amsar da za ta ba shi.

"Me ya sa bayan duk abubuwan da na maka a baya, ka kuma ga hoton nan ba ka yi ko da yunƙurin rabuwa da ni ba?"

"Ni ba lusarin namiji ba ne.. Ke! Mu bar maganar nan, ba na so ki kuma tunata har abada. Ni na manta ta a gaba ɗaya rayuwarmu, ina so ke ma ki manta ta.. Abu ne wanda Allah Ya rubuta dole se ya faru, ya kuma faru.. mun kuma karɓi hakan matsayin ƙaddararmu.. Don haka kar in sake jin kin tuna wannan maganar.." Jinjina kai ta yi tana cigaba da kallansa. Tana jin yadda wutar ƙaunarsa ke sake ruruwa a cikin zuciyarta. Tabbas Gwani Affan mutum ne har da rabin mutum. Miji ne kuma da kowacce mace za ta yi fatan samun irinsa.

"Maza goge ƙwallar ki yi murmushi in gani.." Ya faɗa a nutse. Babu musu ta yi ƙasa da kai ta ɗauke ƙwallar tana jin murmushi na suɓuce mata. Dan ya sake kautar da maganar ma gaba ɗaya ya sanya shi faɗin

"Yanzu haka ina ji ina gani zan barku har na tsawon kwana 40?" Ya yi maganar a marairaice. Kallansa Lulu ta yi kafin ta sake yin murmushi, kafin ta kai ga cewa komai yace

"Don Allah a rage kwanakin su dawo 10.." Waro idanunta ta yi tana saka hannu a kan bakinta tace

"Kai Habibi kwana 10 fa?" Ɗage girarsa ɗaya ya yi kana yace

"Eh mana.. Ni zan cigaba da kula da ke ai.." Dariya Lulu ta yi kafin tace
Chapter 120 · 0% Book details