← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 122

Sashe 51

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Toh sannu ɗiyata kin ji? Allah ya miki albarka.." Ummeey ta faɗa tana murmushi. Se da ta je ta ajje albasar sannan ta wuce ɗaki. Kai tsaye banɗaki ta wuce ta wanke hannunta kana ta koma ɗakinta. Ba ta daɗe da zama ba ta jiyo sallamarsa cikin ɗakin. Ba ta yi tunanin ze shigo ɗakin da take ba. Se dai cikin ƙanƙanin lokaci se ga shi cikin ɗakin da alama da ma kai tsaye nan ɗin ya taho. Da sauri ta kalle shi lokacin da ya ida shigowa cikin ɗakin. Se ta ɗauke kanta tana tura baki can ƙasa tace

"Ko me kuma ya kawo shi ɗakin mutane.." Jin yanda take wani ƙunƙuni ya sanya shi yin murmushi yana girgiza kai. Se da ya nemi waje ya zauna sannan yace

"Juyo ki kalle ni.." Shiru kawai ta yi kamar ba ta ji me yace ba.

"Ohk ba za ki juyo ba?"

"Ai na ga dai ba ka ba ni wayarka ba.." ta faɗa a kan laɓɓanta. Sarai ya ji abin da ta faɗa, hakan ne ya sanya shi sake yin murmushi.

"Ni ma ba batun wayar ne ya kawo ni ba.. Juyo ki ji.."

"Ina ji." Ta faɗa ba tare da ta juyo ba. Se ya sauke numfashi sannan yace

"Amm anjima zan fita za mu je wata musabaƙa da za a gabatar In Sha Allah.. se zuwa gobe kuma da dare nake saka ran zamu dawo In Sha Allah saboda wajen ba kusa ba ne." Da sauri ta juyo ta kalle shi kamar wadda ta yi mamakin abin da ya faɗa. Se dai a zahiri ita tunani take kenan yau ɗin ze bar mata ɗakin ne ita ɗaya? Ita kaɗai za ta kwana ba ta jin motsin kowa? Tana shirin jin ta sare da lamaein se kuma cikin ƙanƙanin lokaci ta tuna gadon nan da ya hanata kwana tun da aka kawo mata shi idan ba ya gidan za ta iya hawa ta yi kwanciyarta ba tare da wata takura ba.

"Toh.." shi ne kawai abin da ta faɗa.

"Babu fatan alkhairi?" Ya ƙare yana aza mata kyawawan idanunsa. Se ta ɗauke kai kawai. Da ya bari sun cigaba da mutunci tun bayan wannan hoton. Amma ya zo ya ɓata hakan ta hanyar sumbatarta kamar ba Malamin Addini ba.

"Ka gaida gida toh." Yanzu kam se da ya yi dariyar wannan sakarcin na Lulu. Wai ya gaida gida? Wanne gida kuma bayan wanda yake ciki? Jin da ya yi dai da alama daga haka ba za ta sake cewa komai ba ya sanya shi miƙewa a nutse dab da ze fice ya juyo cikin kwantar da murya yace

"Ki kula da kanki.." Daga haka ya fice daga ɗakin. Se ta bi shi da kallo lokacin da ya gama ficewa daga ɗakin. Ga shi har ze je ya kwana a wani wajen amma har yanzu be bata wayar ta kira Didinta ba. Ta murguɗa baki kamar yana gabanta.

... Se bayan la'asar sannan Gwani ya gama shiryawa tsaff. Kamar ko yaushe cikin favourite shigar nan tasa ya shirya, ya yi matuƙar kyau kamar ko yaushe. Daidai lokacin da ta fito daga cikin ɗakin shi kuma yake da niyyar shiga. Se ta yi maza ta koma ciki. Se dai kafin ta gama komawa ya sanya hannunsa ya riƙota. Se gata ta dawo kusa da shi sosai.

"Ni ka sake ni.." ta faɗa tana ƙoƙarin fuzge hannunta. Riƙo hannun ya sake yi sosai kafin ya yi amfani da ɗayan hannun nasa ya riƙo ƙugunta. Se da ya sanya idanunsa cikin nata idanun sannan yace

"Zan tafi.." Kamar ba za tace komai ba. Se dai kuma burinta ya saketa, hakan ne ya sanyata faɗin

"Ai dai na ce ka gaida gida koh?" Ta faɗa tana ɗauke kai.

"Ba haka nake so ba.. Ki ce Allah ya tsare hanya.." ya yi maganar yana sake kawo kusanci a tsakaninsu har lokacin idanunsa a kan fuskarta. Ita dai ba wani addu'a da za ta masa. Ko ya manta wulaƙantatan da ya yi. A hankali ta ji yana sake matsar da fuskarta kusa da tashi. Idanunsa kuma na kallan jajayen laɓɓanta. Ba ta san lokacin da ta yi saurin cusa leɓenta na ƙasa cikin bakinta ba. Jikinta na soma rawa ta buɗe bakin da ƙyar tace

"Allah Ya kiyaye hanya, Ya tsare, Ya dawo da kai lafiya." Be san lokacin da wata dariya ta ƙwace masa ba. Se kawai ya saketa saboda yanda tsoro ya gama bayyana a tattare da ita. Duk kuma uban addu'oin nan da take jerowa ya san saboda yanda ta ruɗe ne, tana tsoron kar a sake maimaita abin da ya faru. Wata ƙatuwar ajiyar zuciya ta sauke wadda har se da ya jiyo sautinta. Ya sake kallanta yana kuma mamakin wannan tsoro nata.

"Ameen Ameen.." ya amsa da hakan yana ficewa daga ɗakin. Ta sake sauke wata ajiyar zuciyar tana sake mamakin halin Gwanin. Ashe da ma haka yake. Yanzu duk ya wani chanja kamar ba Gwani Affan na makarantarsu ba.

A tsakar gida ya tarar da Ummeey da Abeey dake shirin fita. A nutse ya ƙarasa cikin girmamawa yace

"Abeey ya jikin naka?" Murmushi Abeey ya yi sannan yace

"Ni fa na faɗa maka na riga da na warke.. babu abin da ke damuna, ka da ma ka kawo min maganar asibiti."

"Abeey ba dai ka san asibitin nan kawai." Gwani ya faɗa yana sake karantar yanayin Abeey. Shi ma dai a yanda ya gani kam kamar babu abin da ke damun Abeeyn. Saboda yanda jikinsa ya yi kyau sosai babu wata alama da ke nuna akwai abin da ke masa ciwo.

"Akwai haka ɗin ma.. Amma dai na warke."

"Toh Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana." Gwani ya faɗa har cikin ransa yana jin daɗin yanda ya ga Abeeyn.

"Ameen." Ummeey da ke gefe ta amsa da hakan.

"Za ka wuce ne?" Abeey ya tambaya.

"Ehh zan wuce Abeey.."

"Toh Affan Allah Ya tsare, Ya kiyaye hanya.. Se ka dawo. Bari na fita yara na jirana."

"Ameen Abeey.."

"A dawo lafiya." Ummeey ta faɗa tana kallan Abeeyn. Amsa mata ya yi da "Allah ya sa." Sannan ya fice daga gidan.

.. Tana idar da Sallahr isha'i ta koma kan gadon ta sake gyara shi tsaff. Ta karkaɗe shi tass sannan ta koma cikin wardrobe ɗinta. Yau ɗin wani daɗi take ji babu takura cikin ɗakin, ga shi kuma za ta kwana ba a ƙasa ba. Kasancewar babu Nepa ga kuma yanayin gari ya sanya ɗakin da zafi. Dan haka cikin jin daɗin rashin kasancewarsa cikin ɗakin ta shiga haska er ƙaramar fitilar cikin wardrobe ɗin. Wata ƙaramar riga mara hannu irin me zamammen wuyan nan da underwear ta ɗauko ta saka. Kasancewar duka ba su da nauyi ya sanya ta ji daɗinsu, dan ba su da takura ko kaɗan. Haka suke sakayau. Ko bi ta kan wani ɗan kwali ba ta yi ba ta koma kan gadon ta yi kwanciyarta da mifici a hannunta tana fifita. Duk da zafin da ake yi hakan be hana bacci soma ɗaukarta ba. Babu daɗewa kuwa wani nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita.

A hankali ya tura ƙofar ɗakin gaba ɗaya jikinsa a gajiye yake jinsa. Babu haske ko kaɗan cikin ɗakin kasancewar har lokacin babu Nepa. Se ya wuce toilet kawai, se da ya je bakin ƙofar sannan ya kunna fitilar wayarsa ya yi amfani da ita wajen shiga toilet ɗin ya yi wanka ko ze ji daɗin jikinsa. Kaya marasa nauyi ya saka riga mara hannu da kuma gajeren wando. Ko bi ta kan ɗakin da Lulu take be yi ba, dan yana da tabbacin yanzun ta yi bacci ne. Kuma ba ya son takura mata. Hakan ne ya sanya kai tsaye ya wuce kan gadon. Cikin drawer gadon ya buɗe dan ɗaukar maganin sauro ya kunna. Cikin ikon Allah kafin ya ɗago se ga hasken Nepa.

"Ma Sha Allah.." Ya faɗa lokacin da fankar ɗakin ta soma kaɗawa. Se ya rufe drawer ya ɗago dan kashe socket ya yi bacci, dan har wani lumshewa idanunsa ke yi saboda bacci da kuma gajiyar da ta tarar masa. Maganar da yake ƙoƙarin yi ce ta maƙale lokacin da idanunsa suka sauka a kan Lulu da ke baje kan gadon ta yi ɗaiɗai da alama baccin na mata daɗi. Kanta da babu ɗan kwali ya sa gashinta da ke a tsefe kuma ba a ɗaure ba ya warware a kan gadon. Fuskarta ta yi mugun kyau. Yayin da ɗan ƙaramin bakin nan nata ta wani cuno shi gaba kamar me shirin yin kuka. Gaba ɗaya fararen hannayenta a buɗe suke. Saboda rigar da ba ta da hannu, hatta farin wuyanta a buɗe yake har zuwa wajen da wuyan rigar ya fara. Underwear ɗin da ta saka kuwa gaba ɗaya ya tattare ya koma saman gwuiwarta, hakan ne ya sanya kyawawan madaidaitan fararan ƙafafunta suka fito. Ɗan runtse idanunsa ya yi yana jin yanda zuciyarsa ta harba da ƙarfin gaske. Wajen minti 1 idanunsa a rufe yana so ya kawar da abin da ya ɗarsu a cikin ransa. Se dai hakan ya citira. Ya ɗan buɗe idanun nasa da cikin ƙanƙanin lokaci suka ɗan sauya kala kamar ba na shi ba. Se ya sake sauke idanun nasa a kanta lokacin da yake sake jin wata kasala na rufe shi. Da ma ga gajiyar da ya yi, duk se ya ji kamar an masa wani mugun duka. A nutse bayan ya sake lumshe idanunsa ya buɗe ya ƙarasa kan gadon, ya nemi gefe ya zauna a kasalance. Hannunsa ya kai inda socket ɗin ɗakin yake ya kashe. Cikin ƙanƙanin lokaci ɗakin ya sake yin duhu kamar ɗazun. Ba ka jin komai se ƙarar fanka da ke ta aikinta.

MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO52*
Chapter 51 · 0% Book details