← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 122

Sashe 40

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tace in kawo miki waɗannan kayan ki saka.." Da mamaki Didi ta bi kayan da kallo, kayan da kallo ɗaya za ka musu ka san an kashe kuɗi wajen siyar su da kuma ɗinka su. Ba ta san dalilin da ya sa Mommahn tace ta saka ba, se dai kuma ba ta so ta zama me ƙalubalantar umarnin Mommahn. Hakan ne ya sanyata karɓar kayan tace

"Toh bari na saka.."

"Yawwah 'yata.. Idan kin gama shiryawar se ki fito ki ɗauki abincin ki kai masa zan ƙarasa shirya komai." Lumshe idanunta Didi ta yi, gane dalilin da ya sa Mommahn tace ta saka kayan. Ta sauke ajiyar zuciya tana sake jin raunin dake tare da ita na ƙaruwa.

"Toh." Shi ne kaɗai abin da ta iya amsawa Baba Atinen da shi. Daga haka ta fice. A hankali ta saukar da kanta kan kayan tana kalla kamar me son gano wani abu daga jikinsu. Ta kai wajen minti 2 a haka ba tare da ta yi yunƙurin yin komai ba, se kuma ta sake sauke ajiyar zuciya a karo na barkatai sannan ta shiga saka kayan jikinta a matuƙar sanyaye.

Tsayawa ta yi tana kallan kanta lokacin da ta ida saka kayan, wani irin kyau ta yi kamar wadda ta saka wasu kayan na daban da ba ta taɓa saka irinsu ba. Murmushi ta saki tana tuna er uwatta, a irin wannan lokacin ita kaɗai ke kallanta tace mata ta yi kyau ta yadda. Idan kuwa har Lulun tace mata ba ta yi kyau ba toh ta yadda da hakan ko da kuwa kowa ze ce mata ta yi kyau. Se dai yanzu kam ko da Lulun ba ta kusa ita da kanta ta san ta yi kyau. Hijab ɗinta ta ɗauka madaidaici ta saka, wanda shi ma ya yi matuƙar karɓarta.

Kamar ko da yaushe a hankali ta isa ƙofar ɗakin ta shiga knocking. Se dai ta ji shiru babu alamar za a zo a buɗe. Abun hannunta ta ajje a ƙasa ta saka hannu ta taɓa ƙofar ɗakin. Ga mamakinta se ta ji ta a buɗe se dai ƙofar a jaye take. Kamar ta bar abincin a wajen, se kuma ta tuna wani abu dan haka kawai se ta saka hannunta a kan ƙofar ta tura cikin kula. Idanunta ta fara kaiwa cikin ɗakin dan ganin ko yana ciki? Cikin sa'a kuwa ba ta hangi kowa ba. Don haka se ta dawo ta ɗauki abinciccikan da suka dafa ta shigar da su cikin ɗakin inda ya kamata. Se ta shiga wuwwurga idanunta ko za ta gano wani abun da be dace ba ta yi maganinsu. Cikin sa'a kuwa se ga wasu kwalaben guda biyu a kan mirror se sheƙi suke alamar a sanyaye suke.

"Ya ilahy.." ta faɗa a sanyaye cikin ranta tana mamakin shi kam wane irin musulmi ne shi? Wane irin mutum ne shi? Wace irin halayya ce da shi haka? Shin ba ya tunanin ze mutu ne? A nutse ta ɗan lumshe manyan idanunta sannan ta buɗe su still a kan mudubin.

"Allah ka taimake ni.." ta faɗa bayan ta runtse idanunta. Se da ta buɗe idanun sannan ta shiga ƙarasawa a hankali zuwa wajen ta saka hannunta ta kwashi guda biyun, ta juya da niyyar ficewa daga cikin ɗakin, daidai lokacin shi kuma ya buɗe ƙofar toilet ɗin ya fito daga ciki. Jin motsin buɗe ƙofa da ta yi ne ya sanya ta dakatawa daidai lokacin da ƙirjinta ya buga da ƙarfin gaske. Ba ta san lokacin da ta saki kwalaben a ƙasa ba saboda tsananin firgicewa, cikin ƙarfin hali kuma ta ɗaga kai dan ganin motsin abin da ta ji. Ƙarar fashewar kwalaben da ya ji shi ne ya ankarar da shi wanzuwar wata halitta cikin ɗakin. Ya zame towel ɗin da yake tsane jiƙaƙƙiyar sumar kansa da ta kwanto har kan fuskarsa yana ɗaga fararan idanunsa zuwa inda Didi take. Daidai lokacin da ita ma ta kalli inda yake. Cikin lokaci ƙanƙani fuskarsa ta haɗe tsaff, se ya ida sauke towel ɗin yana sake kallanta cikin matuƙar mamaki. Ɗaure yake da towel daga kan ƙugunsa, ya yin da fafffaɗan ƙirjinsa ke a buɗe. Wanda kasancewar babu wani abu da ya saka dan lulluɓe shi ya sanya kwantacciyar tulin jiƙaƙƙiyar gargasar dake kwance muraran a kan ƙirjinsa ta gama bayyana kanta. Ta yi lankaf a kan farar fatarsa. Murɗaɗɗen jikinsa me kyawun gani da ɗaukar hankali ya fito fili. Tun da Ammi ta haifeta ba ta taɓa ganin namiji a irin yanda ta ga Bad Man ba. Cikin tsananin ruɗewa da gigicewar da ta haɗar mata da tsoron da ta ji ɗazun ta runtse idanunta da ƙarfi lokacin da ta fasa ƙarar rashin sanin mafita, lokaci ɗaya kuma tana zamewa a kan ƙafafunta lokacin da jikinta ya ɗauki rawa. Ita ba ma ta san kwalaben da ta yar sun fashe ba se da ta ji ƙafarta ɗaya ta taka wani abu me shegen zafi da tsini..

MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO45*

____Runtse idanunta ta yi da ƙarfin gaske lokacin da ta ji shigar kwalbar nan cikin ƙafarta. Ta shiga juya kanta har lokacin idanunta a rufe cikin rashin sanin abin yi.

"Inna lillahi.. wayyo Allah na.." shi ne abin da take faɗa cikin tsananin jin zafi da kuma haɗewar tsoron da ta ji da ta ga Bad Man, hannunta na riƙe da ƙafar tata da cikin lokaci ƙanƙani jini ya fara zubowa. Wani irin gumi ke kwaronyowa tun daga kanta har ƙafarta, ita kaɗai ta san me take ji, ban da juya kai babu abin da take yi.

Idanunsa ya sake buɗewa yana kallan kwalaben da ke zube a ƙasa abun cikin su ma a ƙasa. Wata zazzafar iska ya fesar daga bakinsa fahimtar tabbas wannan ɗin giyar da ya fito da ita ne ze sha ita ce yake gani a ƙasa.

"Wayyo.." Abin da ya ji Didi ta faɗa shi ne ya sanya shi ɗaga ido ya kalli inda take. Cikin lokaci ƙanƙani ransa ya ɓaci. Kaff cikin gidan nan babu wanda ya san yana shan wani abu, yanzu ga shi ita ta zo ta gano shi. Lallai dole ya karta mata warning.

"Kee!!" Ya faɗa fuskar nan ba annuri. Sam ba ma ta ji shi ba ita gaba ɗaya a tsorace take da yanda ta ga jini na cigaba da zubowa daga ƙafarta.

"Keee!" Ya sake maimaitawa a karo na biyu. Se a lokacin ma ta tuna a inda take. Se ta soma ƙoƙarin miƙewa dan ficewa daga ɗakin tun kafin ma ya fahimci abin da ya kawo ta wajen. Ba tare da ta kalle shi ba ta yi nasarar miƙewa a kan ɗayar ƙafar tata, ya yin da take riƙe da ɗayar. Fuskarta gaba ɗaya ta cika da hawaye caɓa caɓa. Cikin kula ta soma takawa dan ficewa daga ɗakin tana yarfe hannayenta a tsorace. Tsaki ya ja yana ɗan cije lips ɗinsa, duk da ya lura da jinin da ke a ƙasa hakan be sanya shi jin tausayinta har ya kai ga taimaka mata ba. Se dai a lokacin da ya ɗaga kai ze yi mata warning ɗin saboda fahimtar da ya yi ta gama ruɗewa se idanunsa suka yi tozali da yanda jinin ya cigaba da zuba a inda duk ta sanya ƙafarta. Iska ya fesar daga bakinsa kamar me tunani, se kuma can ya shiga takawa gaba.

"Kee!!" Ya faɗa yanzun cikin er ɗaga murya da kaurin murya. Ba ta san lokacin da ta tsaya ba tana runtse idanunta, shi kenan ita kam yau tata ta ƙare. Ga wannan uban ciwo da ta ji ga kuma ɓarnan da ta masa.

"Nemi waje ki zauna." Ya faɗa yana tsareta da idanunsa. Ita kanta ma a wani wajen yake dan haka har yanzun ba ta ɗaga ido ba balle ta kalle shi. Se dai kamar yanda yace mata ɗin se ta koma ƙasa kawai ta zube a wajen tana jin wasu hawaye na taho mata. Be sake cewa komai ba se komawa cikin ɗakin da ya yi. Bayan wajen minti 1 ya dawo inda take. Ita ta yi tunanin ma ko wani abun hukuncin ya tafi nemowa dan haka har ta gama saddaƙarwa, ta kuma rabu da zugin da ƙafarta ke yi mata. Ba tare da ya kalleta ba yana zuwa kawai ya sanya tattausan tafin hannunsa ya kama ƙafarta da ke da ciwon. A zabure ta ɗaga kai ta kalli ƙafar jikinta na ɗaukar wani rawa. Se ta soma ƙoƙarin janye ƙafar tata, shi kam ya haɗe face waje ɗaya babu alamun wasa. Babu ɓata lokaci ya shiga naɗe ƙafar da bandage duk da har lokacin Didi ba ta bar ƙoƙarin fuzge ƙafafunta ba. Hannu ta kai da niyyar ƙwace ƙafarta. Ya ɗago idanunsa ya watsa mata wani kallo da ya sanyata saurin janye hannunta lokaci ɗaya tana share hawayen da ke ta reto a kan kuncinta. Be saki ƙafar ba se da ya naɗeta tass sannan ya saketa. Ta sauke wata ƙatuwar ajiyar zuciya tana ƙoƙarin miƙewa, se ganinsa ta yi yana ƙoƙarin haɗe tazarar dake tsakaninsu. Ƙirjinta ya sake bugawa, wani irin tsoro ya ziyarceta. Er tazara kaɗan ya bari a tsakaninsu sannan yace lokacin da ya ɗora gaba ɗaya idanunsa a kan fuskarta.

"Saka idanunki cikin nawa.." Ya yi maganar cikin bayar da umarni. Sam ba ta da niyyar yin hakan, se ma ƙoƙarin tashi da take son yi ta gudu, se dai a yadda ya matso dab da ita idan dai har ba ta ɗaga idanu ta kalle shi ba toh se dai ta kalli gangar jikinsa da har yanzun take a buɗe. Mafita ɗaya ta rage mata shi ne ta saka hannu ta riƙe ƙafar tata me ciwo sosai sannan ta soma ƙoƙarin tashi da sauri. Hannunsa ya saka ya riƙo hannunta da ƙarfi har se da ta runtse idanunta. Ya sake watsa mata wani kallo sannan yace
Chapter 40 · 0% Book details