← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 122

Sashe 4

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Idan shi ya gane, ai ni ban fahimta ba. Me kake so kace ne? Wallahi har yanzu na kasa gane abin da kake nufi da ɗana.." Mom ta faɗa tana ji kamar ta saka ihu.

"Waye mahaifin Areef..?" Daddy ya faɗa yana kallan Mom.

"Kai ne..!!"

"Toh na ɗaura masa aure. Period.." Daddy ya faɗa a ɗan fusace yana dakatawa. Se kuma ya ɗora da

"Za ki iya fice min daga ɗaki.."

"In je ina? Babu inda zan je se ka tabbatar min da gaske wannan abun da kake faɗa."

"Tabbatarwa kike buƙata? Toh ki jira ranar juma'a za ki tabbatar.. Kada ki sake furta mun komai cikin ɗakin nan, idan ba haka ba wallahi zan saɓa miki.." Shiru Mom ta yi tun bayan da Daddyn ya gama magana. So take ta ƙara cewa wani abu, amma kuma ba ta so ta kai Daddyn bango. Hakan ne ya sanyata kallan Bad Man daidai lokacin da yake faɗin

"So da gaske aure ka min Daddy? Se kace wasan yara?" Ya faɗa sanda jijiyoyin kansa suka tashi har a kan goshinsa. Idanunsa suka sauya kala, haka zalika muryarsa ma se da ta sauya, sannan kuma yana kallan Daddyn ne cikin ido dan sake tabbatar da abin da yake faɗa ɗin.

"Areef.. Kada ka biyewa mahaifiyarka, ka yi ƙoƙarin ƙuntata min ko kuma bijire min. Kai ba mace bane ballantana ka yi tashin hankali dan na aura maka yarinya."

"But kana magana ne fa a kaina Dad.. Ta yaya zan yi shiru?" Ya yi maganar sanda ya kai hannunsa kan kujerar dake gefe ɗaya ya yi watsi da duk wasu abubuwa da ke kai. Nan take suka zubo daga kai, waɗanda suke na glass suka tarwatse a wajen. Be haƙura ba ya ɗan runtse idanunsa sannan yace

"Meye wani aure? Meye amfaninsa? Har ka yi min shi without my knowledge.. phhuuuu.." ya ƙare yana fidda wata zazzafar iska daga bakinsa.

"Hey Areef.. Kada ka manta wanda kake tare da shi.." Daddy ya faɗa yana kallansa, yana riƙe kansa dan kar ya mare shi.

"Ko kuwa dai kamar yanda Mom ke tunani u're just joking.." ya faɗa yana buɗe idanunsa a kan Daddyn.

"Wait and see.."

"Till when..?" Ya yi saurin katse Daddyn da faɗar hakan. Shiru Daddy ya masa kamar be ji abin da ya faɗa ba. Yana shirin sake cewa wani abu Daddy yace

"If u dare say something again, I will definitely deal with u wallahi.. Get out.." ya faɗa yana nuna masa hanya. Mom dake zaune har lokacin bata sake cewa komai ba, ta kalli Bad da har lokacin huci yake fitarwa.

"Dad.." ya faɗa da ɗan ɗaga murya.

"I said get out.." Daddy ya faɗa ba tare da ya kalle shi ba. Juyawa ya yi a fusace, ya sake dukan wani glass dake gefensa da ƙarfin gaske. Nan take ya fashe lokaci ɗaya kuma jini na soma zuba daga hannunsa. Duk kuma da hakan, be damu ba, be kuma bi ta kan hannun ba ya cigaba da takawa se dai yanzun cike da sassarfa, farar fuskarsa ta haɗe waje ɗaya ta sake yin ja, haka zalika idanunsa ma sun yi ja kamar waɗanda aka watsawa garwashi. Cikin sauri Mom ta miƙe tana faɗin

"Na shiga uku ni Salma.." ta faɗa tana bin bayan Bad da ya hau haɗaɗɗen step ɗin dake cikin ɗakin. Cike da kuzari yake haɗa step har zuwa sanda ya gama hawa, kawai ya faɗa cikin wani ɗaki. Mom ba tayi ƙasa a gwuiwa ba wajen bin bayansa. Runtse idanu Daddy ya yi bayan tashin Mom daga wajen. Dama kowa akwai tasa kalar ƙaddarar, shi kuma ɗansa ne ƙaddarar tasa. Duk da yanda yake ƙoƙari da jajircewa wajen bawa Areef ɗin tarbiyya da sakawa rayuwarsa ido, da tsawatar masa a kan duk wani abu da be dace ba, hakan be sanya shi zama kamar kowanne ɗa da uba ze yi alfahari da shi ba. Be zama cikin 'ya'ya masu biyayya ba, se me jayayya dasu, me kuma iya maida musu da martani. Ba dan shi ɗin tsayayye bane, gefe ɗaya kuma yana haɗawa da addu'a, da be san yanda zata dinga kayawa tsakaninsa da Areef ɗin ba. Se dai yana fatan wannan auren ya zamo sanadiyyar shiryuwarsa. Ko kuma Allah ya kawo wata hanyar da za ya gyaru ya zama mutumin arziƙi wanda kowa ze iya alfahari da shi.

"Allah ka shiya min yaron nan.." ya faɗa a hankali kuma a sanyaye.

... A ɓangarensu Twins kuwa tun bayan da kowaccensu wahalallen bacci ya ɗauke su, basu farka ba se bayan shuɗewar wasu awanni sannan Lulu ta soma buɗe jajayen idanunta da suka kumbura kamar wadda ta yi fama da ciwon ido. Ɗakin ta shiga bi da kallo kamar wadda ta ta soma ganinsa a yau ɗin. Tamkar wadda ake faɗawa se ta shiga tariyo duk abin da ya faru. Ƙirjinta ya buga da ƙarfin gaske, kada dai ace ba mafarki take yi ba? Juyawa ta yi ta kalli Didi dake gefenta tana bacci, tana sauke numfashi a hankali, wanda hakan ke nuna mata tana bacci ne cikin kwanciyar hankali. Ashe mafarki take yi bata sani ba? Se ta lumshe idanunta, se dai duk da yadda ta fahimci mafarki take yi hakan be sa jikinta dake a sanyaye komawa daidai ba. A hankali ta sauko daga kan gadon daidai lokacin da Ammi ta shigo cikin ɗakin

"Kin tashi?" Ammi ta faɗa tana kallanta. Ba ta yi tsammanin ma Lulun zata iya faɗin wani abu ba saboda tashin hankalin ɗazu amma se ji tayi tace

"Ehh Ammi.." Cikin matuƙar farin ciki da fatan shiryuwar ɗiyar tata tace

"Toh ki watsa ruwa a jikinki za ki ji daɗi sosai.."

"Tohm.." ta amsa da hakan tana shigewa cikin toilet ɗin lokaci ɗaya tana sake tuna wannan mummunan mafarkin da tana tunanin da bata tashi daga shi ba dab zuciyarta take da bugawa, mafarkin da ke ƙoƙarin yi mata shamaki da farin ciki na har abada. Babu daɗewa ta fito daga toilet ɗin tana mamakin yanda idanunta suka kumbura, duk da yanda zuciyarta ke son hararo mata kamar abin nan da ya faru gaskiya ne, hakan be hanata dannewa ba, tana sake ƙaryata kanta da kuma sake tabbatarwa da kanta cewar mafarki ne ta yi. Babban abin da yasa ta sake yadda mafarkin ne shi ne yanda ta ji babu wanda ya sake yin maganar, daga Ammi har Abba. Ita dai Didi se ta zama tamkar mara lafiya, miskilancinta ya ƙaru, se dai ta nemi waje kawai ta zauna ta yi shiru, tana tunanin makomarsu ita da er uwarta.

... "Didi Abba na kiranku.." Little ya faɗa tun kafin ya ƙarasa shigowa cikin ɗakin.

"Tohm.." suka amsa a tare suna miƙewa. Tare suka fito daga cikin ɗakin zuwa parlour, inda Abba da Ammi ke zaune. Suka ƙarasa suka nemi waje suka zauna a ƙasa.

"Abba ga mu.."

"Yawwah.." Abba ya amsa da hakan yana gyara zamansa. Se da ya ɗan yi gyaran murya sannan ya soma faɗin

"Kamar yanda na shaida muku ne tun ranar farko, toh yau ma zan maimaita muku, na ɗaura muku aure.. Se dai wannan kiran ya sha banban da wancan, dan kuwa wannan ɗin ina so ne na sanar daku cewar gobe idan Allah ya kai mu za a ɗauki kowacce a miƙata gidan mijinta.. Ina fatan ba zaku bani kunya ba, za kuma ku nuna irin tarbiyyar da muka muku.. Ke Afrah bana jinki hakan ne ma yasa ban damu da sanar dake ko waye mijin naki ba, duk da dai baki san shi ba, amma na san gobe zaki san shi idan Allah ya yadda.. Sunansa Areef.. Ke kuma Afaaf ina saka rai a kanki, ko dan faɗan da zan muku, don Allah kar ki zubar min da mutunci.. kar ki nuna bamu isa dake ba. Ki yiwa Allah da Annabinsa ki zauna da mijinki lafiya, kar in ji kar in gani. Affan yaron kirki ne In Sha Allah ze kula dake, ze riƙe amanar da na damƙa masa. Matuƙar dai zaki saukar da kanki ƙasa, ki kuma gane yanzun fa a ƙarƙashinsa kike.." Tunda Abba ya soma magana Lulu ke girgiza kai, ba tare da ta shirya ba, wasu zafafan hawaye suka soma zarya a kan fuskarta. Ashe ba mafarkin ta yi ba gaskiya ne komai? Gwani shi ne wanda Abba ke kiran ya aura masa ita. Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.. Da ƙyar ta iya buɗe bakinta ta soma faɗin

"Abba me na maka? Abba wane laifi na maka ka hukuntani da wannan hukuncin? Abba me yasa zaka min haka? Abba don Allah ka aura min kowane ne amma banda Gwani.. Abba ka min wannan alfarmar don Allah.." ta ƙare tana sakin wani sabon kuka. Ƙasa da kanta Didi ta yi itama hawaye na sakkowa daga cikin idanunta. Bayan duk waɗannan maganganun da Abban ya faɗa, da abubuwan da suka fi kama da roƙo gami da neman alfarma a wajensu, da wane ido zata kalli Abban tace wani abu a kan wannan auren da ya musu? Ta buɗe baki tace mene ne bayan tarin ƙaunarsu da Abban ke yi. Tun ba ma wannan ba, ko a iya roƙon da ya musu, da nuna ya isa dasu ɗin da ya yi ba ta ji zata iya furta komai bayan godiya, duk da yanda zuciyarta ke mata zafi.

"Me kika min kuwa Afaaf? Tsananin ƙaunarki da nake yi, da son inganta gobenki ya sanya ni aurawa Malam Affan ke. Ina kuma fatan ba zaki bani kunya ba.." da dai ta fahimci ba ta da wata mafita se karɓar Gwanin a matsayin mijinta ne ya sanyata faɗin, har lokacin bata dena kuka ba

"Abba ka sa shi ya sake ni, ka aura min koma wane ne don girman Allah.." Sauke numfashi Abba ya yi yana ɗan dafe kansa. A karo na barkatai ya sake ɗaga kansa ya kalli Lulun yace
Chapter 4 · 0% Book details