← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 122

Sashe 8

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ameen.." ya zura takalminsa yana wucewa ɗakin nasa. Ga mamakinsa yana buɗe ƙofar se ya sake ganinta tsugunne dai a wajen, ya bita da kallo yana mamakin abin da ya zaunar da ita a wajen haka. Se kuma be bi ta kanta ba kawai ya wuce zuwa cikin ɗakin. Kai tsaye toilet ya wuce, ya watsa ruwa me ɗumi kamar ko yaushe idan ze kwanta bacci. Sannan ya fito shirye cikin wata jallabiya daidai jikinsa wadda ta yi masa kyau duk da ba wata me tsada ba ce, sumar kansa da ba kasafai ya fiya barinta a buɗe ba se sheƙi take yi ya kwanta luff luff. Dadduma ya shimfiɗa ya shiga karatu kamar kowane dare. Ya shafe mintuna masu yawa yana yi sannan ya ajje Qur'an ɗin. Ya miƙe ya ninke daddumar kana ya hau kan gadon. Se a lokacin ya tuna da halittar dake zaune a bakin ƙofa, ya ɗaga kai ya kalleta, har lokacin dai tana zaunen kanta a kan gwuiwarta. Kamar ka da ya tankata, se dai ya san ko babu komai yanzu duk wata kulawarta na ƙarƙashinsa ne, hakan ne ya sanya shi ƙarasawa wajen, a hankali kuma cikin kaushin murya yace

"Tashi ki je ki kwanta.." Shiru ta yi kamar ɗazun dai duk da ta ji abin da ya faɗa ɗin. Se dai ita ko fuskarsa ma ba ta san gani ballantana maganarsa. Tsayuwarsa ya gyara kafin yace

"Kar ki bari na maimaita.." Ya yi maganar sanda ya ɗan ƙara matsowa kusa da ita. Jin maganar tasa a kusa da ita ne ya sanya ta ɗaga kai ta kalle shi. Wani kallo da yafi kama da na gargaɗi shi ya jefa mata, da sauri ta ɗauke kai tana murguɗa baki gami da huhhura dogon siririn hancinta.

"Ina ruwanka da ni?" Ta faɗa ƙasa ƙasa tana miƙewa tsaye ta koma gefe ta cigaba da tsayuwa.

"Ki..."

"Wai me ye haɗinka da ni ne? Ina ruwanka da inda zan kwanta? Ka rabu da ni mana a'ah.." ta yi saurin katse shi da faɗin hakan, duk da yanda wannan kallan kawai da ya mata ya hautsina mata 'ya'yan hanji. Amma duk da haka, kwaɓar zuciyarta kawai take yi ka da tun yanzu ta masa abin da ta san in dai ta yi dole ya saketa. Shi yasa jira kawai take yi gobe ta yi Mami ta dawo ta ji abin da za ta faɗa mata. Be ce komai ba ya koma kan gadon, ya ɗauki bargonsa da yake lulluɓa da shi me taushi, da pillow ya taho daidai bakin ƙofar ya ajje su. Sannan yace

"Wuce ki je.." ya faɗa yana tsareta da waɗannan idanun nasa masu shegen kwarjini da kyau. Gaba ɗaya se ta dibibice. Amma duk da haka ƙoƙarin sake bijirewa take yi, se dai har ga Allah ta ji tsoron yanda ta ji sautin muryarsa. Se dai duk da haka ba ta bar da kai bori ya hau ba, se ta ɗauki ƙoƙarin bin abin da ya faɗa ɗin da take yi a matsayin kawai dan tana jiran gobe ta yi ne. Ba dan haka ba kome ze mata se dai ya yi amma ba za ta ko da ɗaga ido ne ta kalle shi ba. Cike da sassarfa ta soma takawa zuwa cikin ɗakin, fuskar nan a ɗinke tsaff, ita a lallai dole kar ya rainata ballantana yace umarninsa ta bi. Hakan ne ya sanyata ɗan buɗe baki tace ƙasa ƙasa

"Dan dai dama ina da niyyar kwanciya ne. Ban da haka ba wanda ya isa ya min dole se na kwanta.. Ai dai na ga jikina ne.." ta ƙare tana hararar gefe. Sarai ya jita amma ko bi ta kanta be yi ba, ya shimfiɗa daddumar dake ajje a wajen kana ya hau kai ya zauna idanunsa a lumshe. Zuwa can ya buɗe bayan ya furzar da iska me ɗan ɗumi ba can ba. Yana kallan lokaci da take gyara zaman labulen da ya kare gadon ɗakin, ya ɗauke kai yana sakin ƙaramin tsaki zuciyarsa na masa wani zafi.

... Kallan ɗakin Mom ta cigaba da yi, duk da yanda Mommah ke da muguwar tsafta hakan be hana sashen nata nuna baƙi basu daɗe da watsewa ba. Mom ta jinjina kai tana yamutse fuska ta cigaba da takawa zuwa cikin ɗakin.

"Ohk.. yanzu dai kina nufin ki ce min da gaske har an kawo amaryar?" Mom ta faɗa tana kallan Didi da har lokacin take zaune kan kujerar kanta a ƙasa. Murmushi Mommah ta yi kana tace

"Wallahi kuwa.." Lallae kam se yau ta tabbatar da abin da Daddyn ke faɗa gaskiya ne. Babu shakka ya shammacesu, ya kuma wulaƙantata, ya wulaƙanta ɗansu ɗaya tilo. Yaro me ji da jini a jika, kyakkyawa ɗan ƙwalisa, wanda ke ji da ƙuruciya da kuma kuɗi, shi ne za a yiwa auren cushe, auren haɗi, auren dole, da yarinyar da be sani ba? Yarinyar da be san wace ce ita ba? Yarinyar da karon farko hatsaniya ce ta soma haɗasu, kafin kuma komai ya saitu har Daddyn ya ɗaura musu aure? Lallai akwai sake a wannan al'amari. Maida dubanta kan Didi Mom ta yi tace

"Toh ke se ki tashi mu yi gaba koh?" Kafin Didi ta kai ga ɗago kanta se ta ji Mommah na faɗin

"Ki yi haƙuri Hajiya.. Amma Yallaɓai be ce ta je ko ina ba.. Ya ce ta zauna anan har ya dawo, yana san ganinta ita da Areef ɗin.." Sheƙewa da dariya Mom ta yi tace

"Yau ni nake ganin ikon Allah.. Wato ke da baki haifa ba, ballantana ki aurar. An kuma haifa kina ƙoƙarin nuna iko da matar da ba ki da haɗi da ita. Me ye haka ne?" Mom ta ƙarasa a fusace. Se kuma ta ɗora da

"Ko kuma dai, idan ma ba za ki bamu yarinyar ba, ki cigaba da riƙeta anan ɗin. Ai ɗakin ki ba baƙon Areef bane. Ze shigo ne har nan ya bata takaddarta. Idan ya so in kin ji haushi a yau ki yi ciki ki haifi ɗa namiji ki aura masa yarinyar.." Runtse idanunta Mommah ta yi saboda yanda maganganun Mom ɗin ke saukar mata kamar mashi. Tabbas ta ji raɗaɗinsu matuƙa gaya, ta ji tamkar ta yi kuka ko za ta samu ta ji sauƙi a cikin ranta. Ina ma Allah ze azurtata da ciki duk da yanayin shekarunta da suka ja. Da tafi kowa farin ciki a rayuwarta. Se dai duk da hakan ma ko a yanzu tana godewa Allah a bisa ni'imomin da ya mata masu yawa.

Ita gaba ɗaya Didi ta gaza fahimtar abin da suke faɗa, ta kasa fahimtar inda zancen nasu ya dosa. Idan ma za tace ta gane, toh be wuce wasu abubuwa ƙalilan da ta gane a cikin maganganun nasu ba. Amma abin da ta kasa ganewa shi ne.. Ita wace ce a cikin gidan? Mene ne matsayinta? Wacce ce sirikarta a cikin waɗannan mata biyun? Waye ma shi kansa mijin nata da ake magana a kansa?. Wayarta Mom ta ɗaga ta soma kiran layin Bad Man ba tare da damuwa da yanayin da maganganun da ta faɗawa Mommah suka jefata ba. Se dai a karo na 2 ta sake gwada kiran nasa babu amsa. Se ta sauke ajiyar zuciya tana maida dubanta kan Didi tace

"K..." Kafin ta kai ga ƙarasa faɗar abin da ta yi niyya sallamar Daddy ta karaɗe cikin parlourn daidai lokacin da Mommah ke ƙoƙarin barin wajen, dan haƙiƙa maganganun Mom ɗin sun karceta da yawa.

"Sa'adatu.." Daddy ya faɗa yana kallan Mommah. Juyowa ta yi ta kalle shi daidai lokacin da ya sake faɗin

"Ka da ki je ko ina.. Dawo ki zauna.." Ba dan ta so ba, se dan bin umarnin Daddyn ta dawo. Ya nemi waje ya zauna. Ya kalli Mom ma yace mata ta zauna. Dukkansu zaunawa suka yi, ya kalli Didi dake zaune duk a takure yace

"Ɗiyata.." Zamowa ta yi daga kan kujerar cikin siririyar muryarta tace

"Barka da wannan lokaci.."

"Barkanki dai 'yata.." Daddy ya faɗa da murmushi a kan fuskarsa. Se kawai ta cigaba da zama a ƙasan, dan dama tafi jin daɗinsa, dan Mommah ta maidata kan kujerar ne ya sa ta zauna. Wayarsa ya ɗauko daga cikin aljihu ya danna kiran Bad Man. Dab da za ta tsinke ya ɗaga, cikin murya me kama da ta me bacci ya amsa kiran sunansa da Daddy ya yi.

"Ka zo parlourn Mommah.. Ina jiranka yanzu.."

"Bacci nake.." ya faɗa yana ɗan lumshe idanunsa saboda abin da ya gama sha yanzun nan.

"Ka zo dai na ce.." Daddy ya faɗa. Jin shiru ne ya sanya shi sake faɗin

"Ka ji?"

"E.." ya amsa a taƙaice yana kashe wayar. Sanye cikin ƙananan kaya riga da wando, dogon wando ne wanda ya ɗan tattare shi zuwa ƙasan gwuiwarsa, se riga me gajeren hannu wadda ta bayyana ƙaƙƙarfan damtsen hannunsa. Kansa babu hula se kwantacciyar sumar kansa dake a gyare kamar ta mace. Fuskarsa a cunkushe take sosai, sexy eyes ɗinsa sun sake lumshewa, wanda hakan ya ƙara musu kyau, da armashi, suka kuma ɗan ƙanƙance, sannan suka sake bayyanar da zallar kwarjinin dake tattare da shi.

"Zo ka zauna.." Daddy ya faɗa yana kallansa. Ƙarasawa kawai ya yi ya je ya zauna dan shi sam be ma lura da wata sabuwar halitta da ke zaune cikin ɗakin ba.

"Afrah.."

"Na'am.." ta faɗa a sanyaye.

"Areef.." Daddy ya faɗa yana kallan Bad Man da ya ɗan kifa kansa a kan kujera.

"Bacci kake ji ne?" Jinjina kai ya yi kamin yace yana ɗan dafe kan nasa.

"Yeah.. Na sha magani ne, ban san yana saka bacci ba.." ya yi maganar muryarsa a ɗan cunkushe. Da sauri Didi ta ɗaga kanta ta kalli me maganar, saboda yanda ta ji kamar ta san me muryar. Se dai tun a kallan farko, kafin ta ida kallansa ma ta sauke kanta tana girgiza kai. Saboda yanda ta ga halittar da bata taɓa gani ba, ballantana ta kai ga sanin muryarsa.
Chapter 8 · 0% Book details