Sashe 38
A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Who are you?" Bad Man ya faɗi hakan lokacin da ya ƙanƙantar da madaidaitan kyawawan idanunsa. Se a lokacin Gwani ya buɗe baki kamar ze ce wani abu se kuma ya fasa. Ya sanya hannunsa cikin aljihu ya fito da wayarsa. Ya yi danne danne na en wasu sakanni sannan ya miƙawa Bad Man yana kallansa. Yanayin shigar Bad Man ɗin kaɗai ta isa ta nuna maka ko dai shi ɗin ya kasance ɗan gidan wani shegen ne ko kuma shi kansa wani shege ne. Se dai duk da haka, hakan be sanya gwuiwar Gwani ta yi sanyi ba, be kuma sanya ya sassauta ko ya ƙasƙantar da kansa ba. Tunda har Lulun ta nuna masa shi a matsayin na jikin hoton ya ji ko mene ne ze faru se ya tabbatar ya ji gaskiyar lamarin. Ze kuma so ya samu Lulun matsayin me gaskiya. Cikin rashin fahimta Bad Man ya bi wayar da wani banzan kallo sannan ya maida kansa kan Gwani ya karkatar da kansa alamar "Mene ne?" Sake miƙa masa Gwani ya yi ba tare da yace komai ba. Yau ɗaya ya ji yana son sanin waye wannan ɗin, me kuma yake son nuna masa a waya? Shi ɗin da abubuwa masu muhimmanci ma ba tsayawa yake yi ya bi ta kansu ba, se ga shi ya miƙa hannunsa ya karɓi wayar hannun Gwanin. Kusan sakanni 10 ya ɗauka yana kallan hoton kafin ya ɗaga kai ya kalli Gwani.
"Me ye ma'anar wannan ɗin?" Ya tambaya cikin er basarwa. Gyara tsayuwa Gwani ya yi yace
"Me kake nufi da tambayar? Dalilin da ya sa ka saka aka ɗaukar maka hoton nake so na ji kafin na kai ga ɗaukar mataki.." Gwani ya faɗa kamar ba da Areef ɗan gidan Alhaji Matawalle yake tare ba, yake kuma yi wa magana ba. A mamakance Bad Man ke kallan Gwani, se ya sake maida dubansa kan wayar kamin ya girgiza kai, se ya koma jikin motar ya jingina yana tuna wannan ranar. Idan dai har be manta ba wannan ɗin Hero ne, ita kuma wadda ke jikin hoton ita ce wadda ke zaune cikin gidansu yanzu haka da suke kiranta da matarsa. Toh shi kuma wannan ɗin me ye haɗinsa da hoton kenan?
"Matata ce.." Gwani ya ba shi amsar tambayar da ya masa ransa a ɗan ɓace.
"Matarka..? How..? Oh dama matar aure ce? Waccan ɗin?" Ya yi maganar dukka lokaci ɗaya yana nuna Didi dake tsaye ɗan nesa kaɗan da su tana jira su gama maganar da za su yi. Kallan inda ya nuna Gwani ya yi se ya girgiza kai sannan yace
"A'ah.. er uwatta.." A'ah yanzu kam fa Bad Man kansa ya gama ɗaurewa. Me wannan mutumin ke nufi? Ita wannan ɗin ba ita ce wadda ta mare shi ba? Har ya je ramawa garin haka aka ƙaƙaba masa aurenta? Me kenan?
"Ba ka da abun faɗa kenan?" Gwani ya faɗa yana kallan Bad Man. Se a lokacin Bad Man ya buɗe murfin motarsa, ya shiga driver seat ya zauna gaba ɗaya ƙafafunsa a waje. Ya ɗan taɓe baki sannan yace
"Ba son maganar nake ba.. se dan son sanin gaskiya kawai.. En biyu ne?" Bad ya faɗa cike da mamakin dai. Waɗannan tambayoyin sun fara fusata Gwani, dan haka kamar ba ze amsa ba dan yana ganin ba su da amfani, se kuma yace
"Ehh.. se kuma me ye?" Iska ya fesar daga bakinsa kafin ya saki tsaki cike da takaici. Ashe ma wadda ta masa abu daban wadda ya je ɗaukar fansa kanta daban. Ya sake jan tsaki a karo na barkatai kafin ya buɗe baki kamar ba Bad Man ba ya soma faɗin
"Abokina ne wannan ɗin.. an samu misunderstanding ne.." Daga nan se ya faɗa masa abin da ya faru a taƙaice har lokacin fuskarsa babu yabo babu fallasa. Shiru Gwani ya yi na en wasu sakanni yana nazarin maganganun Bad Man ɗin. A zubin halitta be yi kama da wanda ze zauna ya tsaro shiryayyiyar ƙarya kamar haka ba. Be kuma yi kama da wanda ze yi ƙarya dan kare kansa ba.
"Ya za a yi na same shi..?" Gwani ya faɗa.
"Akwai abin da zan yi yanzun.. but ka bar ni da shi zan saka a kama shi.." Girgiza kai Gwani yace
"Na gode da hakan.. Amma ina son ganinsa ne da idanuna.. ina son jin dalilinsa na yin hoton, dan ba ze taɓa zama babu dalilin ɗaukar hoton ba.." Shi kansa Bad Man ya yadda da abin da Gwanin ya faɗa, musamman shi da ya san wane ne Hero. Ze yi wuya a ce babu wani dalili da ya sa aka yi hoton. Ɗan taɓe baki ya yi tunawa da ya yi dalilin hakan ne ya sanya shi cikin ruwa tsamo tsamo kamar ma shi ya aikata abin da Hero ɗin ya yi. Gwani dai ba su rabu da Bad Man ba se da suka yi exchanging contact, kafin Gwani ya masa sallama yana jin wannan nauyin da ya tokare ƙirjinsa na raguwa yana yin nasa wajen. Se da suka sake yin sallama da Didi sannan ta ƙarasa inda motar take tana mamakin abin da ya haɗa Gwani da kuma Bad Man ɗin har suka yi magana me tsawo irin wannan. Ni kaina yau har mamakin Bad Man ɗin nake yanda yake magana kamar ba shi ba, yanda ya saki jiki suka yi magana ta tsawon mintuna da mutumin da be sani ba, be ma taɓa gani ba.
Be jira ƙarasowarta ba se tayar da motar da ya yi, ganin hakan ne ya sanyata dakatawa dan be nuna mata inda za ta shiga ba, kar ta je ta yi shishshigi. Shi kansa ta ɓangarensa gani yake kamar yace mata ta shiga baya, saboda kar a yi tunanin ko ita ɗin wata tasa ce. Se dai kuma ya zama Drivernta kenan? Mafitar dai ɗaya ta shiga gaban, dan haka ya saka hannunsa ya tura ƙofar dake gefensa. Hakan ne ya sanya ta riƙowa ta shiga duk da a ɗarare take. Ta kame jikinta a nutse ta shiga ta zauna. Babu ɓata lokaci ya tashi motar suka fice daga cikin asibitin. Cikin lokaci ƙanƙani ƙamshin turarensa da sassanyan dake tashi cikin motar, da kuma nata me sanyi mara hawa kai suka shiga gogayya da juna. Se dai saboda daɗin ƙamshin turarensa mara hawa kai ya sanya ya danne kowanne, se ya kasance duk wata shaƙa da fitarwa da za ta yi se ta shaƙi ƙamshin me sanyi. Haka kuma idan ta tashi fidda numfashi se ta fesar da ƙamshin nasa. Tilas ta lumshe idanunta tana sake kama jikinta waje ɗaya.
... Daidai lokacin da yake shirin shiga ɗakin Ummeey ma ta shiga. Se ya yi murmushi yana faɗin
"Ummeey.."
"Ka shigo kenan? Sannu da zuwa" Ta tambaya bayan ta maida masa da martanin murmushin.
"Yawwah Ummeeyna.." ya amsa da hakan yana murmushi. Tare suka ƙarasa cikin ɗakin Ummeey ta nemi waje ta zauna tana kallan Lulu dake kwance tana bacci.
"Ina fatan su sallame mu saboda jikin nata ya yi sauƙi sosai.."
"In Sha Allah.." Gwani ya faɗa yana jinjina kai.
"So nake na je gida wajen abeeynka jikin ba daɗi ya masa ba.. se dai kuma ina so na ga farkawar ɗiyata.."
"Za ki mata wani abun ne?" Gwani ya tambaya. Girgiza kai Ummeey ta yi tace
"A'ah.. ka san dai har yanzu jikin nata be koma daidai ba, babu ƙwari sosai.." Cikin fahimtar zancen Ummeeyn ya jinjina kai kafin yace
"Haka ne.. Amma idan babu damuwa Ummeey ki je kawai.. zan kula da ita In Sha Allah.."
"A'ah Affan.." ta yi maganar tana kallansa. Se ya yi murmushi sannan yace
"Babu komai Ummeey.." Ajiyar zuciya Ummeey ta sauke kamin tace
"Toh shi kenan.. Allah ya ƙara mata lafiya, ya sa su sallame mu.."
"Ameen" ya amsa mata da hakan. Kafin ya shiga taimakawa Ummeeyn dan haɗa wasu kayayyakin da za ta tafi da su gida dan rage shirgi.
Neman waje ya yi ya zauna tun bayan fitar Ummeey daga ɗakin. Har bayan wajen awa ɗaya tana cigaba da baccinta. Se zuwa can sannan ta soma ƙoƙarin buɗe ido. Da sauri ya miƙe ya ƙarasa zuwa bakin gadon yana kallan fuskarta da ta yi fayau ta ƙara haske. Ganin tana ƙoƙarin tashi zaune tun kafin ta ida buɗe idanunta ya sanya shi miƙa hannu a nutse ya taimaka mata dan miƙewar. Ba ta jin komai a jikinta yanzu haka se abin da ba a rasa ba. Tana kuma da ƙarfin da za ta iya yin komai. Se dai har ranta ba ta kawo shi ba ne, ta ɗauka Ummeey ce kamar yanda ta saba taimaka mata ko da ta nuna ba ta so. Shi kam be ce mata komai ba lokacin da ta buɗe baki cikin magagin baccin da ya mata daɗi, wanda ta daɗe ba ta yi irinsa ba tace
"Banɗaki zan je.." Babu musu ya ƙarasar da ita zuwa banɗakin. Se da ya kaita sannan ya saketa yana shirin fitowa daga ciki ita kuma ta ida buɗe idanunta da niyyar ganin Ummeey. Se dai me? Se ganin mutum ta yi wanda ke shirin juyawa dan ficewa daga cikin toilet ɗin. A tsorace ba ta san lokacin da ta ƙwalla ƙara da iya ƙarfinta ba. Ganin mutum da ta yi a tsakiyar banɗakin dumu_dumu ba tare da ta ga fuskarsa ba. Cikin sauri ya sanya hannunsa ɗaya ya janyota, yayin da ya yi amfani da ɗayan wajen toshe bakin nata kafin ta ida kai ƙarshen ƙarar da ta soma. Ya ɗan matsar da ita cikin jikinsa lokacin da yake kai bakinsa saitin kunnenta yace a nutse
"Ki samu nutsuwa.. Ni ne.." ya yi maganar kamar me raɗa dai dai lokacin da ya runtse idanunsa saboda yanda ƙarar da ta saki ɗin ta ratsa cikin dodon kunnensa. Shi kam ya rasa se yaushe ne Lulun za ta girma...
Alhamdulillah! Mun gama azumi lafiya, Allah Ya sa mun yi ibada karɓaɓɓiya. Fatan kuma an yi sallah lafiya, Allah Ya maimaita mana, Ya sa muna da rabon ganin ta baɗi da rai da lafiya, Ameen. 🤗😍
MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO44*