← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 122

Sashe 17

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Da so samu ne har gidanta zan kai yaron nan. Se dai kin san yanayin ba ɗaya ba ne. Dan haka gwara a bari idan an kwana biyu se na kai shi ita ma ya ganta." Cike da gamsuwa da maganar Abban Ammi tace

"Haka ne.. Toh Allah ya tsare." Se da Abba ya amsa da "Ameen" sannan Ammi ta juya ta kalli Fatima dake tsaye nesa da su tace

"Yawwah toh zo ki wuce ku tafi.. Ki gaida min da Lulun" Murmushi ta yi kafin ta amsa da

"Toh za ta ji" Daga haka ta soma takawa. Little bakinsa ya kasa rufuwa saboda farin ciki, dan haka yanzun ma ko kula Ammi be yi ba se tsallensa yake. Se da suka kusa giftata sannan ta riƙo hannunsa tana faɗin

"Aou haka ne abun?" ta faɗa tana murmushi. Shi ma murmushin ya yi lokaci ɗaya yana faɗin

"Ammi mun tafi.."

"Toh se kun dawo.." Ammi ta faɗa tana ɗaga masa hannu. Kai tsaye compound ɗin gidan suka nufa, inda Abba tuni ya tayar da motarsa. Dan haka babu ɓata lokaci suka ƙarasa suka shiga. Abba ya tashi motar.

Har ƙofar gidan Abba ya kai su, ya yi parking motarsa sannan ya kalli Fatima yace

"Ku shiga ciki. Zuwa anjima In Sha Allah zan zo na ɗauke ku.. Ki faɗa mata takanas zan zo ganinta idan dai har ta kwantar da hankalinta da wannan auren."

"Toh Abba" Fatima ta faɗa tana buɗe ƙofar motar ta fita cike da zumuɗin son ganin masoyiyarta. Da sallama ta shiga cikin gidan, se dai a hankali kasancewar baƙon waje ne kuma ba ta ga fuskar kowa ba. Ummeey ce ta amsa mata sallamar. Ta yi murmushi duk da ba ta shaida fuskar ba tace

"Shigo mana.." Ita ma Fatima murmushin ta maidawa Ummeey sannan tace

"Ina yini?"

"Lafiya ƙalau.." ta ƙarasa maganar tana kallan Little da shi ma ke gaisheta. Se kawai ta ji yaron ya burgeta, musamman da ƙananun shekarunsa amma ya san ya gaida babba. Ta amsa masa tana haɗawa da tambayar sunansa.

"Areef.." ya faɗa a hankali.

"Sannu Areef ka ji?"

"Don Allah Afaaf nake tambaya.." Fatima ta faɗa da ɗan sarewa, dan har ta fara tunanin ko sun yi ɓatan kai ne. Murmushi Ummeey ta yi tace

"Tana ciki.." ta faɗa tana nuna musu ɗakin Gwani.

"Mun gode" Fatima ta faɗa da murmushi a kan fuskarta. Da sauri ta ƙarasa ta buɗe ƙofar ɗakin har lokacin hannunta na riƙe da na Little. Zaune take ruwan da da shi take rayuwa shi ne a hannunta tana sha. Se dai sallamar wadda ta ji ne ya sanyata saurin ɗaga kai dan tabbatarwa. Kamar a mafarki kuwa se ganin Masoyiya da Little ta yi tsaye bakin ƙofar. Wurgi ta yi da cup ɗin hannunta ta taso a miliyan ta ƙaraso inda suke. Babu ɓata lokaci suka rungume junansu Little na tsakiyarsu. Kawai se ta fashe da kuka cikin rashin sanin abin yi.

"Lulu me ye kike kuka? Dukanki aka yi?" Little ya faɗa yana goge mata hawayen. Kallansa ta yi ba ta san sanda ta yi murmushi ba tana sake rungume shi.

"Little.." ta faɗa cike da matsananciyar kewarsa. Shi ma rungumetan ya yi yana faɗin

"Ina Didi?" Ɗago shi ta yi tana kallansa, zuciyarta na komawa ga tunanin er uwarta da aka raba su. Ko yanzun tana ina? Se ta miƙe tana riƙe da hannun Little tace

"Taho.." Ta yi maganar tana jansu dukansu bayan ta riƙo hannun Fatima.

"Masoyiya.. Kin zo tafiya da ni ne koh?" ta tambaya tana kallan Fatima. Cikin mamaki Fatima tace

"Tafiya dake kuma? A'ah fa Abba ne ya kawo mu mu zo mu gan ki.." Kamar wadda aka tsikara ta miƙe da sauri tana faɗin

"Abbanmu? Yana ina?" Hannunta Fatima ta riƙo tana faɗin

"Ya tafi fa, yace ze zo ganinki idan kin kwantar da hankalinki a kan auren nan.. Masoyiya zo ki zauna me ya faru ne wai? Me kike magana a kai?"

"Gwani shi suka ce sun aura min.. Ni kuma ba zan iya zama da shi ba. Masoyiya tunda kin zo ki tashi mu tafi kawai.."

"Ban gane ba? Yi min bayani yanda zan gane wane Gwani?" Wata uwar harara Lulu ta jefa mata tana faɗin

"Wanne kika sani? Toh Affan.." ta faɗa tana ji kamar ta fasa ihu. Shiru Fatima ta yi tana cigaba da kallan Lulun, gaba ɗaya kanta ya kulle. Gwani kuma? Toh ta ya ya aka yi auren? Tunda dai ta san babu wanda ke son wani a cikinsu? Kenan ta ya ya hakan ta kasance?.

"Lulu nan gidan kika dawo?" Little ya faɗa sanda kansa ke ɗore a kan cinyar Lulu. Girgiza kai ta yi tace bayan ta ɗauke kanta daga kallansa.

"A'ah yau zan koma gidanmu.."

.. Hannunta Fatima ta kamo tace

"Ki yi haƙuri Masoyiya, haka Allah ya ƙaddara cewa mijinki ne. Ki yi haƙuri ki karɓi hakan, ki yi biyayya a kan abin da su Abba suka miki. Kin san da cewa ba za su taɓa yi miki abin da ze cutar dake ba saboda suna sonki.."

"Yanzu ba sa sona.." ta faɗa muryarta na rawa se dai a fusace. Murmushin yaƙe Fatima ta yi tana girgiza kai tace

"Sam ba haka ba ne Masoyiya.. Tsantar sonki da suke yi ne ya sanya su zaɓa miki Gwani a matsayin mi.. "

"Kee kin ga ya ishe ni haka. Ki rabu da ni, ki ƙyale ni.." ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa.

"Shi kenan amma dai ki dawo ki ci abinci.." Fatima ta faɗa tana kallan abincin da Ummeey ta aiko musu da shi.

"Ke ba zan ci komai ba..ko da kuwa zan mutu. Da ma na fi so a ɗauki gawata daga cikin gidan nan.." Ta faɗa a fusace tana kallan Fatiman, kuma abin da ta faɗa ɗin har cikim ranta tana nufin hakan. Dan kuwa ko yanzu ma yunwar take ji, amma taurin kai, da baƙar zuciya sun hanata cin komai tun zuwanta gidan.

"Lulu wannan fa ba maganar wasa ba ce. Ba maganar da za ki dinga ɗaukarta kamar wasa ba ne. Wannan fa ana magana ne a kan rayuwarki, rayuwar aurenki fa. An riga fa an ɗaura miki aure da Gwani, ina ganin kwantar da hankalinki ki karɓi auren nan a matsayin ƙaddara shi ne kaɗae mafita Lulu. Lulu don Allah ki zama me biyayya. Ki yi koyi da Didinmu mana plsss.." Fatima ta ƙarasa tana riƙo hannun Lulun. Fizge hannunta ta yi tana faɗin

"Idan kin san wannan maganar ce ta kawo ki don Allah ki tashi ki fita, ba na buƙatarki. Idan dai har ba zuwa kika yi ki ba ni shawarar yanda zan rabu da auren mutumin man ba toh ki ƙyale ni. Ki bar ni na yi abin da na ga dama. Dama na daɗe da cire ran wani ze taimake ni, tun lokacin da Mami ta ƙi taimakona. Dan haka ga hanya nan ki tashi ki tafi, amma ki sani nan da kwana biyu za ku zo ku ɗauki gawata.."

"Wai me ye haka kike faɗa ne masoyiya? Me ye haka ne wai?" Fatima ta faɗa cikin er ɗaga murya. Ko kallanta Lulu ba ta yi ba se miƙewa da ta yi ta barta a wajen a fusace. Dan ita sam ba ta ga amfanin zuwanta ba, kawai se ta ja Little duk da yanda zuciyarta ke zafi amma haka ta zauna tana jin hirar Little ɗin da ta yi missing nata. Ganin da Fatima ta yi sam Lulun ba ta buƙatar wannan hirar ya sanyata haƙura ta dena mata ita, sannan ta kuma yin iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta ci wani abun amma hakan ya citira. Dan firr ta ƙi cin komai se zaunawa kawai da ta yi tana kallansu su lokacin da suke cin abincin. Har Isha suna gidan, se da aka idar da sallah sannan Abba ya zo ɗaukarsu. Se da Lulu ta gama shan kukanta cikin ɗaki sannan ta samu damar fitowa daga cikin ɗakin har lokacin hannunta riƙe da na Little. Fatima ta miƙa masa hannu tana faɗin

"Zo mu tafi.. Za mu dawo.."

"A..ah" ya faɗa yana sake lafewa a jikin Lulu.

"Ka taho ka ji.. Abba na jiranmu.."

"A'ah.." ya sake faɗa yana kautar da kansa gefe. Hannu Fatima ta saka dan ɗaukarsa se kuwa ya fashe da kuka da ƙarfi yana riƙe Lulu. Ita ma kukan take ji, kawai basarwa take yi, dan ba ta ga amfanin yinsa ba a wajenta, ita da ta sallamawa rayuwa. Gwara ta sauƙaƙawa kanta, se dai kuma har cikin ranta ba ta san tafiyar Little ɗin. Ji take tamkar idan ya tafi ba za ta sake ganinsa ba.

"A'ah me ya faru? Kukan mene ne?" Abeey da fitowarsa kenan daga ɗaki ya faɗa yana kallansu. Kasancewar ɗazun sun gaisa ya sanya Fatima cewa

"Wai tafiya za mu yi shi ne ya ƙi yarda.."

"Toh a bar shi mana.." Abeey ya faɗa yana murmushi. Kallan Little ɗin da yaƙi kallanta ta yi sannan tace

"Ai Abba na waje yana jiranmu.."

"Toh mu je kawai.." Abeey ya faɗa yana yin gaba. Se da Fatima ta kalli Lulu ta sakar mata murmushi sannan tace

"Na tafi Masoyiya.. Allah ya baku zaman lafiya ya kaɗe fitina, ya gyara tsakaninku.." Wata banzar harara ta jefa mata manyan idanunta kamar za su faɗo, tana ɗauke kai ba tare da tace komai ba. Ita dai Fatima ba ta damu ba ta fito daga gidan.

.. "A'ah Malam da kanka?" Abba ya faɗa yana miƙawa Abeey hannu. Murmushi Abeey ya yi yace

"Toh ya za a yi.." Se da suka gaisa sannan Abeey yace

"Wato dama maganar wannan yaro ce Areef.. Me ze hana ka ɗan bar mana shi ya kwanar mana ko 3 ne, tunda dai ka ga yanzun haka ma kuka yake"

"A'ah Malam idan babu damuwa ka bari ko zuwa nan da sati ɗaya ne, ni da kaina zan kawo shi.."

"A'ah wannan kam alfarma ce nake nema, idan dai har za ta yiwu toh a yi min ita." Abeey ya katse Abba da faɗin haka. Ɗan karkatar da kansa Abba ya yi kafin yace

"Toh babu damuwa zuwa gobe se na wuto na ɗauke shi." Murmushi Abba ya yi yace
Chapter 17 · 0% Book details