← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 122

Sashe 100

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya Babyna? Fatan dai ba ya wahalar min da ke?" Yanda ta ji wani yamm da tattausan hannunsa ya taɓa fatar cikinta shi ne dalilin da ya sanyata saurin ɗora hannunta kan nasa. Tuni bugun zuciyarta ya ƙaru, burinta kawai ya janye hannunsa, musamman da suke cikin ɗakin da wani ze iya shigowa ya gansu.

"Kar wani ya shigo.." Ta yi ƙarfin halin faɗa tana sake riƙo hannunsa. Cikin basarwa yace

"Babu wanda ze shigo.. Ba ni amsata." Sake waiwayawa ta yi kamar me neman wani. Se dai da ta ga alamar ba shi da niyyar janyewa ya sanyata saurin faɗin

"Lafiya ƙalau." Se a lokacin sannan ya sauke hannunsa. Se gani ta yi ya zame a kan ƙafafunsa, ba ta yi tunanin komai ba, se binsa da kallo da ta yi dan ganin abin da ze yi, duk da yanda take ta ƙoƙarin basarwa amma kamar hakan na neman bijirewa. Soma matso da kansa ya yi a hankali har ya ƙaraso da shi kusa da ita. Maimakon ɗazu yanzu a kan rigar kawai daidai inda ya riƙe ɗazu ya sumbata yana jin wani shauƙi a cikin zuciyarsa. Ji yake tamkar yau ne yaron ze fito. Abin da ba ta tsammata ba kenan hakan ne ya sanyata kawai ta saki baki tana kallansa. Ita wallahi har yanzu idan ya yi wani abun ta kasa dena mamakin Gwani ne. Se kuma ta tura baki tana ƙoƙarin miƙewa ya yi saurin riƙo hannunta yana faɗin

"Yi haƙuri.. na tuba na bi Allah." Ya faɗa lokacin da ya gama miƙewa ya sake zama gefenta. Kamar ba za tace komai ba se kuma can tace

"Toh ina zuwa."

"A'ah kar ki min haka.." Ya faɗa a marairaice wai duk dan ta tausaya masa har da wani langaɓar da kai ya yi.

"Ai dai zan dawo."

"Kin yi alƙawari?" Ya katseta da faɗin hakan. Se ta jinjina kai tana ƙoƙarin miƙewa ya yi saurin saka hannu ya riƙo nata hannun.

"Rufa min asiri.. Yi a hankali." Ya yi maganar bayan ya ɗagota daga kan kujerar da kansa. Kawai se ta cigaba da kallansa kamar wadda ta soma ganinsa yau. Se ta cigaba da takawa zuwa ɗakin, ba ta san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba. Maganarsa ta ƙarshe ita ce ta sanyata murmushin hadda girgiza kai. Iska kaɗan ya fesar daga cikin bakinsa kafin ya gyara zama bayan ya sauke ajiyar zuciya.

"Ko dai na zo na tayaka hira ne?" Sam be lura da zuwanta wajen ba se muryarta da ya ji. Tana sanye cikin wata riga da wando masu kyau, duk babu wanda ya kamata a ciki. Ta yi kyau abinta, ta saka earpiece a kunnenta ɗaya, waya kuma ta riƙe da hannunta.

"A'ah babu buƙata." Ya faɗa yana ɗan wanzar da annuri a kan fuskarsa idanunsa na kan ɗakin da Lulu ta shiga.

"Ahh haba dai ai ko ya ya ne dai zama mutum biyu ya fi." Ta ƙare tana neman gefen kujerar ta zauna.

"Barka da wannan lokacin.." Ta yi amfani da faɗin hakan dan kawar da hankalinsa daga wani tunanin.

"Barka.. Akwai abin da za ki yi cikin ɗakin ne?" Ya tambaya, dan ba ya so ko kaɗan ya wulaƙanta wani ɗan adam. Musamman ma ita da take er uwa. Girgiza kai ta yi tana sauke earpiece ɗin kunnenta tace

"A'ah fa.. Wajenka na zo fa kawai." Ta ƙare tana murmushi. Daidai lokacin Lulu ta fito daga cikin ɗakin. Cikin sa'a se idanunta suka sauka a kan Iftihal dake zaune kusa da Gwani. Dakatawa ta yi daga inda take se dai har lokacin nan ɗin take kalla. Kamar wadda ake ja se ta cigaba da takawa zuwa cikin ɗakin. Murmushi Gwani ya saki yana kallan Lulu a nutse kuma cikin kulawa yace

"Sannu da dawowa.. Kin dawo kenan.." Ba tace komai ba Lulu se kallansa da ta cigaba da yi. Iftihal yi ta yi kamar ba ta ji me yace ba, ba kuma ta lura da wanzuwar Lulu a wajen ba, cikin basarwa tace

"Ko dai na haɗo maka tea ne? Na san za ka ji daɗinsa." Wani kallo Gwani ya watsa mata, dan kamar ya soma fahimtar da wata manufar take wasu abubuwan. Ƙirjinta ya buga saboda yanda kallan ya hautsina mata 'ya'yan hanji. Se dai ta sake basarwa ta miƙe kawai dan wucewa kitchen, dan ita babban burinta be wuce ta ƙonawa Lulu rai ba. Duk yanda Lulu ke kai zuciyarta nesa, da kuma yanda take ƙaryata kanta a kan ɓacin ran da take ji ba shi da alaƙa da Iftihal dake tare da Gwani amma hakan ya citira. Ta yi ta yi ta jure ta kaasa. Har wani tafasa zuciyarta ke yi. Yau ɗin tabbas Iftihal ɗin ta kaita bango ainun. Hannu ta saka ta riƙo mayafin Iftihal ɗin ta dawo da ita baya. Saboda Iftihal ɗin ba ta tsammata ba se gata ta dawo baya kamar za ta kifa. Se dai da Allah Ya tsare se ta tsaya a kan ƙafafunta. A fusace ta juya ta kalli Lulu, daidai lokacin da fusatattun kyawawan idanun Lulu ke kanta tana binta da wani banzon kallo. Har ba ta san lokacin da ta buɗe baki tana jin zuciyarta na cigaba da harbawa kamar wadda ta yi mugun gudu ta gaji, ta soma faɗin

"Ke wace irin mace ce mara aji? Wane irin abu ne kike yi haka babu kyan gani? Wani yace miki ana buƙatar wani abu ne daga gare ki? Za ki wani ɗauki tsumman ƙafafunki kin tafi aikin neman suna. Toh ki kama kanki, ki riƙe mutuncinki tun kafin kallan rashin ajin da nake miki ya ƙarasa rushewa gaba ɗaya." Da wani irin kallo Iftihal ke bin Lulu da shi, ba ta taɓa tunanin za ta iya tsayawa tana faɗa mata irin waɗannan maganganun a gaban Gwanin ba. Duk da dai tun kallan farko da ta mata ta san yarinyar ba kanwar lasa ba ce. Amma yanda ta ga ta iya shariya a kan abubuwa, yanda take nuna tamkar ba ta gani ba ko da ta gani kuwa, ya sa ba ta taɓa kawowa a wannan karon ma za ta nuna ta gani ba ballantana har ta tanka. Kunya da haushi suka taru suka haɗarwa Iftihal. Ji take kamar ta saka ihu ko za ta ji daɗi, dan ba shakka wannan yarfin ya shigeta.

"Ni kike faɗawa haka? Ni kike faɗawa haka?" Shi ne abin da Iftihal ta faɗa tana huci, ji take kamar ta kama Lulu ta yi wa shegen duka ko za ta ji daɗi. Se da Lulu ta sake bata wani kallan da ya fi na ɗazu muni kafin ta ja tsaki ta juya ta bar wajen. Dan tsabar takaici da baƙin ciki ita kam Iftihal ba ta sake cewa komai ba se ɗaukar ƙafafunta da ta yi a kunyace, ba tare da ta sake kallan inda Gwani yake ba ta wuce ɗakinta. Tun da ta soma magana yake kallanta har ta kai aya. Kai har ta juya ta shige ɗaki kallanta yake yi. Kawai ya kasa cewa komai, abubuwan da suka faru yanzu su kaɗai ke sake maimaita kansu cikin ƙwaƙwalwarsa. Idan dai har ya lura da kyau kamar kishi ne yake gani a cikin idanun Lulu fa? Kishi dai me suna kishi. Kishin ma kuma a kansa? Kenan hakan na nufin tana sonsa? Tun da dai ba a kishi se a kan abin da ake so. Toh kenan daga wanne lokaci hakan ta faru? Yaushe ta fara son shi amma be ankare ba? Shin abin da yake hasashe yake kuma gani a idanunta haka ɗin ne? Shi kam me ya kamata ya yi idan ba godewa Allah ba?.

... Ya kai fiye da rabin awa a tsaye ba tare da yana komai ba se kallan kwalabe guda biyun da gabansa, kamar wanda ke tunani ko kuma wani abun. Se can dai ya koma ya zauna yana cigaba da kallansu ban da harbawa babu abin da zuciyarsa ke yi, idanunsa sun sake ƙanƙancewa. Wane irin abu ne wannan? Sam ya kasa komai cikin lumana? Shin Mommah me take jira ya yi ne wanda ze sa ta gane ya yi laushi? Me take jira? Ya ya ze yi da wannan ɓacin ran da yake ji shi kam? Waɗannan abubuwan dake gabansa ya san yana sha ze ɗan ji sauƙi ko ya ya ne. Se dai ya kasa sha. Tun ɗazu suke gabansa amma ya kasa ko da ƙoƙarin ɗauka ne ya sha. Ya fesar da zazzafar iska daga bakinsa yana miƙewa. Ɗaukar bottles ɗin ya yi har lokacin bugun zuciyarsa be saitu ba. Ko me yake ji ze haƙura, tun da dai har mahaifiyar da ta haife shi ce ta ga hukuncin da ta yanke shi ne daidai ya haƙura. Ba ze sha wani abu ba, amma fa ko me ya samu zuciyarsa toh tabbas silar soyayyar Didi ne. A hankali ya soma takawa dan ficewa daga ɗakin da niyyar dubawa ko babu kowa dan ya fita ya je ya fasa su gaba ɗaya. Se dai a daidai wannan lokacin ne Didi ta shigo ɗakin da sallama ɗauke a bakinta cikin siririyar muryarta. Dakatawa ya yi yana kallanta cikin matuƙar mamakin ganinta. Ya zuba mata lumsassun idanunsa kamar wadda ya ga baƙuwar halitta. Se ya lumshe idanunsa dan tabbatar da da gasken ita ɗin ce ko kuwa idanunsa ne suka soma masa gizo. Tabbatar da da gasken ita ce shi ne ya sanya shi matsawa gefe ya ajje bottles ɗin yana juyowa inda take cikin maɗaukakin farin ciki. Daidai lokacin da ita kuma idanunta suka sauka a kan kwalaben. Wallahi ba ta san lokacin da abincin hannunta suka tarwatse ba. Cikin lokaci ƙanƙani kowanne ya yi nasa wajen. A take jikinta ya ɗauki rawa. Shin wannan wane irin ɗa ne? Shi kam wane irin miji ne? Wane irin uba kuma yake son zama? Yanzu duk yanda Mommah ta gama yabo da kuma fatan a ce ya dena har abada, wanda hakan ne ya sa ta aikota da kanta ashe be dena ba?
Chapter 100 · 0% Book details