← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 122

Sashe 39

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

___ Wata ƙatuwar ajiyar zuciya ta sauke wadda har se da ta fito fili lokacin da ta ji muryarsa cikin kunnenta. Se dai ta yi maza ta janye jikinta tana jin yanda bugun zuciyarta ke ƙaruwa, a lokaci guda kuma tana ƙoƙarin saita shi ya koma daidai. Be sake cewa komai ba se ficewa daga toilet ɗin da ya yi. Binsa ta yi da kallo lokacin da yake ficewa daga banɗakin. Tun jiya take jira ta ji ya yi mata magana a kan hoton nan amma shiru har yanzu. Dan tun jiya ma da ya fita ba ta sake ganinsa ba se yanzu. Cikin lokaci ƙanƙani ta ji ƙwalla ta tarar mata cikin idanu, se ta lumshe idanun tana jin wani rauni na zuwar mata.

... "Ko dai asibitin za mu je?" Ummeey ta yi maganar tana kallan Abeey. Murmushi Abeey ya yi kafin yace

"Zuwa asibitin nan ya isa haka.. ko zuwa wankin ƙodar nan ai ya ishe ni. Shi ma ɗin da da dama cewa zan yi a bar shi haka nan ai mun sha jar miya.." ya ƙare yana murmushi cikin kallan Ummeeyn. Ɓata rai Ummeey ta yi tace

"Kai dai ka na son maganar nan Malam.. don Allah ka dena.." Sake wani murmushin Abeey ya yi kana yace

"Toh shi kenan.." Daga haka ya sauke numfashi daga kishingiɗen da yake. Sallamar da aka yi cikin gidan ne ya katse Ummeey daga faɗin abin da ta yi niyyar faɗa. Se ta miƙe lokaci ɗaya tana faɗin

"Bari na leƙa na gani.." ta faɗa ba don tana buƙatar amsa daga wajen Abeeyn ba.

Sanye cikin atamfa da mayafi madaidaici wanda ta saka shi a wuya, ta riƙo jaka a hannunta. Jadwa ke gefenta ita ma sanye cikin atamfar se dai ita ɗinkin straight gown ne wanda ya bi lafiyar jikinta ya lafe.

"Gafaran ku dai.." Mami ta faɗa tana kallan cikin gidan a wulaƙance kamar ko da yaushe.

"Yawwah.." Ummeey ta faɗa lokacin da ta ƙaraso inda suke.

"Kuna ciki kenan? Ina Afaaf ɗin?" Mami ta yi maganar lokaci ɗaya.

"Ku shigo mana.." Ummeey ta faɗa fuskarta babu yabo babu fallasa.

"A'ah a'ah babu buƙata.. toh fa!!.." Mami ta ƙare maganar tana kallan Jadwa irin "Kin ji mun iyayi.." Jadwa ta taɓe baki ba tare da tace komai ba.

"Afaaf ɗin na asib.."

"Ko da yake ma dai na zo sake ganin ɗaki ne kawai saboda gobe da za a kawo kayan Afaaf cikin gidan nan.." Mami ta katse Ummeey da faɗin haka a yatsine.

"Ai shi ne nake faɗa miki Afaaf ɗin babu lafiya tana asibiti.. Idan kuma ɗakin kawai kika zo gani ga shi can.." Ummeey ta faɗa fuskarta babu yabo babu fallasa tana me nuni da ɗakin Gwani. Don sarai ta gane fuskar Mamin, ta kuma fahimci take_takenta na rashin daraja tun zuwanta na farko cikin gidan.

"Mami ki zo mu tafi don Allah.." Jadwa ta faɗa tana riƙo hannun Mamin.

"Kya bari dai in ji inda aka kwantar min da ɗiya koh?" Ta faɗa tana watsawa Jadwan harara, duk da gefe guda kuma ta tafi tunanin dalilin da ya sa Lulun ke asibiti. Kar dai daga kawo masa yarinya har ya ɗirka mata ciki? Idan kuwa haka ne lallai abubuwa sun kwaɓe musu. Kuma mamakinta ɗaya idan hakan ya kasance gaske da Lulun ta yi shiru ta ƙi faɗa mata kasancewar wani abu a tsakaninsu. Ko dai yaron nan ya juyawa Lulu ƙwaƙwalwa ne? Wata gauruwar ajiyar zuciya ta sauke tana jijjiga kai, a ranta tana sake ƙaryata hakan da zuciyarta ta ayyana mata.

"Allah ya sa dai wannan jinin talakawan be haɗa jiki da 'yata ba." Ta yi maganar a kan laɓɓanta.

"Let's go pls Mami." Jadwa ta faɗa a ƙage. Se a lokacin sannan Mami tace

"Ba ki ji me na ce miki ba ne?"

"Bayan wanda ta ba mu?" Jadwa ta faɗa tana kallanta. Taɓe baki Mami ta yi dan har ga Allah ba ta san lokacin da Ummeeyn ta yi magana ba saboda tunanin da ta faɗa. Saboda takaici ba ta san lokacin da ta ja tsaki ba tana jan hannun Jadwa suka fice daga gidan.

"Allah ya kyauta.." Ummeey ta faɗa tana komawa ɗakin Abeey.

... "Na shiga 3!! Daughter da gaske ba ki da lafiya? Me ke damun ki?" Mami ta faɗa da sauri tana ƙarasawa cikin ɗakin. Da sauri Lulu ta ɗaga kai ta kalli Mamin da tun kafin ta ƙaraso ta shaida muryar. Hannu Mami ta kai da niyyar taɓa Lulun, cikin sauri ta janye jikinta tana faɗin

"Kar ki taɓa ni.." ta faɗa tana matsawa sosai daga inda Mamin take. Da mamaki Mami ta kalli Lulun, wai an ya kan yarinyar nan ɗaya kuwa? Me ke damunta haka? An ya zuwanta gidan nan ba ta samu taɓin hankali ba?.

"Lulu.."

"Kar ki kuma kiran sunana.. ki fita a ɗakin nan ba na son ganin ki, ba na son ganin ki.." ta faɗa tana girgiza kai idanunta a kulle. Kallan Mami Jadwa ta yi cikin mamakin abin da take gani se dai ba tace komai ba.

"Lulu me na miki? Wa ye ya shiga tsakaninmu? Ko dai wannan tsinannen da aka aura miki ne?" Mami ta faɗa cike da fargaba. Da ƙyar idan ba abin da take tunani ba ne ya faru. Buɗe idanunta Lulu ta yi a kan Mami daidai lokacin da Gwani ya shigo cikin ɗakin. Se ta yi maza ta kalle shi lokacin da idanunta suka cika taff da ƙwalla tace

"Ka ce mata ta fita ba na son ganinta, ba na so.." ta faɗa tana nuna Mamin. Kallan Mamin ya yi a fuzge dan fahimtar wace ce ita. Idan dai har be yi kuskure ba wannan ɗin er uwarsu Lulun ce. Amma me ye dalilinta na cewa ta fita ba ta son ganinta? Se ya shiga takawa zuwa inda take a nutse, ya ƙarasa ya ɗan ranƙwafa a nutse kamar me raɗa yace

"Me ya faru?" Ya faɗa yana kafeta da idanunsa. Girgiza kai Lulu ta yi cikin takaici dan a yanzu ba ta buƙatar komai se ta buɗe ido ta dena ganin Mamin a gabanta.

"Ka ce mata ta tafi don Allah.. kar ta sake zuwa inda nake." Shi ne abin da Lulu ta sake faɗa wanda jin hakan da Mami suka yi ita da Jadwa ya saka su kasa furta komai saboda tsananin mamaki. Lumshe idanunsa ya yi a nutse yana buɗe su lokaci ɗaya ya buɗe baki ze yi magana se jin hannunsa ya yi cikin lallausan hannun Lulu daidai lokacin da ta sanya ƙwayar idanunta cikin nasa tace

"Don Allah.." ta faɗa wasu hawaye masu ɗumi na kwarayowa daga cikin idanunta. Bin hannun ya yi da kallo cikin matuƙar mamaki. Ya ɗan sake lumshe idanunsa saboda yanda ya ji wani abu ya tsirga masa musamman da be tsammaci hakan ba, kafin ya miƙe tsaye. Se a lokacin sannan ta saki hannun nasa. A nutse shi kuma ya juya inda su Mamin suke waɗanda zuwa lokacin sun yi mutuwar tsaye daga ita har Jadwan.

"Idan babu damuwa ki ɗan je pls, tace ba ta san ganin ki.." Wani ashar ne ya zo wa Mami cikin ranta wanda take ƙoƙarin fiddo shi zuwa kan bakinta dan ta nanawa Gwani shi, se dai ta gaza aikata hakan saboda tsananin mamakin da ya kusa kasheta a wajen. Riƙe hannunsa da Lulu ta yi, wani kallo da ta ga sun yi wa junansu ba ƙaramin tsorata ta yi ba.

"Mu je koh?" Gwani ya faɗa yana soma takawa. Kamar wata doluwa se kuwa Jadwa ta soma takawa dan ficewa daga ɗakin. Lura da ta yi Mami ba ta taho ba ne ya sanya ta saka hannu ta riƙo ta.

"Sake ni don uban ki.." Mami ta faɗa a fusace. Ko bi ta kanta Jadwa ba ta yi ba, kamar za ta fice daga ɗakin se kuma ta saka hannu ta sake riƙo hannun Mamin tana faɗin

"Wai Mami me ye haka ne? Ki mu tafi mana se korar mu ake yi.." Shiru kawai Mami ta yi dan a lokacin mamakin Lulu ya kusa kasheta. Wato ita tana nan tana yaƙi a kan nemo mata 'yanci ashe ita tana nan tana zaman lafiya. Har da wulaƙantata gaban wannan wulaƙantaccen talakan. Ga shi nan shi ma har ya samu dama wajen faɗa mata magana. Lallai da sake a lamarin nan. Se ta ja ƙwafa tana sake hura hanci kamar wata saniya. Ita dai Jadwa ta janye ta suka fice daga cikin ɗakin.

... Sun kwashe awanni fiye da 3 cikin kitchen ɗin suna girki wanda Baba Atine ta saki jiki ta ci ƙarfin aikin kamar yanda Mommah ta umarceta. Se dai da yake Didin gwana ce kuma ba ta da wasa se ya kasance kusan komai tare suka yi shi. Sosai aikin ya yi mata daɗi se dai wanda ake yi wa girkin ne idan ta tuna waye shi duk se ta ji jikinta ya yi sanyi. Haka dai suka ida aikin jefi jefi suna hira, da yake Baba Atinen gwana ce wajen son hira. Se da suka gama komai suka kwashe suka zuba inda ya dace kafin Baba Atine ta bar sashen, ya yin da Didi ta wuce kai tsaye ta faɗa toilet dan yin wanka. Ta kwashi mintuna masu ɗan dama tana wankan kafin ta fito. Ta nemi waje ta zauna dan gyara jikinta. Ko minti 2 ba ta yi da zama ba Baba Atine ta yi sallama cikin ɗakin. Amsawa Didi ta yi sannan Baba Atinen ta shigo. Murmushi suka yi wa junansu kafin Didi tace

"Baba.."

"Na'am 'yata.. kin fito kenan? Allah ya sa dai ba ki gama shiryawa ba." Ta yi maganar tana kallanta. Girgiza kai Didi ta yi tace

"A'ah fitowata kenan.. Wani abun za a miki?"

"Wane ni? Matar uban masu gida..?" Ta faɗa cikin wasa saboda ta san Didin ba ta so ta dinga faɗa mata hakan.

"Kai Baba.." Didi ta faɗa.

"Toh shi kenan.. Yanzu dai Hajiya ce ta aiko ni.." ta yi maganar tana neman waje ta zauna. Kafin Didin tace komai se ta soma buɗe ledar dake hannunta sannan ta ɗora da faɗin
Chapter 39 · 0% Book details