← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 122

Sashe 117

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Toh shi kenan.." Ya dakata a nan yana nannaɗe hannun rigarsa. Kawai se ta tsaya tana kallan ikon Allah. Se da ya ida ɗauke hannayen rigar tasa kafin ya kamo hannunta, a nutse ya soma takawa da ita har zuwa kan wani ƙaramar kujera da ke cikin kitchen ɗin. Ya zaunar da ita a hankali kafin yace

"Zauna ki kalli yanda mijinki ze girka miki abinci me daɗi." Buɗe ido ta yi da sauri. Ta ɗan gyara zamanta tana kai hannu ta ɗora a kan cikinta da ɗan ciki ma ya motsa.

"Wai kai?"

"Ƙwarai kuwa.. Bari ki ga.." Ya ba ta amsa irin da gasken nan iyawa ya yi. Dariya ta yi tana binsa da kallo, lokacin da ya ƙarasa inda ta baro. Tace har lokacin tana kallansa.

"Habibi toh fitar kuma fa?" Dan yanzu tare suke fita da Bad Man.

"Bari zan kira shi." Ya faɗa yana ɗaukar wuƙar da ke a ajiye. Se ta sake gyara zama tana kallan yadda za a gabatar da wannan girkin. Cikin ƙanƙanin lokaci ya soma yanka albasar gabza-gabza. Tana daga gefe tana riƙe dariyarta, ya yin da shi kuma ya taƙarƙare aiki yake me kyau.

"Wai Habibi haka ake yanka albasar?" Ta faɗa dan ta kasa yin shiru. Juyawa ya yi yana kallanta, cikin basarwa yace

"Yankan ƙwararru ake gaya miki.." Ba ta san lokacin da dariya ta ƙwace mata ba. Har se da ta saka hannu ta sake dafe cikinta da zuwa lokacin ya fito sosai. Se ya shagala da kallanta, shi ma murmushi na tashi a kan kyakykyawar fuskarsa. Se da ta gama dariyar kafin yace

"Gama dariyar ki zo kina santi." Kafin ya kai ga juyawa ya ga abin da yake yi ya cigaba da yanka albasar. Inda cikin rashin sa'a maimakon ya yanka albasar se ya yanki hannunsa. Da yake idanunta gaba ɗaya na kai ya sanyata gani. Idanunta ta buɗe da sauri, har ba ta san lokacin da ta miƙe ba. Duk da nauyin jikinta hakan be hana ta saurin ƙarasowa inda yake ba, ta kama hannun da ya riƙe yana kalla tace idanunta cike fall da ƙwalla.

"Sannu Habibi.. Sannu.." Ta faɗa tana cigaba da kallan hannun. Hannun ya karɓe yana kalla yanda ta ruɗe gaba ɗaya. Ya ja ta jikinsa ya rungume kafin yace

"Babu komai fa Uhmmm?" Girgiza kai ta yi tana barin ƙwallar ta sauko daga cikin idanunta tace

"Ban yadda ba.. Ni dai ka zo mu je asibiti."
Murmushi ya yi yana sake jin ƙaunar Lulun na ratsa shi. Yanda take magana kaɗai ya isa ya nuna maka yanda take a ruɗe. Ballantana kuma ka kalli yanayinta.

"Me zan yi ki yarda da ban ji ciwo ba.. Ko na ƙarasa girkin?" Ai ba ta san lokacin da ta tashi daga jikinsa ba, ta shiga girgiza kai tana faɗin

"A'ah, ba na jin yunwa.. Na ƙoshi Allah kuwa." Ta faɗa tana riƙo hannayensa dan ma kar yace ze cigaba. Murmushi ya yi kafin yace

"Toh shi kenan.. Amma dai ki yi murmushi." Maƙe kafaɗa ta yi tana ɗan rufe idanunta ta buɗe a lokaci ɗaya. Shi ma ɓata fuska ya yi, kafin a ɗan marairaice yace

"Haba mana Matata Uhmm? Matar Gwani Affan..?" Tilas maganar tasa ta sanya ta dariya. Ya sake rungumeta yana faɗin

"Dats my baby girl.." Sun kai wajen minti 2 a haka kafin ta tashi. Yace yana kallanta

"Me za ki ci yanzu? Kar ki ce min kin ƙoshi, idan ba haka ba zan cigaba da girkina ne."

"Ba na son cin komai yanzu Allah kuwa.."

"Toh se me za ki ci?" Ya tambaya cike da kulawa. Shiru ta yi tana nazarin abin da za ta faɗa. Se ta jiyo muryarsa yana faɗin

"Ko za ki ci abincin gidan Ummeey?" Murmushi ta yi tana jinjina kai. Shi ma murmushin ya yi cikin ransa yana jin daɗin mafitar da ya samu, dan ya san da ba lallai ta ci ba.

Aikuwa gidan Ummeeyn suka nufa kai tsaye bayan ya shiryata da kansa. Sanda suke shirin shiga Abeey da jikinsa ya yi kyau sosai ke shirin fita. Suka dakata suka gaisa.

"Ga shi kun shigo ni kuma zan fita.." In ji Abeey.

"Wallahi kuwa Abeey." Gwani ya faɗa.

"Ko za ka zo mu je ne? Karatu ne zan gabatar, na ɗauka ayyuka sun maka yawa shi ya sa ban sanar da kai ba." Girgiza kai Gwani ya yi kafin yace

"A'ah Abeey, bari na shiga mu gaisa da Ummeeey se na fito."

"Toh shi kenan.."

"A dawo lafiya Abeey." Lulu ta faɗa.

"Allah ya sa ɗiyata.." Ba ta sake cewa komai ba ta bi bayan Gwani suka wuce cikin gidan. Gaisawar kuwa kawai ya yi da Ummeeyn ya faɗa mata fitar da za su yi da Abeey kafin ya yi sallama da abar ƙaunar ta shi kana ya fito suka fice da Abeeyn. Da ma in dai Lulun ta zo gidan, Ummeey ba ta zama haka nan. Dalili kenan da ya sa ta miƙe kai tsaye ta faɗa kitchen dan ɗora mata wani abu me sauƙi da za ta iya ci kafin ta gama girki. Cikin sa'a ma kafin ta fito Lulun ta ɓingire se bacci.

... Har sun soma tafiya dan ficewa daga wajen, Sadik yace

"Bad!" Juyawa ya yi ya kalli Didi da ta wani haɗe rai. Ya yi murmushin gefen baki yana ɗan cizar laɓɓansa. Ya juya daidai lokacin da Sadik ɗin ya ƙaraso inda suke.

"Areef!" Buɗe ido Sadik ya yi kafin yace

"Ka san Allah har manta sunanka nake yi.. Kawai ka bar ni na cigaba da kiranka da hakan." Da dai ya ga ba fahimta ze yi ba kawai se cewa ya yi

"Madam ba ta so." Buɗe ido ya yi yana kai hannu bakinsa yace ƙasa ƙasa

"Masu abu da abinsu.. Toh a mana afuwa mun tuba."

"An yi muku." Areef ya faɗa yana murmushi, kafin ya saci kallan Didi. Murmushi ita ma ta yi, ya sauke ajiyar zuciya. Se da suka ƙara magana kafin suka sake yin wata sallamar Sadik ya koma ciki, ya yin da Areef ya ƙarasa inda ya bar Didi suka wuce.

_BAYAN WASU WATANNI_

... Sanye cikin wasu tausasan kaya na sanyi dukka suke. Waɗanda suka mugun yi musu kyau. Kai idan ba ka san daga inda suka fito ba se ka ce da ma can en asalin ƙasar ne. Saboda yanda suka fito suka yi kyau, suka kuma saje da en ƙasar. Waje ne me kyau, shiru babu hayaniya, se korayen shuke-shuke da suka mugun ƙawata wajen. Sun kai awa ɗaya a wajen, kowanne na tare da matarsa cikin farin ciki da ƙaunar juna. Se lokacin da suka miƙe za su tafi. Hannun kowannensu na saƙale da na matarsa. Ya yin da daga Lulu har Didi cikin kowaccensu ya fito ya yi acan-acan cikin wadatacciyar rigar jikinsu. Idan ba ka sani ba ma se ka ɗauka watannin cikin nasu duka ɗaya ne, dan Didi na da girman ciki ne ya sa girman cikinta ya zo ɗaya da na Lulu da ta shiga watan haihuwa.

"Za ki iya ƙarasawa ko na ƙarasar da ke?" Areef ya faɗa yana kallan fuskar Didi. Girgiza kai ta yi kafin ta amsa da

"A'ah fa Babe zan iya.." Ta yi maganar ƙasa ƙasa tana cigaba da takawa a hankali. Sake riƙota ya yi sosai dan ta ji daɗin tafiyar, cike da takatsantsan suka cigaba da takawa. Daidai sun fito daga wajen Lulu ta dakata daga tafiyar da take da ƙyar. Bayan ta ɗan ajje numfashi tace tana kallan Gwani da shi ma ya dakata.

"Ka ga se harbi na yake yi koh?" Ta faɗa kamar za ta yi kuka.

"Waye?" Ya ƙare yana buɗa idanunsa, dan sam be fahimci abin da take nufi ba.

"Babyn nan mana." Ta ƙare tana nuna cikinta. Bin tirtsetsen cikin nata ya yi da kallo, wanda rigar jikinta ta ɓoye girmansa, kafin ya yi murmushi gane abin da take nufi. Se ya gyara tsayuwa kana yace

"Shi ma ya ƙagu ya ga Abbunsa.." Ya ƙare yana murmushi. Turo baki ta yi kafin yace

"Aou ban da ni koh?"

"A'ah har da ke mana.. Amma ya fi so ya ganni.." Ya faɗa cike da tsokana.

"Ni dai ban yadda ba." Ta faɗa tana ɓata fuska.

"Toh shi kenan, yana son ganinmu duka Uhmmm?" Ya faɗa yana kallanta fuskarsa ɗauke da murmushi. So yake kawai ta amsa da ehh dan su wuce, saboda ba ya son wannan tsayuwar kar ta wahala, abin cikinta ma ya wahala. Se kuwa ta jinjina kai tana murmushi. Ya sauke numfashi yana sake riƙo hannunta suka ƙarasa inda motar take.

"Mommah ce.." Ya ƙare maganar yana kallan Areef da ke kallansa lokacin da wayar ke hannunsa. Buɗe ido Areef ya yi kafin ya ɗan yi murmushi. Daidai lokacin da Gwani ya ɗaga wayar. Daga can ɓangaren Mommah tace bayan sun gaisa

"Affan.."

"Na'am Mommah.."

"Wai yaushe za ku dawo min da 'ya'ya ne? Ina fa sane da Afaaf ta shiga watan haihuwarta.. Me kuke jira ne? Ko so kuke su haihu a inda ba su da kowa?" Harara ya jefawa Areef da ke kallansa, ya yi dariya ƙasa-ƙasa yana ɗauke kai.

"In Sha Allah cikin satin nan za mu taho.."

"Toh ku ƙoƙarta dai.. Allah Ya ƙara lafiya."

"Ameen Mommah." Ya amsa da hakan yana ajje wayar. Ya dubi Areef yace

"Malam ko da me kake tafiya cikin satin nan za mu koma gida.. Haka kawai?"

"Duk abin da ka ce ai haka za a yi Oga." Ya ƙare maganar kamar irin yaron da ke gaban Ogansa. Tilas ya yi dariya dan yanda ya yi maganar ba ƙarya ya ba shi dariya.

A ɗaya ɓangaren kuwa bayan da Mommah ta sauke wayar, Daddy da ke gefenta yace

"Ke da 'ya'yan naki ne?"

"Wallahi kuwa Rankayadaɗe, sun riƙe yara sun ƙi dawowa, haka nan kawai su haihu a can.. Gwara su dawo nan cikin dangi se ya fi." Murmushi Daddy ya yi kana yace

"Gaskiya dai kam.. Toh Allah Ya dawo da su lafiya."

"Ameen." Tana kai ƙarshen maganar ɗaya daga cikin sabbin ma'aikatan da Daddy ya zuba ya ƙaraso inda suke. Cike da girmamawa yace
Chapter 117 · 0% Book details