← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 122

Sashe 12

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Inna lillahi.. Wallahi na manta, wallahi sam na manta da kamarsu ɗaya za ka iya kasa gane wace ce Afaaf.. Inna lillahi.. wallahi mantawa na yi.." ta faɗa kamar za ta fashe da kuka. A fusace Ladi ta kalleta jin ashe tun farko ita ta so ta kwafsa musu, se dai kafin ta kai ga cewa komai Hero yace

"Ba su da bambanci koh?" Jinjina kai Abida ta yi tace duk a muzance

"Basu da shi, kamar su ɗaya sakk. Ni ma ina gane su ne kawai ta hanyar niqab da ɗayar take sakawa. Sannan ita shiru shiru ce tana da haƙuri yayin da ita Afaaf ba ta da haƙuri ko kaɗan, se dai ita ma miskila ce kamar er uwar.."

"Idan haka ne kenan ba ki da tabbacin da wadda na haɗu a restaurant..?" Hero ya tambaya yana kallanta. Se da ta saci kallan Ladi dake cigaba da auna mata da harara sannan tace

"Ehh.." Ajiyar zuciya Hero ya sauke a ransa yana tuna haɗuwarsu da Lulu. Duk wata hanya da ze bi wajen gane wadda ya haɗu da ita ya ma kasa ganewa. Toh ita kanta Abidar ma da ta sansu ba ta gane ba ballantana shi?

"Yanzu wace hanya ta rage mana?" Ladi ta yi ƙoƙarin faɗin haka. Buɗe baki Abida ta yi da niyyar yin magana Ladi ta katseta da

"Dallah yi mana shiru. Ina ke kika janyo duk wani abu da ya faru? Fice min da gani tun kafin na kai miki duka.." ta faɗa tana watsa mata wata banzar harara.

"Ki yi haƙuri, wallahi mantuwa na yi.."

"Kin ga ki fice min a ɗaki nace koh?" Ganin Abidar na ƙoƙarin sake cewa wani abu, ya sanya Ladi sake faɗin

"Ki fice min nace dallah.." ta faɗa cikin ɗaga murya. Sum_sum ta ja ƙafafunta ta fice daga ɗakin cike da haushin kanta da kuma takaicin abin da Ladin ta mata. Maida dubansa Hero ya yi kan Ladi yace

"Toh wai ki haƙura da yarinyar nan mana.. Ga mata nan kala kala a cikin garin nan, ba ma garin nan ba, ko a wajen garin nan ne za ki samu duk kalar macen da kike so za ki iya samu, ki haƙura da wannan, ban da wahala babu abin da muke sha."

"Haba Hero.. Kai ɗin ne kuwa? Anya kai ne kuwa? Ina dukka ƙwarin gwuiwarka? Ya kake so na yi idan ka juya min baya? Ni kawai ina son yarinyar, kuma ba zan iya haƙura da ita ba. Don da zan iya haƙura da ita da tuntuni na haƙura tun lokacin da ta suɓuce min.." Ajiyar zuciya Hero ya sauke, a ransa yana jin haushin irin wannan nacin na Ladi.

"Shi kenan.. Yanzu ya kike so a yi?"

"Ina hoton nan da ka ɗauka?" Ladi ta tambaya.

"Wane amfani ze mana?" Ya yi maganar cikin halin ko in kula.

"Ina dai yanzu neman Afaaf muke yi? Waye ya aureta? Ya za a yi na san inda take, su ne abin da muke nema koh?" Ta ƙare da sigar tambaya. Se dai ba ta jira yace komai ba ta ɗora da faɗin

"Wannan hoton ze matuƙar taimaka mana.. Ta inda za mu gane da gasken ma ta yi auren ko kuwa? Idan ta yi auren tana ina? Idan mun gano inda take wa ta aura? Ina kuma abokinka yake?"

"Duk da hoton?" Hero ya tambaya irin a sheƙen nan. Se ta jinjina kai kafin tace

"Ƙwarai kuwa.. abu ɗaya kawai za mu yi, shi ne neman ta inda hoton ze isa wajen mijin nata. Daga nan zamu san ko shi waye, na kuma san dole ze sakota, idan da gaske ta yi auren kenan. Daga nan kuma kamar yanda na faɗa wasana ze soma.. Kai ni ko be ma sakota ba, idan dai har ya bayyana kansa na san waye shi, neman gidansa ba ze min wahala ba, dan haka har cikin gidan zan je, ni ba baƙuwar zafi ba ce, musamman ma kuma a kan abin da nake so.." ta ƙare tana murmushi, ji take kamar ta gama samun Lulun ta gama.

"Hakan ya yi.. Se dai wani hanzari ba gudu ba.."

"Me ya faru?" Ladi ta faɗa tana kallan Hero.

"Zan ɗan yi tafiya ne in dawo na en kwanaki kaɗan. Saboda haka ki jira dawowata, ni zan yi miki aikin komai. Kin ga kuma ga abokina ya shiga cikin case ɗin, dole zan fi bada himma wajen nemo gaskiyar lamarin." Da sauri Ladi ta girgiza kai, tace sanda ya kai ƙarshen maganarsa.

"A'ah.. Allah ya tsare hanya.. amma kafin ka dawo na gama aikata abin da na tsara.. Babu buƙatar se ka je ka dawo, kawai ka ba ni hoton, zan san yanda zan yi.."

"Ohk kina nufin ba kya buƙatar taimakona."

"No ba wai haka ba ne.. Kawai dai tun da tafiya za ka yi, ai gwara na yi komai da kaina koh?"

"Toh je ki yi.. Amma ki sani duk wata matsala da aka samu, kar ki tuhume ni. Ka da ma ki sake janyo ni cikin wannan harkar taki.." ya ƙare yana shirin juyawa. Da sauri Ladi tace

"A'ah kai fa daɗina da kai kenan, saurin fushi.. dawo ka ji.."

"Za ka kai kwana nawa kafin ka dawo..?"

"Kwana 5.." ya faɗa cikin basarwa.

"Shi kenan zan jiraka.. Dama akwai wasu en mata da nake jira, gobe goben nan za su iso.. Idan ya so kana dawowa se mu dira a kan wannan maganar.."

"Kar ki damu.." Hero ya faɗa yana juyawa dan barin ɗakin..

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO30*

___A ɓangaren Bad Man kuwa, kwance yake a kan gadonsa, bayan sanda wannan nannauyan baccin ya yi awon gaba da shi. Idanunsa ya shiga buɗewa a hankali kamar wanda ya gama shan wasu kayan maye. Fuskarsa ya yamutse saboda yanda ya ji kansa ya wani irin sara masa. Se ya kai hannunsa kan nasa ya ɗan dafe shi, kafin ya miƙe zaune har lokacin be saki kan nasa ba. Har wani ɗan layi yake sanda ya miƙe ɗin, hakan ne ya sanya shi komawa ya sake zama na en sakanni. Sannan ya sake miƙewa kai tsaye ya wuce toilet ɗinsa. Ya shafe fiye da mintuna 30 a ciki sannan ya fito lokacin da duk wata sumar dake jikinsa take a jiƙe, ta kuma sake lafewa a jikinsa. Kai tsaye kaya ya saka, kamar ko yaushe ƙananan kaya. Wayarsa ya ɗauka ya jefata a aljihu kafin ya fice daga ɗakin, dan yau ɗin so yake ya ɗan fita ko yaya ne. A parlour suka yi kaciɓus da Daddy dake ƙoƙarin haurowa saman. Se ya dakata cike da mamakin ganinsa, dan abu ne da be saba gani ba. Daddyn a sashensa ba tare da wani ƙwaƙwƙwaran dalili ba.

"Me ya samu wayarka ina ta kiranka ba amsa?" Daddy ya tambaya cikin kulawa, dan ba kaɗan ba hankalinsa ya tashi, saboda kiransa da ya dinga yi babu amsa. Ɗan yamutse fuska ya yi bayan ya shafi gefen kansa yace

"Tana silent ne."

"Ohk toh me ya samu idanunka haka?" Daddy ya faɗa yana karantar yanayinsa. Cikin basarwa ya gyara tsayuwarsa yana faɗin

"Babu.. Ciwon kan nan ne dai kawai.."

"Ohk.. ya kamata ka je ka ga likita.."

"Tohm.." ya amsa da hakan yana shirin wucewa.

"Areef.." Daddy ya faɗa. Se ya juya ya kalli Daddyn ba tare da yace komai ba.

"Me kake yi cikin part ɗin nan?" Da mamaki yake kallan Daddyn jin abin da ya faɗa. Kafin kuma yace komai Daddy yace

"Ka manta yanzu ka yi aure? Wancan sashen za ka koma kafin komai ya daidaita.." Shiru ya yi na tsawon sakanni har lokacin yana kallan Daddy. Shi gaba ɗaya ma ya manta da wannan wasan yaran. Toh abu ne da ba ya tunanin yiwuwarsa dan haka ta yaya ma ze yiwu? Kamar ba ze ce komai ba se kuma ya buɗe baki da ƙyar yace

"Daddy.." se kuma ya dakata kamar wanda ya manta abin da ya soma faɗa. Jin shirun da ya yi ne ya sanya Daddy faɗin

"Kaa fahimta koh?"

"Za mu fita da Kaseem ne, na san yana jirana.." shi ne abin da Bad Man ya faɗa cikin basar da zancen Daddyn da sam ba ya son jin shi. Zuciyarsa zafi take masa sosai, gani yake yi kamar ya gama zubewa ƙasa warwass, har kamar shi za a ɗaurawa aure ba tare da saninsa ba? Da yarinyar da be santa ba? Kuma a ɗauketa a kawota gidansu, har ake faɗa masa ya koma inda aka kaita. Wace ce ita? Wace ce ita da har ze iya haɗa wajen zama ɗaya da ita? Lallai kuwa yau ɗin idan dai har ya shiga part ɗin, toh fa ba ze fito ba har se ya rubuta mata takaddar saki.

"Ka dai ji abin da na faɗa maka ai. Za ka iya tafiya.." Daddy ya faɗa yana riga shi yin gaban ma. Bin Daddyn ya yi da kallo sanda ya fice daga ɗakin. Ya ɗan ciji gefen lips ɗinsa na ƙasa yana fidda numfashi da ɗan sauri.

... Da sauri Mom ta ƙarasa inda yake, ta yi saurin riƙo hannunsa tana faɗin

"Ina za ka je?" Juyawa ya yi ya kalli Mom ɗin yace muryarsa a ɗan zafafe se dai ba cikin ɗaga murya ba

"Zan je na aikata abin da na yi niyya ne.." ya faɗa ransa a ɓace.

"Me kenan? Kar ka ce min sakin yarinyar can?"

"Yeah shi.." ya faɗa yana tsare Mom ɗin da ido, cikin rashin fahimtar abin da take nufi da dakatar da shi da ta yi. Girgiza kai ta yi da sauri tace kamar za ta yi kuka.

"Rabu da ita tukunna Boy.. Kar ka sake ka saketa.. Daddynka yace duk ranar da ka saketa ni ma ze sake ni.. dan haka ka bar komai a hannuna, zan nemo hanyar da za ka saketa cikin kwanciyar hankali ba tare da kowa ya zargi wani abu ba." Hannunsa dake cikin nata ya cire a hankali yana kallanta. Ya ma rasa abin da ya kamata ya yi. Da gaske Mom ɗin ke faɗin haka? Kar ya saketa fa take faɗa, toh ta zauna ta masa uwar me? Shin duk abin da Daddyn ya masa ba ta ji babu daɗinsa ba? Ko kuwa me yake faruwa.
Chapter 12 · 0% Book details