← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 122

Sashe 114

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Haka ne.. Allah Ya yi muku albarka. Shi kuma Alhaji Matawalle Allah Ya saka masa da alkhairi." Ya ƙare maganar yana ƙoƙarin komawa ya kwanta. Da sauri Gwani ya ƙarasa ya taimaka masa ya kwanta ɗin yana ɗan sauke ajiyar zuciya. Gwani ya bi shi da kallo cike da tausayawa. A kan laɓɓansa ya furta

"Allah Ya ba ka lafiya me ɗorewa Abeey."

.. A ɗaya ɓangaren kuwa kulle ɗakinsu Lulu ta yi ta koma na su Didi. A nan suka yi wanka, sallah da duk wasu abubuwan. Kafin suka zauna hira. Har zuwa lokacin da Didi ta shiga hamma da alama bacci take ji.

"Wai bacci kike ji?" Lulu ta tambaya tana kallanta. Jinjina kai Didi ta yi tana rufe bakinta da hannunta saboda hammar da ta sake yi.

"Hmm uhmm.. Yanzu wai kwanciya za ki yi?" Ta yi maganar tana kallan Didi da ke ƙoƙarin ɗora kanta a kan ƙafarta. Jinjina kai Didi ta yi tana ida ɗora kan nata a kan ƙafar Lulun tace

"Don Allah kar ki motsa ƙafarki." Ta faɗa tana riƙe ƙafar sosai.

"Na ji." Lulu ta faɗa tana tura baki, dan ita dai so ta yi su cigaba da hirarsu kafin su dawo. Ita kuma wai bacci, haka tana ji tana gani cikin ƙanƙanin lokaci bacci ya kwashe Didin.

"Lallai ma Didi." Ta faɗa tana kallan fuskarta. Cigaba da zama ta yi har zuwa lokacin da ta ji an yi knocking ɗin ƙofar. Ta saka hannunta ta sauke kan Didi daga kan ƙafarta ta maida kan pillow kafin ta miƙe. Ta sanya key ta buɗe. Murmushi ta yi ganin Bad Man tace

"Aou Ya Areef.."

"Na'am, ina matana?" Ya faɗi abin da ke ransa.

"Oh ni Afaaf.." Ta faɗa a kan laɓɓanta.

"Idan ma Affan ne.." Ya faɗa yana murmushin gefen baki dan sarai ya ji abin da ta faɗa. Ba ta zata ba, hakan ne ya sa ta buɗe baki cike da mamakin yanda aka yi ya ji ta. Se kuma ta murguɗa baki tace

"Habibin guda?" Ba ta jira yace komai ba ta fice daga ɗakin, dan ita kanta ta ba wa kanta kunya. Murmushi ya yi kafin ya shige cikin ɗakin. A kan gado ya hangota tana bacci cikin nutsuwa. Ya ƙarasa fuskarsa ɗauke da mamaki yana kallan fuskarta da ta yi fayau. Ya juya a hankali ya kalli ƙaton agogon da ke manne a jikin bangon ɗakin kafin ya dawo da dubansa kanta.

"Wannan wane irin bacci ne? An ya na lafiya ne kuwa?" Ya tambayi kansa cike da fargabar da lokaci ƙanƙani ta ziyarce shi..

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO83*
Second to the last page... 😩😭🥳

___ A hankali ya ƙarasa gadon har lokacin idanunsa na kanta. Ya kafe ta da idanunsa na tsawon sakanni kafin ya saka hannunsa ya ɗaga ta ya gyara mata kwanciyar. Ya ja blanket ya lulluɓe ta kafin ya wuce toilet. Ya kwashe mintuna masu dama kafin ya fito. Ya shirya cikin wasu kayan bacci masu kyau. Ya ƙarasa ya kwanta a kan gadon. Se da ya ja ta jikinsa ya rungume kafin ya lumshe idanunsa yana jin yanda numfashinta ke sauka cike da nutsuwa.

... A nutse ya kamo hannunta cikin nasa, dalili kenan da ya sanya ta ɗaga idanunta ta zuba cikin nasa. Se kuma ta ɗan janye daidai lokacin da yace

"Ki na lafiya?" Juyawa ta yi gaba ɗaya tana kallansa cikin mamakin jin tambayarsa. Fahimtar yanayinta ya sanya shi jinjina kai. Se ta yi murmushi dan kawar masa da damuwar da ta gani shimfiɗe a kan fuskarsa, duk da ita ma haka nan kawai take jinta kamar ba lafiya ba. Se dai takamaimai ta kasa gane abin da ke damunta, tace

"Eh fa, ba abin da ke damu na."

"An ya kuwa?" Ya sake yin maganar yana ƙura mata idanunsa. Lumshe idanunta ta yi kafin ta buɗe. Ta ɗauko ɗayan hannunta da ba ya cikin nasa ta ɗora a kan hannun nasa, ta ɗan riƙe sosai kamin ta jinjina kai tana lumshe idanunta a cikin nasa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya fesar da iska daga bakinsa yace

"Alhamdulillah.." Kallansa kawai take yi tana jin ƙaunarsa na ratsa kowacce gaɓa ta jikinta. Kulawarsa a gareta tana da yawa.

"Ko in matso ki cinye ni kawai?" Ya faɗa cike da tsokana yana ɗage girarsa guda ɗaya. Kanta ta ɗora a kan cinyarsa tana faɗin cike da shagwaɓa

"Ni dai.. ni dai Allah kuwa ba na so.." Dariya ya yi kafin ya saka hannunsa ya ɗago ta. Ta kauce jikinta tana sake shagwaɓe fuska. Kawai se ya ja ya rungume cikin rarrashi yace

"Ni ne ba? Toh na tuba na dena." Shiru ta yi tana murmushi ƙasa ƙasa. Sun kai wajen minti 5 a haka kafin ya sake ta ya miƙe yana faɗin

"Tashi mu shirya.. Kar su riga mu shiryawa." Ya yi maganar yana ɗaukarta yanda ze fi masa sauƙi.

... Wayarsa da ta yi ƙara ita ce ta sanya Lulu dakatawa. Da yake ta fi kusa da wayar, hakan ne ya sanya ta ƙarasawa ta dauka, ba tare da ta kalli me kiran ba ta ƙarasa inda Gwani yake yana mayar da takardu cikin wata madaidaiciyar jaka.

"Ana kiranka.." Ta faɗa tana miƙa masa wayar. Maimakon ya karɓa, se kallanta da ya yi. Ta turo baki jin ya ƙi karɓa har tana neman tsinkewa.

"Kiranka fa ake.." Ta faɗa har lokacin ba ta maida fuskarta daidai ba. Hannu ya kai ya karɓi wayar. Maimakon ya ɗauki wayar ita kaɗai, se ya haɗa da me wayar gaba ɗaya ya ja ta se ta koma tana kallan inda yake kalla shi ma. Se da ya nemi waje ya zauna yana gyara mata zaman da ta yi kusan a jikinsa, kafin ya ɗaga wayar da aka yi kira na biyu.

"Ina ta ƙoƙarin kiranki se kuma na sha'afa."

"Toh babu damuwa.."

"Idan mun dawo In Sha Allah zan sanar da ke.." Abubuwan da Gwani na ji yana faɗa kenan, waɗanda suka fi kama da bayar da amsa. Kasancewar ba na jiyo abin da ake faɗa a can ɓangaren ya sa ban fahimci zancen gaba ɗaya ba. A hankali kamar wadda ta ga wani abun ta shiga tashi daga jikinsa, duk da yanda ya riƙe ta, amma se da ta fuzge jikinta ta miƙe zaune sosai. Kallansa ta shiga yi da narkakkun idanunta har zuwa lokacin da ya ajje wayar. Se kuma kawai ta soma shirin miƙewa, ya yi azamar saka hannunsa ya maida ta inda ta tashi. Jikinta ta ƙwace tana jin yanda ƙwalla ta cika mata cikin idanu. Se da ya juyo da ita, ya tabbatar suna kallan juna ne kafin yace

"Me ya faru?" Ya tambaya yana kallan cikin idanunta. Runtse idanunta ta yi ba ta so hawayen su zubo, dan kuwa ba ta shiryawa zuwansu ba, kawai jinsu ta yi. Ba kuma ta so ya gani, hakan ne ya sanya ta sake yunƙurin tashi.

"Toh ka bar ni na tafi ka cigaba da wayarka mana." Ta kai ƙarshen maganar tana jin zafi har cikin zuciyarta. Shi wallahi se yanzu ma ya fahimci dalilin fushin nata. Be san sanda murmushi ya ɗan suɓuce a kan fuskarsa ba. Ya basar dan kar ta gan shi ta dira wata shagwaɓar tata.

"Malama Amina ce.. Magana ce kuma a kan musabaƙa da muke shiryawa, wadda za a gabatar nan ba da daɗewa ba. Idan kuma ba ki amince ba ga wayar nan ki kira." Ya ƙare maganar yana miƙa mata wayarsa. Bin wayar ta yi da kallo kamar wata doluwa, kafin a hankali ta maida dubanta kansa, lokacin da ƙwallar idanunta ta soma tsotsewa dan kanta. Duk se ta ji kunya ta kama ta. Tabbas ta yadda da shi ɗari bisa ɗari, amma kishinsa da take na da tasirin da ba za ta iya dannewa ba muddin ta ji shi yana waya da mace. Hannu ta kai ta sake goge ƙwallar gaba ɗaya murmushi na ɗan ƙwace mata, ta kuma kasa ɗaga ido ta kalle shi. Ya lumshe idanunsa yana jin wata nutsuwa. Se da ta ɗago kafin ta saka hannu ta tura hannunsa da ke ɗauke da waya baya. Ta girgiza kai tana kaucewa idanun nan nasa. Murmushi ya yi kafin yace

"Kin amince da ni?" Har lokacin ba ta kalle shi ba ta jinjina kai. Ajiyar zuciya ya sauke yana faɗin

"Na gode wa Allah!" Ya ɗan dakata kafin ya ɗora da faɗin

"Ni fa rashin kallan nan nawa kan jefa ni cikin yanayi.. A kalle ni ko sau ɗaya ne mana.." Ya ƙare yana langaɓar da kai. Tilas ta ɗaga kai ta kalle shi tana murmushi.

"Ki saka a ranki Affan naki ne ke ɗaya har abada.. Kar ki kuma sakawa ranki tunanin zan kula wata ne da sunan soyayya.. Ke ɗin nan kin ishe ni, musamman ma kuma da nan da kwanaki kaɗan za mu ƙaru mu zama mu uku." Ya ƙare yana saukar da idanunsa kan cikinta. Hannu ta kai ta dafe cikin nata tana lumshe idanunta. Ya kai nasa hannun ya ɗora shi ma yana lumshe nasa idanun. Kusan a tare suka buɗe idanun. Gwani ya sauke numfashi yana sake kafe ta da idanunsa.

"Ina son ganin wannan kishin nawa a cikin idanunki. Yanayin kan sa na ji ni cikin nishaɗi, na kuma sake tabbatarwa matata na sona."

"Aou fushin nawa kake so?" Ta ƙare a shagwaɓe. Da sauri ya girgiza kai yana kamo haɓarta ta koma kallansa sosai yace

"Fushinki daban, haka zalika kishinki daban. Yanayin ba iri ɗaya ba ne. Ni kaɗai na san halin da nake tsintar kaina idan na ganki cikin fushi. Ke ba na ma fatan sake ganinki ciki har abada. Ina fatan ɗorewar farin ciki a rayuwarmu har abada. Allah Ya tabbatar da hakan."

"Ameen Mijina.." Ta ƙare tana kwantawa a jikinsa. Rungume ta ya yi cikin jikinsa yana jin yanda wata irin soyayyarta ke sake ratsa ilahirin jikinsa.

Kusan a tare suka gama shiryawa, dan haka tare suka fita. Kai tsaye asibitin suka nufa. Wuni suka yi a cikin asibitin. Ranar gaba ɗaya Lulu da Didi na tare da Ummeey. Wanda hakan ba ƙaramin daɗi ya mata ba. Se da dare kafin suka soma shirin tafiya.

"Tafiyar ce?" Ummeey ta faɗa tana kallansu.
Chapter 114 · 0% Book details