← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 122

Sashe 65

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sosai kuwa Yallaɓai.. Kuma da ma In Sha Allah ni ma na yi ƙoƙarin hakan." Murmushi Abba ya yi dan ya fahimci abin da Ammin ke nufi yace

"Allah Ya saka da alkhairi, Ya ƙara buɗi." Dariya Ammi ta yi jin abin da ya faɗa ɗin. Bayan duk kuɗin da take amfani da su na shi ne. Amma duk da haka se ta amsa da

"Ameen Ameen." Daga haka suka yi sallama.

... Se da ta shirya shi tsaff cikin kayansa masu kyau sannan ta shiga tattare inda ya ɓata. Tana cikin yi ta tsaya ta jefa masa harara

"Haka kurum ka yi ta ɓata waje kamar me.." Turo ƙaramin bakinsa ya yi yace

"Kai Didi Allah kin ƙaro faɗa."

"Aou da ma ina da faɗa kenan koh?" Ta faɗa tana waro ido.

"Ehh." Ya faɗa yana gyaɗa kai kamar wanda ke shirin tsinka shi. Dariya Didi ta yi tana faɗin

"Little.. Little.." tana girgiza kai. Ranar a ɗaki suka wuni abinsu. Ba ta bari Little ɗin ya je ko ina ba ballantana ma Bad Man ya gan shi.

Tabbatarwa da ta yi idanun Little ba sa kanta ya sanyata nufar ƙasan gado ta sanya hannu ta ɗakko wata ƙaramar bottle da ta yi nasarar ɗaukowa daga ɗakinsa ɗazu da ta je kai masa coffee ɗin safiya.

"Kar ka je ko ina ka ji ɗan ƙanina.. Yanzu zan dawo." Ta faɗa tana murmushi. Jijjiga kai ya yi yana cigaba da wasansa. Se kuwa ta fice daga ɗakin. Kamar yanda ta yi ranar nan haka yau ma ta haƙe rami ta fasa ciki ta kuma binne kwalbar. Se a lokacin sannan ta sauke ajiyar zuciya. Kamar kullum da yanzu ya shiga cikin duk wasu addu'o'inta haka yanzun ma a fili ta furta

"Allah Ya shiryeka.. Ya yaye maka wannan masifar." Ta yi maganar tana miƙewa. Karkaɗe jikinta ta soma yi wajen da ƙasa ta ɓata. Ba ta ankara da tahowar mutum ba se ji ta yi an ce

"Daughter!" A zabure ta ɗaga kai ta kalli Mommah da ta ƙaraso wajen. Me ya kawota nan? Ya aka yi ta zo? Yaushe ta zo? Tambayoyin da suke lugude a kanta kenan. Waɗanda suka sakata kasa amsa kiran da Mommah ta mata. Tsoronta ɗaya kar ta je ta ganta shi kenan komai ya ƙare ba tare da ta samu nasara ba.

"Lafiya? Me ya faru? Me kike yi a nan?" Ta yi tambayar duka a jere. Ba ta san lokacin da wani yaƙe ya ƙwace mata ba

"Ehh.. ehhh.. Mommah lafiya.. Kawai dai kin ga na zo dubawa ne ko na yi mantuwa a wajen." Ta yi ƙoƙarin ƙarasa maganar cikin dakiya dan kar ta fahimceta. Kallanta Mommah ta yi, ita tsoronta ɗaya ka da ta je akwai wani abun amma Didin ba ta gaya mata ba. Se dai kuma tun da har tace babu komai bari ta bar shi a haka ɗin.

"Toh shi kenan yanzu kin duba?"

"Ehh na duba babu komai." Didi ta faɗa a ranta tana jin babu daɗi na ƙaryar da ta yi wa Mommahn.

Ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ta zauna a kan gado, har se da Little ya kalleta. Ba ta sake fita daga ɗakin ba har se da dare da za ta fita kai masa coffee sannan ta ja hannun Little suka fita. Suna fitowa ya yi daidai da lokacin da Bad Man ke ƙoƙarin shiga ɗakinsa. Se kuwa Little ya zame hannunsa daga na Didi ya tafi da gudu yana faɗin

"Uncle.."

"Aww baby boy.." Bad ya faɗa yana ɗaga shi sama ya jefa sannan ya sauke shi ƙasa yana ta dariya. Kawai se ta tsaya tana kallansu kamar waɗansu da suka yi shekara a tare. Ga kuma mamakinsa da ya kamata na ganin ya yi murmushi har da sakin fuska kamar ba shi ba. Ashe da ma shi ma yana sakewa ya yi rayuwa kamar ya mutane? Ta tambayi kanta. Gefe guda kuma haushin Little ɗin ya kamata, kamar ta je ta ja shi ta mammamgare shi. Se dai se ta yi shiru tana jira ta ji ko ze sake shi ya taho shi kuma ya wuce ɗakinsa. Se ta ga ya ja hannunsa sun wuce ɗakin.

"Wai toh ko dama shi aka kawo wa Little ɗin ne?" Ta tambaya a shagwaɓe tana binsu da kallo, kamar akwai wanda ze amsa mata. Ta kai wajen minti 2 a tsaye kafin ta wuce kitchen.

Tana tafe tana saƙa ai dai yanzu idan ta je ze bata Little ɗin ta tafi da shi tunda dai dare ya yi. Da sallama ta shiga ɗakin kanta a ƙasa. Tana shirin wucewa ta ji yace

"Malama kin bar mana ƙofa a buɗe.." Ya faɗa ba tare da ya kalleta ba. Kai idan ma ba sanin muryarsa ka yi ba se ka ɗauka ba shi ya yi maganar ba. Sauke numfashi ta yi se ta juya a sukwane ta rufo ƙofar kafin ta juya har lokacin ba ta kalli inda suke ba. Kai tsaye wajen ta ƙarasa ta je ta ajje. Se ta saci kallansa yana kan gado yana danna system. Ya yin da Little ma ke kan gadon yana game, wanda da ka gan shi ka san bacci yake ji, saboda yanda yake lumshe ido. Se kawai ta yi shahada ta soma takawa dan ficewa daga ɗakin. Har ta kusa kaiwa ƙofar ta jiyo muryarsa.

"Heyy!!" Se ta dakata a inda take. Kafin ta juyo ya ɗora da faɗin

"Nemi waje ki zauna yaron nan ya yi bacci ki ɗauke shi.. ko kuwa ni zan kawo miki shi ne?" Ya ƙare a karo na farko tun shigowarta ɗakin yana watsa mata idanunsa..

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO59*

___Shiru ta yi a ranta tana maimaita abin da ya faɗa ɗin. Se take ji kamar kawai ta yi tafiyarta. Amma kuma idan ta tuna da cewar komai fa lalacewarsa mijinta ne, kuma umarni yake bata se ta ji jikinta ya yi sanyi. Hakan ne ya sanyata juyawa ta nemi waje ta zauna. A matuƙar takure take jinta burinta Little ya yi bacci, yace mata ta zo ta ɗauke shi. A karo na barkatai ta sake kallan Little wanda zuwa lokacin har baccin nasa ya yi nisa. Ta sauke ajiyar zuciya tana ƙoƙarin fara miƙewa. Se kuma ta koma kamar wadda aka dakatar. Ta ɗaga kai da niyyar satar kallansa, se idanunta suka faɗa cikin nasa. Sam ba ta yi tsammanin ganin idanunsa a kanta ba shi ya sa ma ta kalle shi, ban da haka da babu abin da ze sa ta kalli inda yake. Se da ya jefa mata wani kallo da ya fi kama da harara sannan ya ɗauke kansa yana wani ciccin magani.

"In zo in ɗauke shi?" Ta faɗa a sanyaye ba tare da ta kalle shi ba.

"Baccin be yi nisa ba." Ya bata amsar cikin basarwa. Ba ta sake cewa komai ba ta cigaba da zaman, dan ta fahimci kamar hadda son wahalar da ita da yake ne ya sa yake mata haka. Bayan shuɗewar wasu mintuna Bad Man ya miƙe kai tsaye kan mudubi ya nufa. Idanunsa ya shiga jefawa da alama wani abun yake nema. Zuwa can ya saka hannunsa ya buɗe drawer, nan ma dai rufeta ya yi a fili yana furta

"A'ah.." Cike da mamaki. Tun da ya soma dube duben nan ta ji hantar cikinta ta kaɗa. Ka da fa a ce abar nan tasa yake nema. Tuna hakan ne ya sanyata cigaba da sussuskuy da kai kamar munafuka tana kuma murza hannunta lokaci ɗaya. A hankali ya sake kallanta yana ganin yanda take kallan inda yake a fuzge. "Ko dai ita ta ɗauka?" Ya tambayi kansa. Ɗan cije lips ɗinsa ya yi na ƙasa yana soma takawa zuwa inda take. Hannu ya saka ya ɗagota daga zaunen da take. Ya zamana tana kallansa ne fuska da fuska. Ƙirjinta ne ya cigaba da harbawa tana ji kamar ta fashe da kuka.

"Ke kike ɗauke min bottles ɗina koh?" Ya yi maganar yana kafeta da waɗannan idanun nasa. Runtse idanunta ta yi ta rasa me za tace. Ji take kamar tace ba ita ba ce. Ji take kamar kuma ta fito fili ta faɗa masa cewa ita ce. Kamar ba za ta yi magana ba se kuma cikin ƙarfin hali ta soma faɗin.. bayan ta yi iya ƙoƙarinta wajen janye idanunta daga cikin nasa.

"Ehh ni ce.." Ta faɗa a fili se ka ɗauka wata boss ta koma. Nan kuwa tsoro ne fall cikin ranta, se dai tana ƙoƙarin ɓoye shi ne dan kar ya fahimta.

"Ke ce..?" Ya tambaya cike da mamakin ƙarfin halinta. Se ta jinjina kai tana wani haɗiye yawu. Shiru ya yi yana cigaba da nazarinta. Kamar ba Bad Man ba yace

"Ko me ya sa?"

"Saboda babu kyau.. Ni kuma ba zan iya ganin ka na saɓon Allah kuma na bari ba. Shi ya sa nake kwashewa ko hakan ze sa ka dena. Amma wallahi ka ji tsoron Allah ka dena don Allah.." Ta ƙare a raunane. Tun da ta soma maganar yake kallanta kamar wani saƙago. Mugun ƙarfin gwiwar da ya shigeta wanda ya bata dama har ta iya tsayawa gabansa ta faɗa masa waɗannan maganganun shi ne ya fi komai ba shi mamaki.

"Ke ki ke kwashewa ashe..?" Ya sake tambaya dan sake tabbatarwa.

"Ehh.. Amma ka yi haƙuri." Murmushin gefen baki ya yi yana sake tuna maganganun da ta faɗa masa. Se dai kafin ya ida ɗin ma ya ji ta ɗora da faɗin

"Kai musulmi ne.. wanda ke zaune da iyayensa. Ba ka tunanin idan har wata rana zancen ya kai gare su wani irin hali za su shiga?" Ta ɗan dakata tana ƙoƙarin yin baya da fuskarta saboda yanda kusancinta da tasa ya ƙaru.
Chapter 65 · 0% Book details