Sashe 6
A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Me ya faru kuka tsaya anan? Ko motar ce ta samu matsala?" Kallanta wata mata dake sanye da atamfa me kyau da mayafi ta yi tace
"Ai mun zo gidan.."
"Wai da gaske?" Ta tambaya har lokacin tsoro be gama fita daga kanta ba.
"Ƙwarai.. Ina amaryar tamu?" Ta amsa mata da hakan tana yin gaba zuwa wajen motar da Lulu ke ciki. Daidai lokacin da Cousin ɗin Ammi me suna Aunty Maryam, da kuma Baba uwani suka soma fito da Lulu daga cikin motar. Tuni wajen ya ɗauki guɗa cike da ƙwarewa. Ba dukansu ne suka shiga gidan ba, wasu se suka zauna cikin mota saboda Didi. Binsu da kallo Mami ta yi kamar wata doluwa, mamaki ya kasa barinta, ta yaya ma hakan ta faru? Anya kuwa Abba ya san wanda ya aurawa Lulu kuwa? Anya kuwa Lulu ta san waye ta aura da har ta yi biyayya ta yarda aka fito da ita daga gida?
"Tirƙashi..!" Ta faɗa a fili tana jinjina kai. Se kawai ta bi ayarin en shigar da amaryar gidanta dan ta ƙarasa kashe kwarkwatar idanunta. Har cikin gidan suka shigar da Lulu, ana cigaba da guɗa. Riƙe kanta Lulu kawai take yi, kada ta yi abin da ze janyo magana, ta sake zubarwa dasu Abba mutunci, a gaban dangi da wasu jama'ar da bata san ko su waye ba. Hakan ne yasa ta cigaba da tausar kanta har zuwa sanda ta ji ana ƙoƙarin zaunar da ita a ƙasa. Tarba ta musamman suka samu daga wajen Ummeey. Cikin mutunci da sanin ya kamata ta karɓesu. Matuƙa sun ji daɗin yanda ta karɓesun, hakan ne ya sanya suka ɗan saki jiki aka ɗan taɓa hira. Mami kam na gefe, bin gidan da kallo kawai take yi, zuciyarta a zafafe, tana ji kamar ta tashi ta yiwa duk wanda ke cikin ɗakin duka. Musamman ma Ummeey da farin cikinta ya kasa ɓoyuwa. Ji take kamar ta tashi ta shaƙeta, wato ai dole ta yi farin ciki, tunda an ɗakko er babban gida an kawo musu gida, ko banza za su dinga samun na sakawa a bakin salati daga mahaifin yarinyar.
"Ya dai kamata ku tashi a kai amarya gidanta. Ko dan sanin da kuka yi muna da aiki a gabanmu.." Mami ta faɗa cike da basarwa. Murmushi Ummeey kawai ta yi. Se wata ƙanwarta tace
"Ai babu damuwa ma. Muje a rakaku ɗakin amaryar.." ta faɗa tana miƙewa. Zuwa lokacin Mami ta gama tabbatar da da gasken dai nan ɗin shi ne gidan Lulu. Se kawai ta bi bayan su kamar wadda ba ta da laka. A haka har suka ƙarasa bakin ƙofar ɗakin Gwani da ya sha sabon fenti daidai da ƙarfinsu. Se sheƙi kuwa yake yi. Mukulli ɗayar ta saka ta buɗe sannan tace
"Bismillah.." ta faɗa sanda ta yi gaba. Babu ɓata lokaci suka soma shigewa cikin ɗakin. Madaidaicin ɗaki ne da shima ya sha fenti kamar daga waje. Duk da kasancewarsa a buɗe, hakan be hana zagaye wajen da labule masu kyau daidai gwargwado ba, hakan ne ya sa ba a iya ganin abin da ke cikin ɗakin, se dai idan an buɗe. Gefe guda kuma ɗakin da aka shigo da shi ne daga waje, ɗan ƙarami ne ba can ba. Shi ma an yi ƙoƙari wajen saka masa labule kamar irin na ɗakin, wankakku masu kyau, ƙall ƙall dasu. Se banɗaki dake cikin ɗakin da ake fara tararwa, shi ma madaidaici ne, a wanke fess kamar wanda aka gina shi yau, saboda mamallakinsa me tsafta ne, kamar yanda jikinsa yake haka ɗakinsa da komai nasa yake ƙall ƙall. Shi yasa duk da ɗakin nasa ba wani kyau ne da shi ba, amma da yake kullum cikin ƙalƙale shi yake yi, da kuma gyara shi tsaff yasa ko da be maka kyau ba, toh ze burgeka. Dukansu bin ɗakin suke yi da kallo, kamar dai yanda aka saba duk lokacin da aka je kai amarya gidanta. Kai tsaye yaye laluben da ya ƙawata ɗakin suka yi, inda gadon Gwani dake gyare tsaff kamar wanda mace ta gyara yake. Nan suka nufa. Anan suka ajje Lulu. Baba uwani ta ɗan yi mata faɗa a gaggauce sannan sukawa Ummeey sallama bayan sun shiga ɗayan ɗakin sun kalla sannan suka fice ba tare da sunwa Lulun sallama ba dan kar su kunnota. Se a lokacin Mami ta iya ƙarasawa kan gadon ta zauna, kai tsaye ta janyo Lulun tana fashewa da kuka. Da sauri Lulu ta ɗaga kai ta kalli Mamin dake cigaba da kuka kamar ƙaramar yarinya. Hankalin Lulu ya sake tashi, se dai bata iya cewa komai ba, har zuwa lokacin da Mamin tace
"Kar ki tambayeni dalilin yin kukana Lulu. Kalli irin gidan da aka kawoki a matsayin gidan mijinki.. Idan dai har da gaske ina kallanki a matsayin ɗiyata toh ya zama dole na yi kuka.. Lulu wannan wane irin gida ne? Me yasa Yaya ze miki haka? Ko dai be san wanda ya aura miki ba?" Ta yi maganar duka a lokaci ɗaya. Idan da Mami ta san yanda maganganunta ke sake baƙanta zuciyarta, suna sake tuna mata da Gwani da ta dena mata. Ita a yanzu wani gida da aka kawota, ko gidan da zata zauna duk ba damuwarta bane. Ita damuwarta ɗaya wanda aka aura mata, yaya za a yi ta rabu da shi? Dan duk wannan gidan ba zama za ta yi a cikinsa ba ballantana ta damu, gwara ta yi tunanin yanda za su rabu da Gwani tunda dai ta riga da ta faru ta ƙare.
"Na san suna can suna jirana.. Zan dawo gobe.." Se a lokacin Lulu ta iya buɗe baki da ƙyar tace cikin dashashshiyar muryarta
"Tafiya za ki yi Mami?"
"Ya zama dole Lulu. Amma abin da nake so dake kada ki sake ki bawa ɗan talakawa fuska ballantana har ya samu damar taɓaki.. Na faɗa miki wannan, na kuma san ba son shi kike ba. Toh idan ma kina tunanin tursasawa kanki zama cikin gidan nan ki dena, ni da kaina zan nema miki mafita. Za ki bar gidan nan cikin kwanciyar hankali ki koma gida."
"Da gaske Mami?"
"Ƙwarai kuwa.. Ke dai kawai ki kwantar da hankalinki.." Girgiza kai Lulu ta yi sanda idanunta dake a kumbure suka cika fall da ƙwalla. Maganar kwantar da hankali kam ai bata taso ba.
"Bari na je.. ki jira zuwana a safiyar gobe.." Lulu bata iya bata amsa ba, se binta kawai da ta yi da kallo har ta fice daga ɗakin. Se ta runtse idanunta har lokacin zafin da zuciyarta ke yi be ragu ba. Se dai maganar Mamin ta yi maganin wata daga cikin damuwarta. Ta kuma sanya ta bar ƙwaƙwalwarta ta huta a kan bulayin neman mafita.
... "Mom ki bar ni.. Tunda ya faɗa ya aikata ne.." Bad ya faɗa yana kallan Mom ɗin. Girgiza kai Mom ta yi tace
"A'ah Boy, ka bari tukunna mu gani mana.. Zuwa anjima zamu tabbatar da abin da ya faɗa ai.."
"Ya riga ya faɗa min wace yarinyar ce. So ki bar ni na je har gidansu, na saketa. Na san ze yi musu rashin daɗi.."
"Noo my son.. Ka san abin da yafi komai ciwo? A kawo yarinya gidan miji a saketa a ranar, ta koma gida.. Ya fi komai takaici. Dan haka ka yi haƙuri don Allah mu jira zuwan su.." Be ce komai ba illa kan gado da ya koma ya zauna fuskarsa a ɗinke tsaff.
"Ka dena fushin haka nan pls.." Mami ta faɗa tana dafa kafaɗarsa cikin rarrashi. Nan ma dai be tankata ba, se lumshe idanunsa da ya yi alamar ya ji abin da tace ɗin.
.. Tunda Mami ta fito jikinta ke a matuƙar sanyaye. Har zuwa lokacin da aka soma tafiya zuwa gidan Alhaji Matawalle. Tun daga bakin layin, Mami ta kasa haƙuri, se ta soma leƙe, ganin irin tamfatsetse kuma hamshaƙin layin da suka shigo. Haka suka cigaba da tafiya, basu suka tsaya ba, se da suka isa ƙofar wani ƙato, haɗaɗɗe kuma tamfatsetsen gida da a kallo ɗaya idan ka yiwa gidan za ka fahimci ya take duk wani gida dake cikin layin. Cikin ƙanƙanin lokaci aka wangale musu gate ɗin, wanda ke zagaye da mutane da dama, masu tsaron iya ƙofar wajen kenan. Babu ɓata lokaci suka danna kan motarsu zuwa cikin gidan. Ai Mami se ta kasa ko da ƙwaƙwƙwaran motsi ne. Ta cigaba da bin ko ina da kallo kamar wata er ƙauye. A bakin part ɗin Mommah suka tsaya, se en uwan Daddy suka soma fita daga cikin motar su. Duk da yanda kowannensu jikinsu ya yi sanyi da ganin irin hamshaƙin gidan da aka kawo er tahalika Didi, hakan be hana su soma ƙoƙarin fitowa da Didi ba. Se da suka ida fiddata sannan Mami ta yi iya ƙoƙarinta wajen fitowa daga cikin motar, duk da yanda zuciyarta ke bugawa. Se kawai ta cigaba da bin gidan da kallo, tana sake jefa idanunta lungu da saƙo na ko ina dan gama ganewa idanunta abin da ta soma gani. Cikin ƙanƙanin lokaci part ɗin Mommahn ya cika da guɗa ta ko ina. Baba uwani riƙe da Didi suka ƙarasa suka ajjeta. Cikin fara'a Mommah ta karɓesu cike da farin cikin ganinsu, dan ita dai tunda Daddyn ya faɗa mata zancen auren Areef ɗin ta ji hankalinta ya kwanta da hakan. Nan ma babu laifi se da suka ɗan taɓa hira se dai ba kamar yadda suka yi da Ummeey ba. Mami na gefe idanu sun yi tsilli tsilli tana cigaba da bin ɗakin da ya gama tafiya da imaninta da kallo.