← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 122

Sashe 86

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"In Sha Allah.." Daga haka matan suka wuce part ɗin Mommah, ya yin da mazan suka wuce ɗakin Bad Man.

Tuni Mommah ta shiga haba haba da sirikanta. Bayan kowaccensu ta yi wanka ta shirya tsaff cikin dogayen rigunan Didi. Se suka nemi waje suka zauna suka shiga hira sama sama. Shigowar Mommah ce ya sanya su katse hirar da suke. Ta ƙaraso da murmushi kan fuskarta tace

"Me za a dafa muku?"

"Mommah ni dai a ƙoshe nake.." Didi ta faɗa tana kallan Mommahn.

"Couscous.." Lulu ta faɗa dan ta tsaya ta yi tunani kawai shi ta ji tana sha'awar ci.

"Toh shi kenan Daughter.." Mommah ta faɗa, daga haka ta fice daga ɗakin. Ji take yau ɗin rana ta daban ce, dan haka ko me sirikanta ko 'ya'yanta ke so za ta tsaya ne ta musu ita da kanta.

"Wai ni kam Lulu yaushe kika zama acici ne?" Didi ta faɗa da mamaki tana kallan Lulu. Turo baki Lulu ta yi kamin tace

"Ni ɗin?"

"Eh fa.."

"Ba wani nan ni kam kawai yunwa nake ji." Jinjina kai Didi ta yi tace

"Toh ya miki kyau ai."

Mommah da kanta ta shiga kitchen, tare da taimakon Baba Atine cikin ƙanƙanin lokaci suka gama dambun couscous da ya ji kayan haɗi. Cikin ƙankanin lokaci sashen Mommahn ya ɗauki ƙamshin girkin Mommahn me daɗin shaƙa. Kwashe shi Mommah ta yi a duk inda ya dace, ta bawa Baba Atine ta fitar mata da waɗanda ta zuba cikin wasu ƙananan warmers. Se ta fito daga cikin kitchen ɗin, kai tsaye ta wuce ɗakinta inda a nan ne su Lulu ke zaune. Lulu na zaune kusa da Little da ke ta baccinsa. Mommah ta ƙarasa ta nemi waje ta zauna.

"Ku ɗan fito ku yi wani aikin lada mana.." Didi ce ta fara miƙewa kafin Lulu ma ta miƙe. Se suka bi bayan Mommah suka fice daga ɗakin. Ba tare da wata kunya ba Mommah ta ba su umarnin ɗaukar abincin kowacce ta kaiwa mijinta. Tura baki Lulu ta yi dan ita kam bacci ya soma fizgarta. Ya yin da ita dai Didi ba ta yi komai ba, ba kuma tace komai ba duk da sanin hali. Abin da kawai ta sani tun da har Mommah tace su yi kawai za su yi ne. Hannu Didi ta saka ta ɗauka, ganin da ta yi Lulu ba ta ɗauka ne ba ya sanyata watsa mata wata harara. Babu shiri ta saka hannu ta ɗauka tana cuno baki. Murmushi Mommah ta yi lokacin da suka fice daga ɗakin, wai yau ita ke da 'ya'ya biyu. Bayan su kuma har da sirikai biyu.

"Allah abun godiya.." Ta faɗa a fili tana sauke ajiyar zuciya.

... Fitowarsa daga wanka kenan, se a lokacin ya tuna da be taho da kowanne kaya ba, toh kenan me ze saka? Ya tambayi kansa. Daidai lokacin Bad Man ya shigo cikin ɗakin, ya saka hannu ya ɗauki wasu kaya da ke a ajje ya matsar da su kusa da Gwani yace

"Ka yi manage da waɗannan kafin gobe.." Kallan kayan Gwani ya yi, kafin ya saka hannu ya ɗauka. Wandon ya bi da kallo, irin wannan crazy ɗin ne mara kirki. Ya kalli Bad yace

"Wannan ɗin zan saka?" Bin wandon Bad Man ya yi da kallo. Shi sam be ma kula da wanda ya ɗauko ba se yanzu. Cikin basarwa yace

"Toh mene ne? Dan dai rana ɗaya? Na ga dai ba wani ne ze ganka ba." Jefar da wandon Gwani ya yi a kan gado ya nemi waje ya zauna a kan gadon lokaci ɗaya yana faɗin

"Ba zan saka ba wallahi." Ya yi maganar ya yi kici kicin da fuskarsa. Tilas hakan ya bawa Bad Man dariya. Ya saka hannu ya ɗaga wandon yana sake kalla.

"Yanzu me ye aibun wannan wandon Iyee?"

"Ka ba ni wandon mutunci Malam." Be ce komai ba Bad Man, se komawa da ya yi ya buɗe wardrobe ɗinsa ya shiga dubawa. Shi dai ya san kwata kwata ba shi da manyan kaya, dan ko Daddy ya ɗinka da shi bayarwa yake yi. Gaba ɗaya kayansa na kanti ne. Shi ya sa nau'in wandunansa duka ba su wuce crazy ko kuma normal jeans irin matsatstsen nan ba. A cikin jeans ɗin dai ya samu ya ɗakko wani me dama dama. Ya ƙarasa ya miƙawa Gwani yace

"Ga shi Malamin Addini.." Ya ƙare yana er dariya ƙasa ƙasa. Harara Gwani ya watsa masa ba tare da yace komai ba.

"Ohh duk ƙoƙarin da na yi ba ka gani ba koh? Ya yi.." Bad ya faɗa yana jinjina kai. Kai idan ka gansu se ka ɗauka sun fi shekara a tare. Ba za ka taɓa cewa da ma ba tare suka rayu ba, saboda kowannensu yana ji da miskilanci, amma kuma ga shi sun saki jiki suna ta maganarsu kamar ba su ba.

"Kawo.." Gwani ya faɗa yana miƙa masa hannu. Miƙa masa ya yi yana komawa gefe ya kwanta yana faɗin

"Bari na ga Malamin Addini cikin matsu.." Ya faɗa ƙasa ƙasa. Shi dai Gwani be kula shi ba ya shirya abinsa. Sosai fa Gwani ya fito ya yi wani mugun kyau abinsa. Yau ɗin se ya fita daban kamar ba shi ba. Shi dai ta ɓangarensa har ga Allah ya saka wandon ne a bisa lalura, dan kuwa haka nan kawai be ga abin da ze saka shi saka irin wandon nan ba.

"Kuma fa ka yi kyau.." Bad Man ya faɗa yana kallansa.

"Ka ji da shi.." Gwani ya ba shi amsa da hakan yana sake kwantar da sumar kansa.

"Wai ba a maka abun kirki ne?"

"Yi haƙuri, na gode." Gwani ya faɗi hakan. Murmushi kawai Bad Man ya yi yana komawa kan gadon ya sake kwantawa.

"Bari na ɗan fita.. zan shigo zuwa an jima." Gwani ya yi maganar yana kallan Bad Man.

"Ohk.." Ya amsa da hakan. Daga haka Gwani ya fice daga ɗakin zuwa palour, ko ze samu ya yi tunani a cikin nutsuwa. Dan ya ga alama idan suna tare da Bad Man ɗin ba ze samu ya yi tunani da kyau ba. Sosai hakan ya bawa Bad Man ma dama wajen zama ya yi tunanin da ya aure su a yau ɗin.

Yana zaune a kan kujerar ɗakin ya yi shiru.. Har yanzu jin abun yake kamar a mafarki, wai su Ummeey ba su ne suka haife shi ba. Amma suka riƙe shi tsayin shekaru ba tare da sun taɓa faɗa masa ba, ko kuma su yi wani abu da ze nuna ba su suka haife shi ba. Kullum soyayyarsu a gare shi ƙaruwa take yi. Kullum burinsu be wuce a kansa ba. Duk wani fatansu na kansa. Se ga shi yau an wayi gari ashe ma ba su ne iyayensa ba. Kenan ya soyayyar iyaye take? Shi dai tun da yake be san wani abu ba ban da soyayya. Dan kuwa Ummeey da Abeey sun nuna masa so, wanda har abada ba ze taɓa mantawa ba. Rayuwarsa da su irin abun nan ne da ake kira wanda ba za a iya mantawa ba. A ko da yaushe abubuwa da dama za su zama waɗanda ze din ga tunawa a matsayin lokuta mafiya tsada kuma masu daraja a cikin rayuwarsa. Gefe guda kuma tunanin yanda aka raba shi da mahaifiyarsa da ɗan uwansa shi ma ya kasa barinsa. Dan haka se ya zamana ya yi shiru ne kawai a fili, amma cikin zuciyarsa cunkushe take da tunanuka kala kala. A daidai wannan lokacin Lulu da Didi suka yi sallama cikin ɗakin. Ya riga ya saba, duk nisan tunanin da yake da wuya a yi magana be ji ba. Dan haka suna yin sallamar ya ji, ya amsa sallamar ba tare da ya kalle su ba.

"Barka da wannan lokacin Ya mu'allim.." Didi ta faɗa cike da girmamawa. Se a lokacin sannan ya kalleta. Ya yakice tunanin ya ƙaƙalo murmushi yace

"Barka dai Afrah.. Ki na lafiya?" Se da suka gaisa sannan ta miƙe a sukwane, duk da yanda take jin kunya na kamata haka dai ta daure ta durfafi ɗakin nasa. Da ta kwantar da hankalinta ma shi Gwani hankalinsa ma ba ya nan. Dan tun shigowarsu hankalinsa ya koma kan matarsa. Zuwa lokacin da suke gaisawa da Didi a lokacin ne kuma Lulu ta samu kanta da tsayawa tana kallansa. Tun da take ba ta taɓa ganinsa da irin wannan shigar ba, se ya fita daban, ya zama kamar ba shi ba. Ita kam ta yi mamakin ganinsa da wannan shigar. Se dai ko mahassadi ya gan shi ya san ya yi kyau. Kansa a buɗe ba kamar ko yaushe ba. Kyakkyawar baƙar sumar kansa a kwance luff luff. Damatsan fararan hannunsa a waje, wanda suka bayyanar da murɗaɗɗen hannunsa me jan hankali. Fahimtar da ta yi yana shirin dawo da dubansa kanta ne ya sanyata saurin ɗauke nata idanun tana maidawa kan abincin.

"Barka.." ta faɗa har lokacin ba ta ɗago ba.

"Barkanki dai.. Ina fata ki na lafiya?" Ya tambaya cike da kulawa. Ita wallahi idan yana wani abun mamaki yake bata. Kawai se ta jinjina kai tace

"Eh.." Daga haka ta miƙe dan ficewa daga ɗakin.

"Tafiya za ki yi?" Ya yi maganar a hankali. Kafin tace komai ya ɗora da faɗin

"Yanzu tafiya za ki yi? Ba za ki tsaya in din ga ganinki ba ko da hakan ze rage abin da nake ji cikin zuciyata ba?" Ba ta san lokacin da ta ɗaga idanunta ta kalle shi ba. Ya lumshe mata idanu yana buɗewa a cikin nata idanun. Ta kautar da idanunta da sauri tana zumɓuro baki gaba.

"Toh ni bacci zan yi.." Ta faɗa kamar a shagwaɓe, se dai sam ba ta san haka maganar ta fito ba. Dan ita ta yi ne kawai ba da wata manufa ba. Kawai tsayawa ya yi yana kallanta ba tare da yace komai ba. Da ƙyar dai ya sake kokawa da zuciyarsa yace
Chapter 86 · 0% Book details