Sashe 93
A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gwajin farko da aka yi wa Lulu aka tabbatar musu da cewa tana ɗauke da juna biyu ne.. Kwantar da kansa ya yi a kan kujerar da yake kai wani irin farin ciki mara misaltuwa na mamaye shi. Gaba ɗaya ya ma rasa a wanne fanni ze iya kwatanta farin cikin da ya tsinci kansa a ciki. Abin da dai ya sani kawai shi ne wannan ranar na ɗaya daga cikin ranaku mafiya daraja da kuma muhimmanci a rayuwarsa. Da gasken dai ya kusa zama uba. Lallai ikon Allah ya wuce gaban wasa. Be taɓa tsammanin hakan ba wallahi. Se ga shi Allah Ya ba shi a lokacin da dukkansu ba su yi tsammani ba. Kawai se ya zube a wajen ya yi sujudush-shukr. Ya miƙe yana sake jin farin cikin da ke sake mamaye shi. Ji yake kamar ya fi kowanne ɗa namiji dace da kuma farin ciki a yau ɗin nan. A ɓangaren Lulu kuwa shiru ta yi na tsawon minti 1 ba tare da tace komai ba se kallan waje ɗaya kawai da take yi kamar wadda ta zare. Ciki? Ita? Cikin ma na Gwani kenan? Shin me ya kamata ta yi? A tunaninta baƙin ciki, ƙunci da kuma takaici na har abada shi ne ze zo mata a yanzun da aka sanar da ita tana ɗauke da cikin Gwani. Se dai ga mamakinta maimakon ta ji wannan tsanar da ta yi masa tuntuni ta yi tasiri a kan cikinsa da ake maganar tana ɗauke da shi, se ta ji saɓanin haka. Dan kuwa wani irin farin ciki ne ta ji ya ziyarceta. Cikin lokaci ƙanƙani ta soma jin wata irin ƙaunar abin da ke cikin nata. Ba ta taɓa tunanin haka ba, ba ta taɓa kawo haka cikin ranta ba. Duk kuma da tunanin nan da take, hakan be chanja yanayin da zuciyarta ke ciki ba. A hankali ta kai hannunta kan cikinta ta shafa, kawai se murmushi ya suɓuce a kan fuskarta. Tun daga nesa yake kallanta tsayin lokaci ba tare da ta sani ba. Addu'a yake yi cikin zuciyarsa Allah ya kawo masa komai cikin sauƙi. Ya san yanzu Lulun ta chanja ba kamar da ba. Se dai har yanzu be sani ba, tana son shi ko ba ta son shi? Za ta iya zama da wani abu da ya dangance shi a jikinta ko kuwa a'ah? Mene ne ze biyo baya bayan shirun nan da ta yi? Tunanukan da ke sanya shi faɗuwar gaba kenan. Sam ya kasa ƙarasawa ya tunkareta ballantana ya ji wani abu daga gareta. Dalili kenan da ya saka shi tsayawa yana kallanta cike da tunanin ta ina za su fara. Se dai ga shi abin da be taɓa tsammani ba shi ne yanda ya ga farin cikin da ake yawan samu daga wajen kowacce uwa a lokacin da aka shaida mata tana ɗauke da juna biyu musamman a karon farko. Be zata ba, be yi tsammani ba ko kaɗan. Dalili kenan da ya sa be san lokacin da wani ƙawataccen murmushi ya suɓuce a kan fuskarsa ba. A hankali ya shiga takawa zuwa inda take zaune. Kamar yace mata wani abu, se dai be ce ba. A nutse fuskarsa ɗauke da annurin da ya kasa barin fuskarsa yace
"Mu wuce koh?" Ba tare da ta kalle shi ba ta miƙe a hankali ta shiga takawa. Ji ya yi kamar ya saka hannu ya ɗagata gaba ɗaya ya fitar da ita daga ɗakin. Se dai kawai ya bita a baya har suka fice daga asibitin.
Sun fi minti 5 da soma tafiya babu wanda yacewa da wani uffan. Zuwa can dai ya kaasa haƙuri, farin cikin da yake ciki yana da yawa. Yanda yake jin Lulun a zuciyarsa kullum ƙara haɓɓaka yake fiye da zaton me zato. Kawai se ya saka hannunsa ya kamo nata ya riƙe sosai, ta yadda ko da ta yi tunanin ƙwacewa ma ba za ta iya ba. Da sauri ta juyo ta kalle shi. Ya zuba mata idanunsa ba tare da niyyar janyewa ba. Tare ta yi amfani wajen ƙoƙarin janye idanunta da kuma hannunta amma ta kasa. Se ta narkar da fuska kafin ta buɗe baki tace
"Don Allah ka sake ni." Idonsa ya ɗaga mata guda ɗaya yana murza hannunta. Hakan ya bata damar janye nata idanun tana maida shi kan hannunta. A hankali kamar me raɗa ya shiga furta
"Allah Ya yi miki albarka Afaaf.. Allah Ya saka miki da alkhairi, Ya albarkaci abin da ke cikinki.. A karo na farko zan yi amfani da wannan damar wajen sanar da ke ina sonki. Ina ƙaunarki.." Ya ƙare yana sake zuba mata duk wani nauyi da idanunsa. Ba ta san lokacin da ta ɗaga kai ta sake kallansa ba. Se dai duk da yanda jikinta ya yi sanyi hakan be hanata janye hannunta ba. A sukwane ta koma gefe ta zauna tana jin yanda zuciyarta ta shiga harbawa da ƙarfi. Kamar wani maraya, kamar kuma ba Gwani ba cikin sanyi ya furta
"Ki taimaka ki amsa min Afaaf.. Ko da ba ki ce ki na sona ba dan na san da ma ba sona ake yi ba koh?" Ya ƙare kamar wani maraya..
"Ehh." Ta faɗa tana ɗauke kai. Be san dalilin da ya sa sam be ji zafin amsar da ta ba shi ba. Ko kuma mamakin hakan ya sanya shi ka sa furta komai, se hakan ba ta faru ba. Hasalima be san dalilin da ya sa be ɗauki amsar tata a matsayin wadda ta fito daga can cikin zuciyarta ba. Duk da dai abu ne a bayyane, ya san ba son na shi take ba. Amma kuma In Sha Allah cikin kwana kaɗan ze yi amfani da wannan cikin da Allah Ya azurtasu da shi ya koya mata son shi.
Tun kafin su ƙarasa cikin gidan kaɗe-kaɗe da bushe-bushe irin na gidan sarauta yake ziyartar kunnuwansu. Dakatawar da drivern ya yi ne ya sanya Gwani ɗaga ido ya kalle shi daidai lokacin da yake faɗin
"Da alama Yallaɓai ya yi baƙi daga gidan sarauta.." Ya faɗa yana sake leƙawa ko ze iya gano yawan motocin da yake hange.
"Babu yanda za a yi mu wuce kenan?" Gwani ya tambaya shi ma yana kallan yawan motocin, lokaci ɗaya kuma kaɗe-kaɗen na cigaba da tashi a nutse, cikin kuma ƙwarewa da sanin ya kamata. Sun ɗauki wajen minti 2 a haka kafin drivern ya samu ya shige cikin gidan. Daidai lokacin da Gwani ya maida dubansa kan Lulu. Duk da Hijab ne a jikinta hakan be hanata yin amfani da hannunta ba wajen ɗora shi a kan cikin nata. Jin abun take kamar a mafarki, ji kuma take kamar hakan ma ba ze taɓa zama gaskiya ba. Ita dai Lulun ita ce ke ɗauke da ciki. Ciki wanda ake haihuwa. Kenan ita ma dab take da ɗaukar jariri ko jaririya, ba ma na mutane da suke ɗauka ba, nata mallakinta na kanta, wanda za ta haifa da kanta. A daidai nan ne wani murmushi ya suɓuce mata. Ta kai hannunta guda ɗaya ta kare fuskarta. Kasa haƙuri ya yi. Har ga Allah idan tana tsiwa kyau take yi masa. Ga shi kuma da ma yana so ya ji muryarta amma se basarwa take yi. Hakan ne ya sanya shi gyara zama yana faɗin
"Ya kuma naga ki na murmushi? Kar dai ki ce min ki na son abun cikin naki." Ɗaga kai ta yi ta kalle shi kamar irin kallan lallai ya ma raina mata hankali. Se kuma ta tura baki tana ɗauke kanta, ciki ciki tace
"Ai dai na ga a cikina yake ba na wani ba."
"Iyeeee me ye kike cewa? Lallai kin girma.. Amma kuma ko kin manta ajiyata ce?" Ya ƙare yana kafeta da idanunsa bayan ya ɗage girarsa guda ɗaya lokaci ɗaya yana cijar gefen lips ɗinsa na ƙasa. Yanzu ma kallansa ta yi da sauri kamar ɗazu. Se dai yanzu da sauri ta janye idanunta dan wallahi ita idan ya yi wani abun yanzu mamaki yake bata. Se ta ga kamar ba shi ba. Bayan surutu har da rashin kunya duka ya koyo. Se ta sake zunkuɗa baki gaba tana haɗe rai, ita a lallai dole kar ma ya ga fuska bare ya sake kawo mata irin wannan maganar da ta ji kamar ƙasa ta tsage ta shige dan kunya. Hannu ta kai da sauri ta buɗe ƙofar tana ƙoƙarin ficewa. Ya yi saurin dakatar da ita ta hanyar riƙo hannunta da kuma faɗin
"Yi a hankali.. saboda ajiyata.." Ya ƙare cikin basarwa ba kuma tare da ya kalleta ba. Dakatawar ta yi amma ba tace komai ba dan kamar ta fahimce shi so yake ya kunnota. Da kansa ya fita ya buɗe mata ƙofar, a hankali ta sauko. Daidai lokacin da ta ida saukowa ɗin idanun Gwani suka sauka a kan masu fitowa daga cikin ɗaya daga cikin motocin da suka riga su shigowa cikin gidan. Da mamaki ya ɗan ƙanƙance idanunsa dan tabbatar da ita ɗin ce. Cikin sakanni kaɗan idanunsa suka tabbatar masa da ita ɗin ce, lokacin da ta fi kusa da shi.. Kenan ya aka yi ya ganta a nan? Ya tambayi kansa..
✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO74*
___A hankali kamar me yin magana da wanin da ba ya so a ji yace
"Maama.." Shi dai a sanin da ya mata tun zuwansa gidan nan er uwa ce ga Mommah. Se ga shi kuma yanzu ya ganta tare da wasu mutane da ke nuni da daga gidan sarauta suke. Ganin hakan ba lallai yana da wani amfani a wajensa ba ya sanya shi maida dubansa kan Lulu.
"Mu je na raka ki.." Ya yi maganar yana soma tafiya tun kafin tace komai. Da ma ba ta yi niyyar cewa komai ɗin ba. Se kawai ta bi bayan nasa zuwa sashen Mommahn.
... "Ni fa Yallaɓai har yanzu mamaki nake.." Mommah ta faɗa maɗaukakin mamaki na bayyana a kan fuskarta. Jinjina kai Daddy ya yi kafin yace