← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 122

Sashe 50

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ehh.." ya amsa mata lokacin da shi ma ya fara tafiyar dan ficewa daga ɗakin. Tare suka fito daga cikin ɗakin. Mom ta zuba ido ta ga ko ze yi hanyar ɗakin da ta tabbatar Didi na ciki. Se ta ga ko kallan wajen ma be yi ba. Ta yi murmushi tana tuna irin macen da za ta zaɓawa Areef ɗin. Er gidan manyan mutane, masu arziƙi. Kai abubuwa da dama dai duk ta ci burinsu a kan Bad Man ɗin, musamman lokacin aurensa.

... A bakin layin da ze sadaka da gidan Bad Man ya yi parking na motarsa. Kusan a tare shi da Gwani suka kalli layin. Daga inda suke suna iya hangen fita da kuma shigar mata da maza yawanci kowannensu sanye cikin kayan mutunci, kai se ka rantse gidan arziƙi suke shiga.

"Ya za a yi?" Bad Man ya faɗa bayan ya kalli Gwani. Sauke ajiyar zuciya Gwani ya yi kafin yace

"Ina ganin mu sauka.. mu saka a kira mana ita. Ga wani waje can za mu iya yin magana a can." Ya ƙare maganar yana nuna wani waje da ke gefen gidan.

"Ohk." Bad Man ya faɗa yana ficewa daga cikin motar. Kusan a tare suka fita daga motar. Babu ɓata lokaci suka soma takawa zuwa ƙofar gida. Cikin ƙanƙanin lokaci idanun mutane da dama suka dawo kansu. Musamman waɗanda suka san Areef Matawalle. Tuni mutane suka zuba na mujiya dan ganin abin da ze faru su je su yaɗa.

A yanda suke tafiya kai ba za ka taɓa cewa wannan ne ɗan gidan me kuɗi wannan kuma akasinsa ba. A haka har suka ƙarasa wannan wajen da Gwani ya nuna musu. A nan suka nemi waje suka tsaya. Ba tare da wani yace da ɗan uwansa uffan ba. Har zuwa lokacin da wani ɗan saurayi ya zo wucewa ze shige cikin gidan. Da sauri Gwani ya ƙarasa ya miƙa masa hannu suka gaisa. Kallansa kawai saurayin yake yi kamar wanda ya ga baƙon halitta.

"Gidan nan za ka shiga?" Gwani ya tambaya. Jinjina kai saurayin ya yi da sauri yana jira ya ji amsar da za ta fito daga bakin Gwanin. Cikin nutsuwa Gwani yace

"Idan ka shiga ka ce mu na son magana da Ladi.. mu na tsaye a can.." Ko a yanayin maganar Gwanin ya isa a fahimci hankalinsa. Se dai shi mamakinsa ɗaya a ce duk wannan kamalar tasa, da zubin muminai. Da kamanni da Allah ya masa irin na larabawa a ce ya zo wajen karuwa. Wannan wace irin lalacewa ce? Ya tambayi kansa duk da cewa shi ɗin ba mutumin kirki ba ne. Amma Gwanin ya ba shi mamaki. Kawai se ya sauke numfashi yace

"Toh.." Daga haka ya juya ya wuce cikin gidan. Komawa Gwani ya yi inda ya bar Bad Man tsaye yana waya da Lucky abokin nan nasa. Bayan wajen minti 10 se ga Jakadiya Ladi ta fito sanye cikin abaya da mayafinta. Fuskar nan ta sake yin ɗau saboda uban mai da ya sake ratsata. Hango mutanen da ke tsaye da ta yi ne waɗanda aka ce su ke sallama da ita ya sanyata jin wani irin daɗi. Ko ba komai ta san yau ɗin ta yi babban kamu, dan kuwa tun kafin ta ƙaraso idanunta sun gama nuna mata tsananin kyawunsu. Har wani chanja tafiya ta yi lokacin da ta kusa ƙarasowa inda suke. Ta shiga ɗan karkaɗa jikinta saboda su yaba. Duk da ba ta san me ya kawo su ba.

"Ka bar ni da ita.." Bad Man ya yi maganar ciki ciki. Wanda idan ba Gwani dake kusa da shi ba babu wanda ze iya jin abin da ya faɗa ɗin. Jin abin da ya faɗa ɗin ne ya sanya Gwani cigaba da tsayawa yayin da Bad Man ya dawo gefensa. Se ta yi murmushi tana faɗin

"Sannun ku da zuwa." Ji ya yi kamar ya share saboda yanda wani takaici ya rufe shi. Musamman yanda wani chanjin iskar da yake shaƙa ta sauya lokacin da suka ɗan samu kusanci. Se dai tuna abin da suke da buƙata ya sanya shi faɗin

"Yawwah.."

"Memakon ku shigo ciki.. Ai ba kwa tsaya a nan ba. Ka san mutane da sa ido, yanzu se ka ji ana yi da mu." Gyara tsayuwarsa Bad Man ya yi yana iya ƙoƙarinsa wajen daurewa ya yi maganar da ita. Ban da haka da ko kallan inda take ba ze yi ba ballantana ya mata magana.

"Babu damuwa.. Ki na ji?" Ya faɗa yana karɓar wayar hannun Gwani.

"Ehh ina ji." Ta yi maganar tana sake gyara tsayuwa.

"Akwai wani hoto da na gani na kuma san aikinki ne. So ni ma ina da buƙatar ai min irin aikin a kan wata yarinya.. shi ya sa na neme ki." Ya ƙare yana miƙa mata wayar. Hannu ta saka ta karɓa, tana jin kanta na wani irin tiriri. Tun da har irin mutanen nan kan zo domin ta saka ai musu aiki ai ita kam shau shau da mai. Ba tare da ta damu ta san a inda ya san ita ce ta saka aka yi aikin ba tace bayan ta gama kallan hoton.

"Ohh wannan ƙaramin aikin..?" Ta faɗa dan ya sake sanin fiye da wannan ɗin ma fa za ta iya. Ta san ze sake mata kallan babban kai. Gwani dake gefe ya ji abin da ta faɗa se ya sake bayar da duk wani hankalinsa kanta dan jin abin da za ta faɗa.

"Oh ƙarami ne ma wannan? Ki ce in saki jiki za a min wanda yafi wannan" Bad Man ya faɗa yana murmushin da iyakacinsa kan fuskarsa. Tana cigaba da kallan hoton tace

"Ehh ƙarami ne mana.. Yarinyar ce kawai na sota kamar me.. se dai ita ta ƙi yadda da ni ita wai er gidan masu mutunci. Shi ya sa na sa aka mata haka kowa ma ya rasa har iyayen nata." Ta ƙare maganar tana kallansa

"Gaskiya ne.." Bad Man ya faɗa se dai lokacin fuskarsa ta soma komawa ainahin tasa ba wadda ya aro ba.

"Ina so a min makamancinsa.. se dai yanzu ana jirana dan haka zan dawo mu ƙarasa magana."

"Toh ba damuwa, duk lokacin da kake so kawai ka zo."

"Yanzu da mutane a ciki ne?" Ya sake tambaya yana karɓar wayar, dan yau ɗin so yake ya gama bugar cikinta kafin su bar ƙofar gidan nan.

"Ehh ehh.. Amma idan ɗaki kake so ai akwai nawa da nake saukar baƙina na musamman." Ta ƙare tana wanshare baki. Saboda takaici shiru ya yi yana jin zuciyarsa na masa zafi. Kamar ya tafi ya bar wajen tun da ya gama jin abin da yake son ji. Se dai gudun kar ta fahimci wani abun ya sanya shi daurewa. Se dai muryarsa a cunkushe yace

"Babu damuwa.. Ai zan dawo." Kafin ta sake cewa wani abun har ya bar wajen dan idan be yi da gaske ba ze iya ɗauketa da mari.

"Toh se kun dawo." Ta faɗa tana binsu da kallo lokacin da suka shige cikin motar Bad Man ɗin. Se ta sake jin kanta na wani irin tiriri. Se dai ganin yanda mutane ke kallanta ya sanyata haɗe ranta tana komawa cikin gidan.

"Ina matuƙar godiya. Allah ya saka da alkhairi." Gwani ya faɗa yana miƙawa Bad Man hannu. Shi ma nasa hannun ya miƙa sannan yace

"Babu damuwa. Gobe ba na da lokaci.. Zuwa jibi se mu ƙarasa abin da ya rage mana. Yanzu dai ka ji gaskiyar al'amari.."

"Ƙwarai kuwa.. Abin da ya rage kaɗai tarwatsa gidan nan kamar yanda na yi buri. Ita kanta wannan ɗin kuma ina son miƙata wajen hukuma dan a hukunta ta. Ba ma ita kaɗai ba.. ka yi haƙuri amma har da Abokinka.." Kamar ba shi ba Bad Man ya yi murmushi yace

"Babu komai.. Ni me taimaka maka ne ma."

"Ina godiya." Gwani ya sake faɗa. Dan babu ƙarya ya mugun jin daɗin taimakon nan da Bad Man ɗin ya yi masa. Daga haka ya tashi motar suka bar wajen. Ba su yi nisa ba Gwani ya sauka, dan ba ya son takura masa kuma. Bayan wannan taimakon da ya masa se ya sake kai shi gida kuma. Dan haka ya sauka ya tari mota ta kai shi gida.

Cike da mamaki yake kallan Lulu dake yanka albasa a zaune a tsakar gidan. Ummeey na zaune gefenta tana tsince zogale. Se ya kaasa ɗauke idanunsa daga kanta, wani abu me kama da shauƙin ganinta na kama shi. Uwa uba kuma da ya ganta tana taya mahaifiyarsa girki. Ga kuma waccan Ladin da ta gama wanketa tass a idanunsa ba tare da ta sani ba. Duk da shi ɗin da ma be taɓa zarginta ba amma dai yana buƙatar tabbatar da gaskiyar al'amari ko dan a yi wa tufkar hanci. Ba ƙaramin kyau ta yi ba daga inda take zaune. Duk da shigar dai kamar ta ko yaushe ce da take kindima uban hijabin nan. Se dai farar fuskarta ta yi matuƙar kyau cikin hijab ɗin da kalarsa da ɗauki fatar jikinta.

"A'ah Affan.. ka dawo?" Ummeey ta faɗa tana kallansa. Se a lokacin ya ƙarasa shigowa cikin gidan da murmushi kan fuskarsa yace

"Ehh Ummeey.. sannu da hutawa."

"Yawwah.." ya ƙare yana maida dubansa kan Lulu yana jira ya ji ko za tace wani abu ko dan ka da Ummeeyn ta saka ayar tambaya.

"Sannu da zuwa.." ya ji ta faɗa kamar wadda aka wa dole. Wani sanyi ya ji har cikin ransa. Bayan haka kuma ya san ita kanta Ummeey za ta ji daɗi.

"Yawwah kin wuni lafiya?" Da ma tana faɗa ta miƙe. Dan haka ba ta kula shi ba ta kalli Ummeey tace

"Ummeey ga albasar nan bari na je ɗaki."
Chapter 50 · 0% Book details