← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 122

Sashe 56

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

___ Lokacin da ya shigo cikin gidan Ummeey ba ta tsakar gidan, dan haka kai tsaye kawai se ya wuce ɗakin nasa. A hankali ya kalli kan gadon cike da fatan ganin fuskarta. Se dai kamar ɗazun yanzun ma har kanta a lulluɓe yake se dai baccin take yi. Sauke ajiyar zuciya ya yi lokacin da yake ajje ledar hannunsa a kan side drawer. Ficewa ya yi daga ɗakin dan ya ƙara mata lokaci ya barta ta yi baccin sosai. Ba shi ya dawo ba se bayan wajen awa 2 duk da lokaci zuwa lokaci ya kan dawo ya duba ya ganta sannan ya koma. Dan duk da be fita gaba ɗaya ba kuma ya san idan ta tashin ba lallai kirki ya haɗa su ba, ji yake kamar idan ya tafi ya ƙyaleta be yi mata adalci ba.

Daidai lokacin da ya shigo ya yi daidai da lokacin da take ƙoƙarin komawa baccin da ta tashi daga shi. Da sauri ya ƙarasa inda take a hankali kuma a tausashe yace

"Kar ki kwanta.. ki tashi ki samu ki ci wani abun.." Shiru ta yi tana cigaba da ƙoƙarin kwantawar. Hannu ya saka da niyyar riƙota, ta kuwa tattaro duk wani kuzarinta ta buɗe baki tace

"A'ah...!!! Ba na ci.." ta faɗa da ɗan ƙarfi.

"Ya Allah!.." ya faɗa hannunsa dafe da goshinsa. Sam ba ya son ta sake takurawa kanta. Ba ya son ya sake jawa kansa sabon haushinsa da take ji. Se dai koma mene tana buƙatar taimako, amma kuma ya ga duk da haka ba ta so. Duk da yanayinta kaɗai ya isa ya nuna halin da take ciki. Ya sauke ajiyar zuciya yana duba agogon wayarsa. Lokaci ya ja babu laifi, har kuma zuwa lokacin ba ta saka komai a bakinta ba. Shi wallahi tausayi ma take ba shi. Shi ya sa ma yake cigaba da lallaɓata, dan kome za ta yi ba kowa ne ya ka fa face shi. Ya kuma san ya riga ya tarowa kansa match. Ba tare da ya sake cewa komai ba ya fice daga ɗakin. Ita kuma tana kwance cikin ɗakin duk da ta gaji da kwanciyar saboda ba ma ta daɗe da farkawa ba. Kawai dai ta fi jin daɗin kwanciyar ne shi ya sa ta kwanta. Sam ba ta yi tsammani ba se jin sallamar Ummeey ta yi cikin ɗakin. Kalar kunyar da ta ji ɗazun ta sake yi mata dirar mikiya. Wai ita kam da wane ido za ta cigaba da kallan Ummeey ne bayan fahimtar abin da ya faru?

"Afaaf.." Ummeey ta kira sunanta a hankali. Yanzu kam babu musu ta miƙe zaune tana amsa kiran da

"Na'am.." Se dai sam ta ƙi kallan Ummeeyn.

"Gyara zamanki ki ci abinci kin ji 'yata? Ai ba kya zauna babu abinci ba.. Ban da galabaita babu abin da za ki yi.." jinjina kai kawai ta yi dan ta kasa buɗe baki ta yi magana, ta kuma kasa yi wa Ummeeyn musu. Mamakinta ɗaya kuma yanda rashin kunyar Gwanin ta kai haka.. Wato shi ko a jikinsa dan Ummeey ta sani. Har da wani zuwa ya kirata dan ta ƙi cin abinci, ko ina ruwansa? Se ta kai hannu ta share idanunta da ƙwalla ta taru. Daidai lokacin da Ummeey ta miƙa mata abinci cikin plate tace

"Ki samu ki ci ko yaya ne Uhmm?" Babu yanda ta iya dan ko doguwar magana ma ba ta so ta haɗata da Ummeeyn. Haka ta ja plate ɗin ta shiga tsakurar abincin da take jinsa tamkar magani take taunawa. Cigaba ta yi da turawa kawai ko da za ta dawo da shi. Da dai ta ga da gasken idan ba ta yi wasa ba za ta iya dawo da shi ta kuma san ba ƙaramin galabaita za ta yi ba ya sanyata ɗaukar ruwan da Ummeyn ta ajje mata ta kafa kanta, se da ta shanye shi tass sannan ta ajje tana ajje numfashi a gurguje.

"Da kin ƙara ko kaɗan ne ai.." Ummeey ta faɗa tana kallanta. A karon farko ta buɗe baki da ƙyar tana sauke numfashi tace

"Ummeey Allah ya ishe ni.." ta ƙare fuskarta kamar za ta yi kuka.

"Toh shi kenan.. Anjima se ki ƙara.."

"Tohm." Ta amsa da hakan tun kafin Ummeey ta dire maganarta. Se a lokacin sannan Ummeey ta fita daga ɗakin. Ya yin da ita kuma ta jinginar da kanta jikin gadon tana sauke numfashi a kai a kai.

.. Ba tare da ya kalleta ba ya shiga shimfiɗa bargon da ya shigo da shi. Ai ba ta san lokacin da ta miƙe zaune dandagarya ba. Nufinsa cikin ɗakin ze kwana? Bayan tana ciki? Ai ko karen hauka ne ya cijeta ba za ta kwana cikin ɗakin da yake ba. Haka kurum? Zamowa ta ƙarasa yi daga kan gadon hannunta dafe da kan gadon ta soma takawa dan ficewa daga ɗakin. Ita ta gwammace ta kwana ko ma a ina ne da dai ta kwana ɗaki ɗaya da shi.

"Ina za ki je?" Ta ɗauke kai duk da yanda zuciyarta ke harbawa dan kuwa yanzun wani shahararren tsoronsa take ji.

"Ni ka matsa min na fita.. Ba zan kwana a nan ɗakin ba.. Allah ba zan kwana ba.." ta ƙare ba tare da ta kalle shi ba. Hawayen kuma da yanzun kamar arharsu take ji har sun wanke mata fuska saboda yanda ta ga ya kare mata hanya kamar ma ba ze barta ta wuce ba.

"Ohh shi kam yau ya ga ta kansa.. wannan yarinya wannan yarinya.." ya raya hakan a cikin ransa. A fili kuma se cewa ya yi

"Shi kenan.. Ni ne koh? Maza ke ki yi kwanciyarki fita zan yi ma daga ɗakin gaba ɗaya kin gani..?" Ya yi maganar yana ɗaukar pillow da bargo. Be jira ta amsa masa ba ya juyo gareta a hankali duk da ta ƙi kallansa yace

"Ki kula da kan ki... idan ba ki ki daɗin jikin naki ba ki sake shiga cikin ruwan zafi.." Ya faɗi kamar yanda ya ga Ummeey ta mata ɗazun. Daga haka ya fice daga ɗakin da sauri. Kawai se ta fashe da sabon kuka fahimtar abin da yake nufi. Ai shi kenan ita kam tata ta ƙare. Duniya ta juya mata baya. Ajiyar zuciya ta cigaba da saukewa lokacin da ta koma kan gadon ta kwanta. Duk da har lokacin jikinta be gama komawa daidai ba amma tun da ya yi magana ba za ta yi komai ba. Se kawai ta ja blanket ta lulluɓe jikinta da shi ta kwantar da kanta a kan pillow tana kallan waje ɗaya cike da tausayin kanta da ya rufeta. Gefe ɗaya kuma haushin Gwani wanda ba ta taɓa jin irinsa ba.

... Knocking ɗin ƙofar da ya ji an yi ne ya sanya shi ɗaga kai ya kalli ƙofar. Da ma daidai lokacin yake da niyyar fita couz ya duba agogon wayarsa ya kai sau nawa amma shiru ba ta kawo Coffee kamar yanda ta saba kawowa ba. Ya ɗauka ma ko ta sake aro taurin kai ne ta sena yi, se kuma ya ji knocking ɗin. K
Ɗan tsayawa ya yi yana kallan ƙofar dan kuwa ya saba idan ta yi knocking ɗin ta ji shiru hakan na nufin ta shiga ne se dai kuma yau be ga ta shigo ba.

"Ko ba ita ba ce?" Zuciyarsa ta raya masa hakan. Se ya sauke ajiyar zuciya kawai yana soma takawa zuwa wajen ƙofar. Daidai lokacin da ta yi maza ta ajje Coffee ɗin ta bar wajen a million. Tsayawa ya yi yana kallan Coffeen dake ajjiye kamar yanda ta fara yi a farko kafin ya taka mata birki. Ba ƙaramin mamaki ya yi ba. Wato hakan na nufin ta yi fatali da unarninsa kenan? Me take taƙama da shi da har ze ce ga abin da za ta yi ta yi wanda ta ga ya fi mata? Ƙwafa ya ja yana cije laɓɓansa har lokacin kuma idanunsa na kan Coffee ɗin. Ba dan ya riga ya saba da ɗanɗanon Coffee ɗin nata ba da ko kula shi ba ze yi ba. Se dai ya kasa hakan, dan haka ya sanya hannunsa ya ɗauka se dai a fuskarsa a haɗe kamar wanda akawa dole ya sha. Komawa cikin ɗakin ya yi ya nemi waje ya zauna. A nutse ya shiga shan Coffee ɗin gaba ɗaya idanunsa a kan ƙofa kamar me neman wani abu. Be san me ya sa abin da ta yi ɗin ya ɓata masa rai ba. Se dai ya alaƙanta hakan da rainashin da ta nuna ta yi bayan ita ɗin ba kowa ba ce. Se da ya shanye tsaff sannan ya tashi ya fice daga ɗakin.

... "Sauri kake yi ne?" Daddy ya faɗa yana kallan Bad Man. Se ya girgiza kai lokaci ɗaya yana amsawa da

"No Dad.. Kamar ka na wani aiki ne?" Girgiza kai Daddy ya yi yana amsawa da

"A'ah zauna.." Babu musu Bad Man ya zauna yana shirin harɗe ƙafarsa ɗaya kan ɗaya Daddy sa ya lura da hakan, ya watsa masa wani kallo, babu shiri ya sauke ƙafar yana ɗan shafa sumar kansa. Daddy ya girgiza kai yana sauke ajiyar zuciya.

"Shirye shiryen me kake yi ne?" Daddy ya katse shi da faɗin hakan.

"Ina so na ɗan je na huta ne ko da na 3 weeks ne.."

"3 weeks for what? Kawai saboda hutu ka tafi wata ƙasar bayan ka na da abubuwa da yawa da ya kamata a ce ka yi? Ko ka manta yanzu ku na da abin yi ne kai da Kaseem? Ko so kake ka bar shi shi ɗaya ya din ga yi komai? Ko kuwa wani hutu ka shiryawa kanka da matarka?" Daddy ya tambaya yana kafe shi da idanunsa. Shi ma kallan Daddyn yake yi kamar wanda ya ga sabon halitta. Se kawai ya yi wani yaƙe jin abin da Daddyn ya faɗa. Wai hutu? Shi da matarsa? Wace matarsa kuma? Ko Daddyn ya manta kawai tana zaune da su ne ba a matsayin matarsa ba?

"Daddy.. Ba wannan gaskiya a tsarina.. Ni kaɗai nake son zuwa, ba na buƙatar kowa.."

"Har matar taka Areef?" Daddy ya faɗa a sukwane. Sauke numfashi ya yi kafin yace
Chapter 56 · 0% Book details